Abinda Tsarkakewa ke Nufi

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Tsarkakewa wata kalma ce daga cikin dogayen kalmomin nan na Tauhidi. Bari mu sa shi kamar haka. A cikin harsunan Littafi Mai Tsarki na ainihi, tsarkakewa na da alaƙa ta kai tsaye da kalmar “tsarki”. Don haka, “tsarkakewa” na nufin “ a tsarkaka.” Kalmar turanci tsarkakewa na da alaƙa da kalmar Tsattsarka. Tsarkakewa hanya ce ta sa wani abu ya zama da tsarki, ko ya tsarkaka.
“Domin wannan Yesu kuma, domin shi tsarkake jama'a ta wurin jininsa, ya sha raɗaɗi a bayan ƙofar birni.” (Ibraniyawa 13:12)
Yesu ya je bayan birni a matsayin hadaya saboda zunubi (dubi, misali, Yahaya 19:16–20). Mun koya daga Tsohon Alkawari cewa ba za a iya miƙa hadayun zunubi a cikin wurin da mutanen Allah su ke ba (dubi, misali, Fitowa 29:14). A koyaushe tsarkakewa ta haɗa da keɓewa.
Domin mu tsarkake kanmu, dole ne mu ba da shaidar da ta dace: “Ta wurin jinin Yesu, na tsarkaka, an tsarkake ni, an keɓe ni ga Allah, an raba ni da dukan abinda ke mugu. Jinin Yesu na tsakani na da kowace mugunta.”
Wanda aka tsarkake yana wurin da Allah zai iya kai gare shi, amma mugun ba zai iya ba. Samun tsarkakewa shine a kawar da mutum daga wurin da Shaidan zai iya ziyarta da kaiwa gareshi a kuma sa mu a wurin da Allah zai iya kai gare mu, amma ba wurin da shaidan zai same mu ba. Wannan shi ne abin da ake nufi da tsarkakewa, a tsarkaka, da keɓewa domin Allah.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-036-HAU