Kawo Zunubi Zuwa Haske

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Zumunta ita ce wurin zaman haske. Wannan shine dalilin da ya sa zumunta wuri ne na gwaji. Yawan zumunta na sa hasken ya ƙara haskakawa, har ya kai in da ba wuri ko lungun da ke a boye. Babu duhu; Babu abin da a ke boyewa, ba a rufe komai. Wannan na iya zama wuri mai ban tsoro ga mutum marar ruhaniya. Amma wurin ne kaɗai jinin Yesu ke cika aikinsa na tsarkakewa. Idan ka na buƙatar tsarkakewa, sai ka zo cikin haske. Idan ka yi laifi a gaban Allah, ko kuma ka yi wa maƙwabcin ka laifi, ba ka cikin hasken sosai. Kuma ba za a iya amfani da jinin ba sai dai a cikin haske.
Menene za ka yi? Ka zo wurin haske. Menene "zuwa wurin haske"? Furta zunuban ka, da bayyana su a fili a gaban Allah. Amma, wannan shine abu mafi wuya ga mutum marar ruhaniya ya yi. Hasken na iya zama da haske sosai. Za ka iya cewa, ah, ba zan iya kawo wannan mugun abu ba, mummunan asiri wanda ni kaɗai na sani; ba zan iya fallasa shi ga haske ba. Mutum marar ruhaniya zai so ya ja baya. Amma gaskiyar ita ce, idan ka kawo shi ga haske, zai shuɗe saboda, jinin ya na wanke shi. Amma idan ba ka kawo shi ga haske ba, ka nan riƙe da shi. Wannan babbar ƙa'ida ce. Jinin yana aiki ne kaɗai a cikin haske.
Misali a ce mun bi ƙa’idar tafiya cikin haske. Idan haka ne, muna zumunta da ’yan’uwan mu Masu Bi, kuma muna da ‘yancin maida wannan ta zama shaidar mu.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-025-HAU