Makaman Yaƙin mu

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
A cikin Wahayin Yahaya 12:7–9, mun ga cewa an tsarkake sama ta wurin korar macijin (Shaiɗan) da mala'ikunsa. Yi murna, samaniya; ki kula, duniya! Yanzu shaiɗan yana nan a duniya, ya kuma san yana da 'yan shekaru kaɗan don ya yi ɓarna da kuma cutarwa. Na gane cewa wannan lokacin yana da alaƙa da duka (ko ɓangare) na makonni saba'in na Daniel (dubi Daniel 9:21–24). Lokaci ne na musamman—da shaiɗan, wanda ɗalibin annabci ne, ya sani sosai. Kuma Yesu ya faɗi cewa za a taƙaita kwanakin (dubi, misali, Matiyu 24:21–22). Ko da yake a rubuce Littafi Mai Tsarki ya ce shekaru uku da rabi ne, a ƙalla za a sami 'yan "kwanakin" da za a rage a ƙarshe. Daga nan, za a ɗaure shaiɗan a jefa shi a kurkuku cikin rami marar matuka.
Shaiɗan yana so mu zama da jahilci a kan wannan gaskiyar, domin muddin muna da jahilci, ba za mu iya yin abin da Allah ya shirya ba. Amma Allah ya ba mu makamai na ruhaniya domin mu fitar da Shaiɗan daga wurin da yake a cikin sammai.
"Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe makamai masu ƙarfi. Muna kada masu hujjoji [tunani] muna rushe kowace irin ganuwar alfarma mai tare sanin Allah (2 Korintiyawa 10:4–5)
Makaman ruhaniya da aka ba mu za su ba mu ikon rushe kowane babban abu da ke adawa da Allah da kuma mulkinsa. Abu na ƙarshe, babban duka, mafi girma da ke adawa da Allah shi ne mulkin Shaiɗan a cikin sammai. An ba mu makaman da za su ba mu ikon cin nasara da shi: jinin Yesu da kuma shaidar mu.
*Prayer Response
Na gode maka, ya Ubangiji, saboda jinin Ɗan Ragon. Ina ɗaukarsa a matsayin makami na ruhaniya, tare da shaida ta, ina furta cewa na ci nasara a kan Shaiɗan ta wurin jinin Ɗan Ragon da kuma shaida ta, kuma ban ƙaunaci raina har ga mutuwa ba. Amin.
Lambar: WD-B097-076-HAU