Yesu Mai Kuɓutarwa

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Wannan Almasihu wanda shi kaɗai ne Mai Ceto shi kaɗai ne kuma mai kuɓutarwa. Yesu ne kaɗai zai iya karya ƙangin aljanu a rayuwar mutane ya kuma kuɓutar da su. Ina so mu sadu da mai kuɓutarwan nan dai dai kamar haka
Ga waɗanda a cikinmu suke buƙatar kuɓutarwa, muna buƙatar saduwa da Kristi kai tsaye a matsayin mutum da mutum. Ga wasu sauƙaƙan sharuɗɗa guda huɗu da muke buƙatar cikawa:
- Mu tabbata mun tuba. Wato, mu sani cewa mun juya baya ga kowane irin zunubi.
- Ka dubi Yesu shi kaɗai, domin Shi kaɗai ne mai kuɓutarwa.
- Mu dogara kacokam a kan abin da Yesu ya yi mana ta wurin mutuwarsa a kan gicciye ba a kan wasu “kyawawan ayyuka" na kanmu ba.
- Mu tabbatar da cewa, ta wurin nufin kanmu, mun gafarta wa duk wanda ya zalunce mu ko ya yi mana laifi.
Lokacin da ni kaina na sami kuɓutarwa daga ruhun baƙin ciki, na sami wannan alƙawarin:
"Amma dukan wadanda suka nemi Ubangiji za su tsira" (Yowel 2:32)
Na kuma tuna waɗannan kalmomi na Yesu:
"Da sunana [almajirai] za su fitar da aljanu" (Markus 16:17)
Da sunan Yesu, mu ma muna da ikon fitar da aljanu.
*Prayer Response
Na gode maka, Ubangiji, saboda jinin Yesu. Ina furta cewa Shi kaɗai ne Mai kuɓutar da ni, kuma "duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto." Shaiɗan ba shi da wuri a cikina, ba shi da iko a kaina, babu abin da ke tsakanina da shi. Jinin Yesu ya biya komai! Amin.
Lambar: WD-B097-052-HAU