Kula da Haikali

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Littafi Mai Tsarki ya kai ni ga yanke wasu shawarwari a zahiri game da jikina. Ba na ƙoƙarin ɗora wa kowa waɗannan abubuwa, amma na ba waɗannan batutuwa kulawa da addu'a sosai, kuma ina shirye in sami babban sauyi a rayuwata, idan nufin Allah ne.
Shawarata ta farko ita ce, dalilan yanke waɗancan shawarwari, shi ne dole ne in kula da jikina da girmamawa tare da kulawa a matsayin haikalin Ruhu Mai Tsarki. Bulus ya sake cewa:
"Ashe ba ku sani ba, jikinku haikali ne na Ruhu Mai Tsarki?" (1 Korinthiyawa 6:19)
Idan muka ɗauki wannan ayar da muhimmanci, to, za mu kula da jikkunanmu kamar haikali, domin haka suke.
Da a ce a wani ɗan lokaci Allah zai ba mu haƙƙin kula da haikali na zahiri - na ginin dutse, katako, da gilashi. Idan muka zama masu himma, za mu yi kwazo wajen kula da shi - za mu tsaftace shi mu goge dukan ƙura, babu karyayyun tagogi ko ba-haya mai kazamta. Za mu ji cewa babbar nawaya ce mu kula da wannan ginin don ya kasance da kyaun gani. A matsayi nmu na Krista, ni da kai muna da babbar nawaya ta kula da jikkunanmu, waɗanda su ne haikali na Ruhu Mai Tsarki, a kyakkyawan yanayi, ya kamata mu gane abin da yin hakan ya kunsa.
A cikin wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Timotawus, Bulus ya rubuta:
"Ai Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamun kai" (2 Timothawus 1:7)
A nan mun ga cewa Ruhu Mai Tsarki Ruhu ne na kamun kai. Amma akwai daidaito mai sauki: Ba zai hore mu idan ba mu yarda a hora mu ba. Idan muka nemi taimakon Ruhu Mai Tsarki wajen horar da kanmu, to, zai taimake mu.
*Prayer Response
Na gode maka, ya Ubangiji, saboda jinin Yesu da kuma aikin Ruhunka Mai Tsarki. Zan nemi taimakon Ruhu Mai Tsarki wajen horar da kaina don kula da jikina a cikin kyakkyawan yanayi, domin haikali ne na Ruhu Mai Tsarki, wanda aka fanshe shi, aka wanke shi, aka tsarkake shi da jinin Yesu. Amin.
Lambar: WD-B097-061-HAU