Hanyoyi Biyu Na Yin Gafara

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Gafara na ɗaya daga cikin kyawawan kalmomi a kowane harshe. Me ya sa ta zama kyakkyawar kalma kuma ta musamman? Dubi wasu sakamakon da ke fitowa daga gafara: sulhu, salama, jituwa, fahimta, zumunci. Duniyar mu a yau na tsananin buƙatar waɗannan abubuwa!
Akasin haka, mu dubi wasu sakamakon da ke fitowa daga rashin yin gafara da karɓar gafara: ɓacin rai, husuma, rashin jituwa, ƙiyayya, da yaƙi. A wasu lokuta, bisa ga alama dai dukan ’yan Adam na cikin haɗari na zama a ƙarƙashin waɗannan mugayen ikoki. Idan har za mu tashi mu ci nasara da waɗannan ikokin, zai kasance ne kawai yayin da muke koyo kuma muke yin amfani da ƙa'idodin yin gafara.
Akwai hanyoyi guda biyu na yin gafara da aka gabatar a cikin Littafi Mai Tsarki. Ana kwatanta waɗannan hanyoyi biyu da wannan babbar alamar bangaskiyar Krista: wato, giciye. Gicciye na da katako guda biyu - ɗaya a tsaye, ɗaya a kwance - waɗanda ke nuna hanyoyi biyu na yin gafara. Katako na tsaye na nuna gafarar da dukan mu muke buƙatar karɓa daga wurin Allah kuma za a iya karɓa ta wurin yarda da hadaya da kuma tashin Yesu Kristi daga matattu. Katakon da ke kwance na nuna dangantakar mu da sauran mutane, kuma ya na magana game da gafarar da, a wannan yanayin, na da hanyoyi guda biyu: gafarar da muke buƙatar samu daga wasu, da kuma gafarar da muke buƙata mu yi wa waɗansu. Har yanzu kuma, wurin da kaɗai za mu sami ikon yin irin wannan gafarar shine gicciye.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-017-HAU