Shi Ya yi kuma Shi Ya saya

Derek Prince
*Last Updated: March 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Ga misalin da na gaya wa wani taron mutanen Maori na Polynesiya, waɗanda manyan masassaƙan itace ne, domin in kwatanta farashin da Yesu ya biya domin ya fanshe mu daga zunubi.
Akwai wani yaro da ya sassaƙa ɗan ƙaramin jirgin ruwa na katako mai kyau. Wata rana ya tafi da shi rafi domin ya gwada shi, amma iska ta canza ya tafi da jirginsa zuwa teku. Tun da ya kasa ƙwato jirgin ruwan, sai ya koma gida ba tare da shi ba.
Sai can wani raƙumin ruwa mai ƙarfi ya sake dawowa da jirgin, sai wani mutum yana tafiya a bakin gulbin ya same shi. Ya dubi jirgin ya ga an ƙera shi da kyau, sai ya je ya sayar wa wani mai shago, shi kuma ya goge shi ya saka shi a bisa tagarsa, ya sanya masa farashi.
Bayan wani ɗan lokaci, yaron yana wucewa ta shagon sai ya ga jirginsa. Nan take ya san cewa nasa ne, amma ba shi da yadda da zai nuna cewa na sa ne. Idan yana so ya karɓe shi, ya san dole ne ya saye shi.
Ya sunkuya neman aiki domin ya sami kuɗin ta wurin wanke motoci, yankan ciyawa, da sauran ayyuka. Da ya tara kuɗaɗen da ake buƙata, sai ya shiga shagon ya sayo jirgin ruwan na sa. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya riƙe a ƙirjin sa, ya ce, “Yanzu ka zama nawa! Ni ne na yi ka, na kuma saye ka.”
Ka ɗauki kanka a matsayin wancan jirgin. Wataƙila ka na ganin kasawar ka, ko ka ɗauki kanka mamar amfani; ko kuma ka yi tunanin ko Allah ya kula da kai. Amma Ubangiji yana ce maka, “Yanzu ka zama nawa sau biyu, Ni na yi ka kuma na saye ka. Ka zama nawa cikakke."
*Prayer Response
Lambar: WD-B097-013-HAU