Biyayya da Gaskiya

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Zumunta ita ce gwaji na farko na sanin ko muna tafiya cikin haske. Idan ba ma jin daɗin yin zumunta da 'yan'uwan mu Masu Bi da kuma Ubangiji, to, ba mu cikin haske, kuma idan ba mu cikin haske, jinin Yesu ba ya tsarkake mu.
Tambaya ta gaba ita ce wadda ta shafi yadda muke tafiya a cikin haske. Sharaɗi na farko shi ne cewa dole ne mu yi tafiya ta biyayya ga maganar Allah. Zabura 119:105 ta ce:
“Maganar ka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma ga tafarkina.”
Bulus ya taƙaita abin da ake buƙata na biyu a cikin Afisawa 4:15, inda ya rubuta:
“Amma garin faɗin gaskiya cikin ƙauna, mu yi girma cikin abu duka zuwa cikin sa, wanda shi ne Kai, Wato, Kristi;”
A cikin wannan aya, "yin tafiya cikin haske" ana bayyana shi da dangantaka da 'yan'uwanmu Masu Bi cikin gaskiya da ƙauna. Dole ne mu kasance masu son yin gaskiya a cikin dangantakarmu da juna, amma dole ne mu yi hakan cikin ƙauna.
Saboda haka, tafiya a cikin haske na ƙunshe da abubuwa biyu da aka haɗa: tafiya cikin biyayya ga Maganar Allah da tafiya cikin gaskiya da ƙauna tare da 'yan'uwanmu Masu Bi. Idan muka cika waɗannan sharuɗɗan, to, za mu iya cewa da cikakken tabbaci, jinin Yesu yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
A yau, muna da masaniya sosai game da gurbacewar yanayin da ake gani kewaye da mu, amma yanayin ruhaniya ma na gurɓata ta hanyar zunubi, ɓaci, da rashin bin Allah. Domin mu ci gaba da zama a tsarkake, muna buƙatar tsarkakewar jinin Yesu a kullum.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-026-HAU