Ba Ruhu haɗin kai

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
"To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani wadansu za su fanderewa bangaskiya, su mai da hankali ga aljanu masu rudi da kuma koyarwar aljanu, ta wurin makakircin wadansu makaryata, wadanda aka yi wa lamirinsu lalas, su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, wadanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya suka kuma san gaskiya su karɓa da godiya. Domin duk abin da Allah ya halittai kyakkyawa ne] kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya; gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a." (1 Timothawus 4:1–5)
A cikin wannan nassin, Bulus yana cewa, da farko, cewa kyale dangantakar aure (watau rashin aure) ba shi ne sharaɗin guda na zama tsattsarka ba; ba lallai bane ya kai ga rayuwar tsarki. A gaskiya, idan muka duba tarihin Ikkilisiya, a lokutan da aka buƙaci Fastoci su zama marasa aure, a bayyane yake cewa rashin aure ba lallai ya kai ga zaman tsarki ba.
Dangane da abinci mai dacewa, abin da Bulus yake faɗa shi ne, "Duk abin da Allah ya halitta a matsayin abinci yana da kyau." Amma wajibi ne mu sani cewa abinci mai kyau da Allah ya halitta na iya gurɓata bisa ga yadda muka shirya shi. Don haka, ka ɗauki lokaci ka kuma yi ƙoƙarin bambancewa tsakanin abubuwan da ke da amfani da abubuwan da ke da illa. Ka ba Ruhu Mai Tsarki haɗin kai.
*Prayer Response
Na gode maka, ya Ubangiji, saboda jinin Yesu da kuma aikin Ruhunka Mai Tsarki. Ina furta cewa zan ba Ruhu Mai Tsarki haɗin kai don bambancewa tsakanin abin da ke da amfani da mai cutarwa ga jikina, domin haikali ne na Ruhu Mai Tsarki, wanda aka fansa, aka wanke shi, aka kuma tsarkake shi da jinin Yesu. Amin.
Lambar: WD-B097-060-HAU