Karfin Zuciya ta Wurin Adalci

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Allah na mai da marasa adalci adalai. Littafi Mai Tsarki ya faɗi haka, kuma na gaskata da shi. Bari mu dubi wata aya mai sauki da ta tabbatar da wannan gaskiyar:
“Shi wanda ba ya san kowane zunubi ba, ya maishe shi zama zunubi sabili da mu, domin mu mu zama adalcin Allah a cikin Sa” (2 Korinthiyawa 5:21)
A cikin wannan ayar, ina so in saka sunaye a madadin wakilin suna: “Gama Allah ya mai da Yesu, wanda bai san zunubi ba, ya zama zunubi sabili da ni da kai, domin mu zama adalcin Allah a cikin Yesu.” Akwai cikakkiyar musaya: An mai da Yesu zunubi da zunuban mu domin mu zama masu adalci da adalcin sa. Wannan adalci na samuwa ta wurin bangaskiya cikin jinin Sa.
Adalci na haifar da waɗansu sakamako da za a iya gani nan take. Bari mu dubi ɗaya daga cikin waɗannan sakamakon kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, hanyoyin rayuwar mu, halayen mu, dangantakar mu, da tasirin rayuwar mu ta Krista da ayyukan hidima za su danganta ne a kan yadda muka gane cewa an mai da mu adalai. Mun karanta a Misalai 28:1:
“Miyagu su kan gudu ba wanda ya ke bin su, amma masu adalci suna da ƙarfin zuciya kamar zaki.”
Krista da yawa a yau ba su da ƙarfin zuciya. Su na da tsoro da saurin ba da hakuri; sukan ja da baya idan su ka fuskanci mugunta ko shaidan. Ainihin tushen wannan shi ne rashin fahimtar gaskiyar cewa su masu adalci ne a gaban Allah—masu adalci kamar Yesu Kristi da Kansa. Sa’ad da muka fahimci wannan gaskiyar, hakan na ba mu ƙarfin zuciya.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-033-HAU