Tsattsauran ra’ayin Biyayya

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
A cikin yin wannan furcin, sai mun zama da tsattsauran ra'ayi. Addinin Krista addini ne na tsattsauran ra'ayi. Kalmar nan ‘tsattsauran ra'ayi’ tana nufin "farawa daga tushe." Lokacin da Yohanna Mai baftisma ya gabatar da bishara da Yesu, ya ce:
"Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiyoyi. Saboda haka duk bishiyar da bata ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare a jefa a wuta" (Matiyu 3:10)
Allah ba zai cire wasu rassa ko kuma ya yanke gindin ba. Zai tafi kai tsaye ne ga tushen. Yana buƙatar itace ya bada kyawawan 'ya'ya. Idan itace bai ba da kyawawan 'ya'ya ba, Allah ya ce a sare shi.
A cikin tsara mai tasowa, akwai yiwuwar su zama masu tsattsauran ra'ayi. Ina ganin ya kamata a ƙarfafa wannan tunanin—ta hanya da ta dace. A Gaskiya, mu tsofaffin tsara mun yi watsi da ra'ayinmu sau da dama maimakon mu kasance masu tsattsauran ra'ayi. Muna buƙatar ba Ruhu Mai Tsarki haɗin kai, wanda sau da yawa yana nuna buƙatar zama da tsattsauran ra'ayi.
"In kuwa Ruhun wanda ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, shi da ya ta da Kristi Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa ta wurin Ruhunsa wanda yake zaune a zuciyarku." (Romawa 8:11)
Bulus yana yin wani kwakkwaran bayani a nan. Ya ce Ruhu Mai Tsarki ne, Ruhun Allah, wanda ya ta da jikin Yesu daga kabari. Kuma idan kana da wannan Ruhu Mai Tsarki a cikinka, to, zai iya yin abubuwa da yawa da kake buƙata a jikinka da ikonsa. Wannan gaskiya ce mai ƙarfi!
*Prayer Response
Na gode maka, ya Ubangiji, saboda jinin Yesu da kuma aikin Ruhunka Mai Tsarki. Ina furta cewa zan yi cikakkiyar biyayya da yin aiki tare da Ruhu Mai Tsarki, domin jikina haikali ne na Ruhu Mai Tsarki, wanda aka fanshe shi, aka wanke shi, aka tsarkake shi da jinin Yesu. Amin.
Lambar: WD-B097-062-HAU