Rayuwar Tashin Matattu

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Littafin Firistoci 17:11 ya ce, "Akwai rai a cikin jini." Lokacin da Yesu ya zubar da jininsa, ya bada ransa. A tawa fahimtar, Allah ya bada ransa a cikin duniya. Kuma babu wanda zai iya fahimtar cikakken abin da wannan yake nufi.
"Sai Yesu ya ce musu, 'Lalle hakika [mafi muhimmanci], ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku. Duk wanda suke cin naman jikina ya ke kuma shan jinina yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.'" (Yahaya 6:53–54)
Ku tuna cewa fansarmu ba ta cika ba har sai mun kai ga tashi daga matattu. A cikin Filibiyawa 3:12, Bulus ya ce, "Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle; a’a sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Yesu Almasihu ma ya riƙe ni saboda shi," wato, "tashin nan daga matattu" (aya ta 11).
Wasu mutane suna tunanin cewa jikunansu ba su da muhimmanci sosai. Amma Allah ya ce jikunanmu suna da matukar muhimmanci— haikali ne na Ruhu Mai Tsarki. An halitta su da ban tsoro da ban al’ajibi (Zabura 139:14). Kuma Allah ba zai bar jikunanmu a yanayin lalacewa ba. Zai tashe su da ɗaukaka kamar na Yesu. Fansa ita ce cikakken aikin hadayar Yesu, kuma ana kammala ta ta wurin tashi daga matattu.
*Prayer Response
Na gode maka, Ubangiji, saboda jinin Ɗan Ragon. Kamar Bulus, “Ina nacewa …domin ko ta ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.” Ina furta cewa na ci nasara a kan Shaiɗan ta wurin jinin Ɗan Ragon da kuma shaida ta, kuma ban ƙaunaci raina har mutuwa ba. Amin.
Lambar: WD-B097-071-HAU