Ni Mallakar Allah Ne

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Littafi Mai Tsarki yana cewa dole ne mu ɗaukaka Allah da jikkunanmu da ruhun mu (duba 1 Korinthiyawa 6:20), domin duka biyun na Allah ne; an fanshe su duka daga hannun shaiɗan da jinin Yesu. Babu wani shashi na rayuwa ta—ruhu, rai, ko jiki—da ke ƙarƙashin iko ko mulkin Shaiɗan.
Bari in bayyana a fili cewa bani da jikin tashin matattu, amma ina da jikin da zai mutu. Amma wannan jikin mai mutuwa—duk jijiyoyinsa, ƙwayoyin halittarsa, da tsokarsa—mallakar Allah ne, ba na shaiɗan ba. Idan shaiɗan ya shiga wannan yanki, to, ya karya doka. Ta amfani da haƙƙinmu cikin Yesu, za mu iya kafa alama mai cewa “Ba a Shiga.” Bisa doka, jikkunanmu ba na shaiɗan ba ne, na Yesu ne, wanda yake da wata manufa ta musamman domin su. An tsara su su zama wurin zama na mutum na uku na Allahntaka, wato, Ruhu Mai Tsarki. Jikkunanmu masu tsarki ne domin an ƙudurta su su zama wurin zaman Ruhu Mai Tsarki.
Littafi Mai Tsarki ya bayyana sau da dama cewa Allah ba ya zama a haikalin da hannun mutane suka gina (misali, dubi, Ayyukan Manzanni 7:48). Haka kuma, ba ya zaune a cikin gine genen Ikkilisiyu, ko Masujada, ko Majami’u, ko wasu gidajen ibada da ake gani. Allah yana zaune ne a cikin mutanensa.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-045-HAU