Cikakkun Haƙƙin Fansa

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
1 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
A cikin Afisawa 1:7, mun ga wannan tanadin jinin Yesu:
“Ta gare shi [Kristi] ne muka sami fansa ta albakacin jininsa, wato, yafewar laifofin mu, bisa ga yalwar alherinsa.”
An sayo mana gafarar zunubai da jinin Yesu. Kwatanta wannan ayar da abin da Yesu ya faɗa a Jibin Ƙarshe a cikin Matta 26:28 lokacin da ya ke ba almajiran ƙoƙon, wanda shine alamar jininsa:
“Gama wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar domin mutane da yawa domin gafara [gafarar zunubai].” (Matta 26:28)
Ibraniyawa 9:22 ta ce idan ba a zubar da jini ba, babu gafarar zunubi. Don haka an zubar da jinin Yesu domin a gafarta ma na zunuban mu.
Za ku lura cewa a cikin Afisawa 1:7, Bulus ya sa waɗannan abubuwa biyu su kasance tare: fansa ta wurin jinin Yesu da kuma gafarar zunubai. Fahimtar wannan yana da matukar muhimmanci domin muna da cikakkun haƙƙin fansa na shari'a muddin an gafarta mana zunuban mu.
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-015-HAU