Miƙa kanmu ga Allah

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Za a iya taƙaita maganin da Allah ya samar na tsohon mutum a cikin kalma ɗaya: kisa. Kisa shi ne abin da ya faru a kan gicciye, lokacin da Yesu ya mutu aka kuma gicciye tsohon mutum namu tare da shi. Ta yaya za mu mori maganin da Allah ya bayar a rayuwarmu?
"Saboda haka kada ku yarda zunubi ya mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha'awarsa, kada kuma ku miƙa gaɓoɓin su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna mika gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci. Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari’a take iko da ku ba, alherin Allah ne." (Romawa 6:12–14)
Waɗanda suka yi bangaskiya ga Yesu kuma suka yarda da hadayarsa a madadinsu ne kawai za su iya bin umurnin Bulus. Wani ya taɓa cewa, "Idan kana son zuwa sama, dole ne ka koyi cewa a'a." Wannan ce gaskiyar. Bulus ya ce dole ka ɗauki ƙudurin yin tsayayya da zunubi. Zunubi da Shaiɗan duka za su iya bambancewa tsakanin lokacin da muke faɗin kalmomi kawai da lokacin da muke yi da gaske. Dole ne mu furta waɗannan kalmomin da tabbaci. Sannan, ta wurin bangaskiya ga Yesu, nufin mu zai sami ‘yanci daga ikon zunubi. Daga nan ya zama haƙƙinmu mu mori nufin mu daidai. Ba Allah ne zai yi mana wannan ba. Ya zama dole mu fahimci haƙƙinmu na lura da nufe-nufenmu.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda nasarar ka a kan gicciye. Ina tsaye yanzu ina furta cewa zunubi da Shaiɗan ba su da wani iko a kaina. Ina furta cewa gaɓoɓina, sassan jikina, kayan aikin adalci ne, waɗanda na miƙa su ga Allah domin hidimarsa da kuma ɗaukakarsa. Amin.
Lambar: WD-B097-064-HAU