Adalci da Rashin Laifi

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
“Balle fa yanzu, baratattu ne ta wurin jininsa, za mu tsira da ga fushin Allah ta wurin Sa.” (Romawa 5:9)
A duk lokacin da muka sami kalmar ‘marar laifi’ a cikin Littafi Mai Tsarki, za mu iya sauya ta da kalmar ‘adalci’. Wannan gaskiya ce a cikin Ibraniyanci na Tsohon Alkawari da kuma Helenanci na Sabon Alkawari. Waɗanda suka fassara juyin King James sun fassara kalma ɗaya ta zama ko dai “adalci” ko kuma “marar laifi.” Sun yi amfani da kalmar ‘marar laifi’ a sha’anin da ya shafi shari'a, ita kuma kalmar ‘adalci’ a sha’anin aikatawa ta rayuwa. Amma kalmar dai duk ɗaya ce.
Inda matsalar ta ke ita ce wajen yin amfani da kalmar barata, wadda galibi an keɓe ta ne don irin al’amuran shari'a a dakalin shari’a a sama. Amma yin hakan ya rage muhimmancin kalmar. Baratarwa na nufin zama marar laifi, ko kuma adali. Kalmar adalci na bayyanawa ne a wuraren da mu ke rayuwa - gidajen mu, wuraren aiki, ko ta dangantakar mu. Kalmar nan ‘rashin laifi’ na nuna al’amurran shari’a da aka zartar a cikin kotu. Littafi Mai Tsarki ya ce (kuma wannan fassara ce da tayi daidai) cewa an maishe mu masu adalci ta wurin jinin Yesu. Ba za mu iya ɗaukar kan mu marasa laifi ba idan ba a mai da mu masu adalci ba. Baratarwa ta fi gaban al’amuran doka ko canjin suna. Canjin hali ne da rayuwa, kuma jinin Yesu ne ya samar da shi. An mai da mu masu adalci da adalcin da ba namu ba—adilcin Yesu Kristi.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-031-HAU