Allah Mai Son Zumunta

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Na taɓa zama farfesa a jami'a mafi girma a Birtaniya, na kuma sami digiri dabam dabam da sakamako mai kyau. Ta kowace fuska, na zama mai hazaka sosai—masani. Amma ban taba jin gazawa a fannin ilimi don na gaskata da tarihin halitta na Littafi Mai Tsarki ba. Kafin in gaskanta da Littafi Mai Tsarki, na nazarci wasu majiyoyi da yawa da suka yi ƙoƙarin bayyana asalin mutum, amma na ji ba su gamsar da ni ba. A wurare da yawa, suna saɓa wa juna. Sai na koma ga nazarin Littafi Mai Tsarki—ba a matsayin Mai Bi ba amma a matsayin shahararren masanin falsafa. Na yi tunani a raina, A ƙalla bai kai wautar sauran abubuwan da na ji ba! Abin mamaki a gare ni, sai na gano cewa Littafi Mai Tsarki ne ke da amsar.
A cikin Farawa, mun karanta ɗan bayani mai sauƙi. Ya fara da, "Ubangiji Allah" - wato, "Allah Jehovah" - sunan Allah ne na kansa. Wannan kalma tana gaya mana cewa Allah mai son zumunta ya halicci mutum domin zumunci.
"Sa’an nan Ubangiji Allah ya siffanta mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuwa ya zama rayayyen taliki [rai]." (Farawa 2:7)
A nan mun ga haɗakar numfashin Allah na har abada daga sama da kuma jikin yumɓu a ƙasa, wanda Mahalicci ya siffanta da hannunsa. Haɗakar ruhu daga sama da yumɓu a ƙasa ya samar da ɗan adam mai rai—wanda zai iya yin zumunta da Allah mai rai.
*Prayer Response
Na gode maka, ya Ubangiji, saboda tanadin da ka yi wa jikina. Ina furta cewa Allah na ya halicce ni domin zumunci da shi—kuma jikina na Ubangiji ne, Ubangiji kuma na jikina ne. Amin.
Lambar: WD-B097-078-HAU