Addu'a Domin Gwamnati

Derek Prince
*Last Updated: May 2026
16 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
Krista na da alhakin gwamnatin da suke rayuwa a ƙarƙashin ta. Idan za ka rage lokacin zargi kuma ka ƙara lokacin addu'a, za ka rage samun abin yin zargi.
Akwai hanyoyi dabam dabam da Ikkilisiya za ta sa ikon ta ya yi tasiri a wannan ƙasar. Zan ba da shawarar hanyoyi huɗu: addu'a, shaida, wa'azi, da yi nagarta. Waɗannan su ne hanyoyin farko da Allah ke son Ikkilisiya ta yi amfani da su don yin tasirin ta.
Allah na son Ikkilisiya ta yi amfani da iyawar ta a cikin al'amuran wannan duniya ta hanyar addu'a. An bayyana wannan a sarari a cikin ayoyin Littafi Mai Tsarki. Idan Ikkilisiya ta kasa yin hakan, to, Ikkilisiya ta zama gishirin da ya rasa zaƙin sa.
A cikin 2 Labarbaru 7:14 muka karanta: “Idan mutanena, waɗanda a ke kiransu da sunana zasu ƙasƙantar da kansu, su juyo ga barin mugun aikinsu; sa’annan zan ji daga sama, zan kuma gafarta musu zunuban su, zan warkad da ƙasarsu.” Wannan ne wahayin da Ubangiji ya ba Sulemanu bayan ya keɓe haikali. Waɗansu daga cikin ku babu shakka suna da ra’ayin: Sulemanu ne aka yi wa wannan alƙawari tun da daɗewa a cikin Tsohon Alƙawari kuma wannan ba shi da ma’ana a gare mu a yau. Bari in magance wannan ƙin yardar a taƙaice.
A cikin 2 Korantiyawa 1:20 mun karanta: “Domin dukan alƙawaran Allah cikar su a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗin ʻAminʻ, domin a ɗaukaka Allah.” Ba wasu daga cikin alƙawuran ba—amma dukan alƙawuran! Ba su wuce, ko za su faru ba—amma suna nan! Ba wai kawai I, ba, amma idan har yanzu kana da shakka, I ne da Amin! a cikin Sa (Kristi) zuwa ga ɗaukakar Allah ta wurin mu. “Mu” na nufin dukan Krista, har da kai da ni. Ta yaya za mu ɗaukaka Allah? Ta wurin amincewa da alƙawuran Sa! Yawan alƙawuran Allah da muke amincewa da su,ta hakan muke ƙara ɗaukaka Allah. Dukan alƙawuran Allah na samuwa a gare mu yau a cikin Kristi.
Idan muka koma ga alƙawarin da ke cikin Labarbaru ta Biyu 7:14, na gaskata ka ga yadda wannan alƙawari ya shafe ka da ni a yau! Allah ya na magana da “...Mutane waɗanda ake kiransu da suna na.” Wannan fassarar Sabon KingJames ce. Fassarar Ibraniyanci ta zahiri ita ce: “...Mutane na waɗanda da sunana ake kiransu da shi.” Mutanen Allah su ne waɗanda da sunansa ake kiran su da shi. Idan kai Krista ne, menene wannan ke nufi? Yana nufin cewa sunan Kristi ake kiran ka da shi. Kana haɗe da sunan Kristi. Ana gane ka a matsayin Krista ta wurin sunan Kristi. Don haka wannan alƙawari ya shafi Krista: Mutanen Allah waɗanda da sunan Kristi ake kiran su da shi.
Allah ya ce idan mutanen sa za su yi abubuwa huɗu, Shi zai yi abubuwa uku. Dole ne mutanen Allah su yi abubuwa huɗu da farko, kafin Allah ya yi abubuwa ukun da ya yi alƙawarin yi. Alƙawari ne na sharaɗi. Allah bai ce zai yi ba tare da sharaɗi ba, amma Ya ce, “Idan mutane na za su cika sharuɗa Na, to, zan yi waɗannan abubuwan.”
Da farko, dubawa zuwa ƙarshen ayar, abu na ƙarshe da Allah zai yi wa mutanen Sa shi ne ya warkar da ƙasarsu. A bayyane yake cewa wannan ita ce ƙasar da suke zaune a cikin ta. Allah ya ce mutanen sa na da ikon yin abubuwan da zai sa ya warkar da ƙasar da suke zaune a cikin ta. Ku dubi ƙasar da muke zaune a cikin ta. Ko tana buƙatar warkarwa? Amsa guda ɗaya ce kawai. I! Gaskiyar cewa ƙasar na buƙatar warkarwa na nuna cewa mutanen Allah sun kasa yin abin da Allah ya umurce su su yi. Alhakin a wuyan mu ya ke—ba ga mai shan ƙwayoyi ba, ba ga karuwa ba, ba ga mutumin da ke duhunta Ikkilisiya ba. Alhakin na wuyan mutanen da ake kira da sunan Kristi!
Idan ƙasar mu ba ta warke ba, dalili guda ɗaya ne kawai. Ba mu yi abubuwan da Allah ya buƙata ba. Na gaskata cewa wannan ita ce ainihin gaskiyar. Wannan ce kawai hanya mai sauƙi na faɗin abin da Yesu ya ce a Matta 5:13: “Ku ne gishirin duniya; amma kadan gishirin ya rabu da zaƙinsa, da me za shi gyaru? Nan gaba ba shi da amfani ga komi ba, sai a yas, a tattake ƙalƙashin sawun mutane.” Idan ƙasar mu ba ta warke saboda kasancewarmu ba, to, gishirin mu ya lalace.
Menene gishiri yake yi? Da farko, yana ba da ɗanɗano. Muddin muna nan a duniya, muna ba duniya ɗanɗano a gaban Allah. Wato, Allah ya na aminta da duniya saboda Krista. Allah yana huɗɗa da duniya cikin alheri da jinƙai, maimakon cikin fushi da hukunci, saboda kasancewar mu.
Na gaskata sosai cewa akwai bambanci a inda na ke. Na gano wannan a lokacin Yaƙin Duniya na II. Sauran sojoji na da kwanciyar rai a inda nake. Sojojin da ba su da ceto sun san wannan. Sa'ad da muke cikin matsanancin yanayi a hamadar Afirka ta Arewa, wasu daga cikin waɗannan sojoji masu saɓon Allah su ka juyo wuri na su ce, “Kofur Prince, ina farin ciki da kasancewar ka tare da mu.” Me Elisha ya ce wa Iliya? “Ubana, ubana, keken Isra'ila da mahayansa!” (2 Sarakuna 2:12). Ina suke? Ba a kewaye da sarakuna ba amma a kewaye da annabawa.
Mu ne mutanen da suke kare ƙasar. Mu ne ƙaƙƙarfar kowace katangar al'umma. Ka dubi misalin Saduma. Ibrahim ya ce wa Allah, “Idan akwai mutane goma masu adalci, za ka ƙyale birnin?” Kuma Allah ya ce, “I.” Amma ba zai iya ƙyale birnin ba saboda ba zai iya samun mutane goma masu adalci ba. Ban san yawan mutane da ke Saduma ba, amma na san cewa wannan kason har yanzu yana aiki. Mutane goma masu adalci za su iya ceton birni mai girman Saduma. Mutane ɗari masu adalci za su iya ceton birni sau goma na girman Saduma. Mutane dubu masu adalci za su iya ceton birni sau ɗari na girman Saduma. Da sauransu bisa ga kason su. Ina jin tausayin wannan duniya lokacin da Ikkilisiya ta tafi. Ba za a sake samun gishiri ba. Daga nan za a zubo da fushi da hukunci ba tare da iyaka ko hanawa ba. Amma yayin da muke a nan, mu ne gishirin duniya.
Haka ma gishiri na hana lalacewar abu. Yana kawar da ruɓewa. A zamanin da babu firji, ana yin amfani da gishiri don hana lalacewar nama. Yana hana ruɓewa . Me yasa muke a nan? Don hana lalacewa. Lalacewa a kowane wuri—na ɗabi'a, na zamantakewa, na siyasa. Muddin muna nan, za mu yi haka. Yesu ya ce, “Kadan gishiri ya rabu da zaƙinsa, da me zai gyaru? Ba shi da wani amfani sai a yas a tattake shi a ƙalƙashin sawayen mutane.” Sa’ad da Ikkilisiya ta daina cika aikin ta na gishiri, sai a yas, a tattake ta ƙalƙashin sawayen mutane. Waɗannan mutane na iya zama ’yan gurguzu ko ’yan Nazi ko mabiya wasu “ƙungiyoyin” da ba su tuba ba. Amma mutane ne za su tattake Ikkilisiyar da ba ta cika aikin ta na gishiri a duniya ba.
Menene abubuwan da Allah ya buƙaci mutanen sa su yi? Da farko dai, “...Mutane na za su ƙasƙantar da kansu.” Wannan shi ne abu mafi wahala ga mutane masu addini su yi. Ban faɗi wannan da wasa ba, ina nufin shi da gaske. Ka ji wasu mutane na cewa, “Allah, ka sa ni in ƙasƙantar da kaina.” Allah bai taɓa faɗin haka ba. Allah ya ce, “Ka ƙasƙantar da kanka.” Bai ce, “Zan yi muku” ba. Allah ba zai ƙasƙantar da kai ba. Allah zai sa ka ƙasƙanta, kuma sai ya yi hakan, amma mutumin da zai iya ƙasƙantar da kai shi ne kai da kanka. Dole ƙasƙantar da kai ta zo ta wurin nufin son ranka na ciki. Ba zai iya zuwa ta wata hanya ba. Idan ba ka zaɓi ka ƙasƙantar da kanka ba, za a iya ƙasƙantar da kai a cikin ƙura amma har yanzu zaka kasance mai girman kai kamar ɗawisu.
Sharaɗi na farko shi ne ka ƙasƙantar da kanka ka kuma miƙa kanka ga Allah. Idan muka miƙa kanmu ga Allah, haka ma za mu miƙa kanmu ga Kalmar Sa da ikon sa. Yana da sauƙi a ce ka miƙa kanka ga Allah, amma Kalmar Allah ta ce: “Kuna sarayad da kanku ga juna.... Mata, ku yi zaman biyayya ga mazajen ku.... Yara, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku...” (Afisawa 5:21-22; 6:1). A nan ne ba shi da sauƙi. Mutane da yawa suna ikirarin cewa, “Na miƙa kaina ga Allah,” amma idan gwaji ya zo a dangantakar su da wasu mutane, a bayyane yake cewa ba su yi hakan ba.
Idan za ka ƙasƙantar da kanka, dole ne ka zama mai aikatawa. Abu ne mai kyau a wasu lokuta ka kwanta da fuskarka a ƙasa a gaban Allah. Ko ka taɓa yin haka? Ka ce, “Allah, ga ni nan kuma a nan ne na dace! Ni tsutsa ce. Daga ƙura na fito kuma ƙura ce wuri na.” Kana tunani wannan wani abin addini ne na kin ƙarawa? Karanta Littafi Mai Tsarki ka ga yawan mutanen da suka kwanta da fuskokinsu a gaban Allah: Ibrahim, Musa, Dauda, Daniel. Kusan babu ko ɗaya daga cikin manyan tsarkaka na Allah da ba a rubuta cewa ya kwanta da fuskarsa a gaban Allah ba. Idan ya kasance wuri ne mai kyau domin Musa, Dauda, Daniel da sauransu, to, ban tsammani wannan zai rage darajarka ba.
“Idan mutane na waɗanda ake kira da sunana za su ƙasƙantar da kansu.” Wannan shi ne mataki na farko kuma ba za ka iya barin sa ba. Allah na da shirin sa na ruhaniya da aka tsara a matakai: a mataki 1, mataki 2, mataki 3, mataki 4. Har sai ka yi nasara a mataki 1, ba za ka je mataki na 2 ba. Ko da za ka yi ta maimaita mataki na 1 shekaru goma a jere, Allah ba zai sa ka yi gaba ba. Wannan ne ya sa wasu daga cikin ku suka daɗe a mataki ɗaya. Kada ka yi tunani, “Ubangiji, ba zan iya yin mataki na 1 ba, amma zan iya yin mataki na 2. Bari in wuce wannan,zan iya yin na gaba.” A’a, wannan ba zai yi aiki ba!
Mataki na biyu shi ne addu’a. “Idan mutane na waɗanda ake kira da sunana za su ƙasƙantar da kansu, su yi addu’a.” Kada ka fara addu’a har sai ka ƙasƙantar da kanka. Ƙasƙanci na zuwa kafin addu’a.
“Yi addu’a kuma ka nemi fuskata.” Mataki na uku shi ne neman fuskar Allah. Me wannan ke nufi? Na fahimci cewa yana nufin shiga kai tsaye gaban Allah Mai Iko Duka—inda ake kawar da duk wani shinge da duk wani abin da ke kawo cikas, kuma ka kasance fuska da fuska da Allah Mai Iko Duka. Kana iya kasancewa a taron addu’a, amma hakan ba lallai shi ne neman fuskar Allah ba.
Wani saurayi ya zo wuri na yana neman batismar Ruhu Mai Tsarki. Ma'aikaci ne na matasa a Ikkilisiya. Na ce masa zan gan shi da yamma ranar Laraba. Ya ce dole ne ya halarci taron addu'a a wannan yammacin. Na ce, “Ina tsammanin hakan ba zai yi kyau ba.” “oh, sai ya ce, “hakan zai yi. Muna yin addu'a daga karfe 8 zuwa 9.” Wannan taron addu'a ne, amma ba neman fuskar Allah ba. Idan zaka nemi fuskar Allah, ba za ka tsaya ba har sai ka shiga gaban Allah—ko da zai ɗauki dukan dare. Akwai addu'o'i da yawa da ba na neman fuskar Allah ba. Ba a kai inda za a sadu da Allah ba.
Mataki na huɗu: “... su juyo ga barin mugun aikinsu.” Su wanene? Masu shan giya, matasan da ba sa son zuwa Ikkilisiya? A’a, Krista —mutanen Allah! Abubuwan da ke hana falkawa a cikin Ikkilkisiya suke, ba a waje ba. Basu taɓa zama a waje ba.
Ko ka san inda hukunci zai fara? A gidan Allah. “Gama lokaci ya yi,” in ji Bitrus, “da shari’a zata fara a kan gidan Allah” (1 Bitrus 4:17). Don ya bayyana shi sau biyu, ya ƙara da cewa, “Yana farawa da mu da farko.” Sannan ya yi tambaya, “To, menene ƙarshen waɗanda ba su yi biyayya ga bisharar Allah ba?” Haka ne a koyaushe Allah ke yin aiki. Yana farawa da mutanen da suka fi sani. “Dukan wanda am ba shi da yawa, za a nemi da yawa daga gare shi” (Luka 12:48). Ka ce, “Ɗan uwa Prince, ba ni da mugayen halaye.” Ni kuma na ce, “Ba ka taɓa kusantar Allah don ka gani ba. Da ka je gaban Allah, da zaka ga mugayen halayen ka. Gaskiyar cewa ma ba ka da mugayen halaye na nuna nisan da ka yi da Allah.”
Bayan waɗannan matakai huɗu, Allah ya ce, “Zan ji daga sama.” Allah bai yi alƙawarin jin kowace addu’a ba. Ko ka san haka? Na tabbata cewa a cikin Ikkilisiyu da yawa addu’o’i ba sa kaiwa sama fiye da rufin Ikkilisiyar. Allah bai yi alƙawarin jin kowace addu’a ba. A gaskiya ma, Allah ya ce, “Idan muka sani yana jin mu, komi muke roƙo, mun sani muna samun abin da muka roƙa, daga wurinsa” (1 Yohanna 5:15). Wahalar ba sa Allah ya amsa ba ne, amma samun Allah ya ji ne.
“...Sannan zan ji daga sama, zan gafarta musu zunubin su.” Zunubin su wanene? Zunubin karuwa ko na mai shan ƙwayoyi ne? A’a, zunubin Ikkilisiya!
“...Kuma in warkar da ƙasarsu.” A gare ni batun a bayyane yake. Idan ba a warkar da ƙasa ba, to, laifin mutanen Allah ne. Na dubi wannan, na yi addu’a a kansa, kuma na yi bimbini a kansa. Nawayar halin America na zamanin nan na bakin ƙofar Ikkilisiya mai shaida bishara ce. Na gaskata cewa wannan ita ce haƙiƙanin gaskiyar. Idan ba a warkar da ƙasarmu ba, alhakin na kan mu. Ina ɗaukar alhakin tare da ku. Ba wai ina gaya muku wani abin da ke gaskiya game da ku ba amma har da ni.
Warkarwa Ta Wurin Yin Addu'a
Ta yaya za mu iya kawo warkarwa? Zan yi muku magana game da addu'a. Zan yi koyarwata a kan ayoyi hudu na farko na 1 Timothawus sura ta 2:
- “Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu'a, ana godo, ana godewa Allah, saboda dukan mutane;
- “da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan muƙamai, domin mu zauna lafiya, rai a kwance,muna bin Allah sosai cikin natsuwa.
- “Wannan ƙyaƙƙyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu;”
- “wanda yake son dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.
Bari mu dubi waɗannan kalmomi.
Bulus ya ce, “Da farko, ku yi addu’a!” Idan ka tsallake addu’a, za ka iya samun shirye-shirye iri iri da tsare-tsare da yawa, amma ba za ka sami ikon yin aiki da su ba. Yana kama da idan kana da wayoyin wutar lantarki, amma kuma ba ka haɗa su da janareta ba. Babu abin da zai yi aiki. Wayoyin na iya kasancewa cikin tsari mai kyau, kuma fitilun na iya zama masu ban mamaki, amma ba za ka sami sakamako ba, domin babu wuta. Ikon Ikkilisiyar Kristi ita ce addu’a, kuma daidai ne da Bulus ya ce, “Da farko, ku yi addu’a!”
To, me ya ce mu yi addu'a a kai? Na farko, “domin sarakuna da duk waɗanda ke kan mulki.” A yanzu dai, abin da na sani shi ne cewa yawancin mutanen Allah da suke shelar bishara, da ƙyar suke yin addu'a domin waɗanda suke mulki, balle su yi musu addu'a da farko. Idan kai ɗan ɗarikar Episcopal ne, zan tabbatar maka cewa a littafin addu'o'inku akwai addu'a domin waɗanda suke kan mulki. Abu ne mai kyau na samun abu kamar haka a ciki. Amma zan gaya maka wani abu daga abin da na sani da kaina a matsayina na ɗarikar Anglican. Abu ɗaya ne a karanta addu'a, amma wani abu kuma shi ne yin addu'ar. Waɗannan abubuwa biyu ba abu ɗaya ba ne. Mutane da yawa suna karanta abubuwa daga littafin addu'o'i kuma idan ka tambaye su bayan minti biyar abin da suka faɗa, ba za su iya tunawa ba. Wannan dai tsari ne kawai.
Menene kan magana na farko don addu’a? “Dukan waɗanda suke cikin mulki”: firayim minista, majalisar zartarwa, ‘yan majalisa, mashawartan birni, kwamishinonin ‘yan sanda, duka. Ko kuna yi musu addu’a? Yaushe ne ƙarshen da kuka yi addu’a domin gwamnati? Wannene kuka yi a ƙarshe—zargin su ko yi masu addu’a? Idan kuna yi wa waɗanda suke kan mulki addu’a, to, za ku rage abubuwan da zaku zarge su a kai. Allah bai kiraye ku don ku yi sukar su ba, Ya kiraye ku don ku yi addu’a. Idan ba kwa yin addu’a, to, kuna rashin biyayya. Ni ɗan Birtaniya ne, amma ina zaune a Amerika, ina yi wa shugaban ƙasar addu’a kusan kowace rana. Matata za ta shaida hakan. Muna yin addu’a tare, kuma da ƙyar wata rana ta wuce da ba za mu yi addu’a domin shugaban wannan ƙasar ba. Na tabbata yana buƙatar addu’a. Menene za mu yi addu’a a kai game da waɗanda suke kan mulki? Wannan wani abu ne game da adduʻa da ya ke a bayyane da zan samu a ko’ina cikin Littafi Mai Tsarki. A sashi na biyu na aya ta 2 an gaya mana mu yi addu’a “domin mu sami zaman lafiya, rai a kwance muna bin Allah sosai cikin natsuwa.” A cikin ƙwayar magana guda mai sauƙi: “kyakkyawar gwamnati.” Ba za ku yarda da haka ba? Idan za mu yi zaman lafiya, rai kwance, muna bin Allah sosai cikin natsuwa, dole ne mu sami kyakkyawar gwamnati.
A aya ta 3 Bulus ya ci gaba, “Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa a gun Allah Mai Cetommu.” Menene “wannan” ke nufi? Ga maganar da ta gabata, “...domin mu yi rayuwa cikin kwanciyar hankali da salama cikin dukan ibada da girmamawa”—a taƙaice, “domin mu sami kyakkyawar gwamnati.”
Me yasa Allah yake son nutsuwa da tsari da kyakkyawar gwamnati? Domin wani dalili na gaske wanda za a aikata. Domin yana son dukan mutane su sami ceto su kuma kai ga sanin gaskiya. A wanne hali ne ya fi sauƙi a kawo gaskiya ga dukan mutane? A ƙarƙashin gwamnati mai adalci da rashin son zuciya kuma mai kiyaye doka da tsari da 'yancin jama'a? Ko a ƙarƙashin gwamnatin da ba za ta iya shawo kan tashin hankali da hargitsi ba kuma ba za ta iya magance lamarin ba kuma mai rashin adalci da mulkin kama-karya? Wacce irin gwamnati ce ta ke da sauƙi wajen kawo dukan mutane ga gaskiya? Duk wani mai hankali zai bada amsa: kyakkyawar gwamnati. Wannan ne dalilin da ya sa Allah ke son kyakkyawar gwamnati, domin tana taimaka yaɗuwar bishara, wadda ita ce manufarsa a wannan zamani. Babu abin da yake da wuya, babu abin da yake da sarƙaƙƙiya, gaba ɗaya abu ne mai azanci wanda kuma za a iya yi.
Lambar: TL-L801-100-HAU