Albarkun Gafara Marasa Ƙirguwa

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
1 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Irin gafarar da muke buƙata, da kuma za mu iya karɓa daga wurin Allah da kansa kaɗai, ita ce gafara ta tsakanin mu da Allah. Akwai wata irin albarka a cikin samun gafarar Allah. Dauda ne wataƙila ya bayyana wannan gaskiyar da kyau a cikin Zabura 32:
“Mai-albarka ne mutum wanda an gafarta masa laifofinsa, wanda an rufe zunuban sa. Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji bai lissafta zunubinsa a kansa ba, wanda ba shi da algus a cikin ruhunsa ba.” (aya 1–2)
A cikin harshen Ibraniyanci, wannan zaburar ta fara da jam’in suna: albarku. “Albarkun da ke kan wanda aka gafarta masa laifofinsa, aka rufe zunuban sa”. Ma’anar ita ce, akwai albarku masu yawa a tattare da samun gafarar Allah daga zunuban mu.
Yana da muhimmanci mu ga cewa Littafi Mai Tsarki bai yi magana game da mutumin da ba ya buƙatar gafara ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa dukan mu muna buƙatar gafara daga wurin Allah; babu bambanci. A wasu zabura, Dauda ya ce babu mutumin da ba ya yin zunubi. Dukan mu mun yi zunubi. Don haka, dukan mu muna buƙatar gafara. Tambayar ko muna buƙatar gafara ma bata taso ba, sai dai ko mun same ta.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-019-HAU