Fita Daga Wani Mulki - Zuwa Wani

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Ubangiji ya fanshe mu domin kada mu zauna a hannun maƙiyi amma a hannun Ubangiji.
“Kuna godiya ga Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkaka da ke cikin haske. Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗan sa.” (Kolosiyawa 1:12–13)
Gaskiya ce cewa Allah ya cece mu daga ikon duhu - wato, mulkin Shaiɗan - kuma ya kawo mu cikin mulkin Kristi.
Ta haka, muna da fansa - an gafarta ma na zunuban mu. Ba mu cikin yankin Shaiɗan kuma ba ma ƙarƙashin ikonsa.
Marasa bi, waɗanda suka ƙi Kristi, masu tawaye, da marasa biyayya suna ƙarƙashin ikon Shaiɗan, amma mu Krista ba ma ƙarƙashin ikon sa.
Gaskiyar ita ce, sa’ad da muka tuba muka miƙa kan mu ga Yesu Kristi kuma muka mai da shi Ubangijin rayuwarmu, an ɗauke mu (canza, ko ɗauke zuwa) — ruhu, rai, da jiki— daga cikin mulkin Shaiɗan zuwa cikin mulkin Kristi. Wannan haƙiƙanin gaskiya ne. Mun gaskata da gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah marar ganuwa domin ba ma yin rayuwa ta wurin yadda muke ji. Garkuwar bangaskiya ta shafi kowane fanni na rayuwar mu. Babu wani kibau mai zafin wuta da zai taɓa iya ƙetare shi (dubi Afisawa 6:16).
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-014-HAU