Yaƙi domin Ƙasar Mu

Derek Prince
*First Published: 2024
*Last Updated: December 2025
8 min read
A cikin dukan wannan koyarwar mai sashi uku na jerin legacy, bisa ga littafin Derek Prince mai muhimmanci sosai, Yin rayuwa a Matsayin Gishiri da Haske, mun fahimci matsayi, dama, da nawayar da Allah ya ba mu a matsayin mu na Krista domin mu yi canji a cikin ƙasar da muke zaune.
A cikin littafin sa, Derek ya faɗi wannan maganar mai ƙarfi: “Ikkilisiya ce kaɗai, daga cikin dukan kungiyoyin da ke duniya a yau, take da ikon canza al’amarin duniya ya zama da kyau.” A cikin wannan wasiƙa ta uku kuma ta ƙarshe, Yin Yaƙi domin Ƙasarmu, Derek ya dubi wata muhimmiyar ƙa’ida: yaƙi na ruhaniya da muke fuskanta yayin da muke yin addu’a don ƙasashenmu. Fahimtar wannan zai taimake mu wajen sauke nauyinmu na zama gishiri da haske a ƙasar da Ya kira mu.
Ziyarar Mala'ika
Za a iya samun ƙa'idar a cikin labarin abin da annabi Daniel ya fuskanta ta wajen hamayya ta ruhaniya. Wannan labarin ya fara da wani bayani mai sauki daga Daniel: “A waɗannan kwanaki, ni Daniel, ina fama da bakin ciki har mako uku” (Daniel 10:2). Daniyel ya sadaukar da kansa na tsawon makonni uku ga addu'a ta musamman da azumi domin neman fuskar Allah sosai. A ƙarshen makonni ukun, amsar addu'ar Daniel ta zo ta wurin ziyarar Mala'ika Jibra'ilu.
“Sai ya [Jibra’ilu] ce mini, ‘Kada ka ji tsoro, Daniel, gama tun daga ranar da ka ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’ar ka; amsar addu’arka ce ta kawo ni.’” (Daniel 10:12)
An ji addu'ar Daniyel tun a ranar farko, amma amsar ta zo a rana ta ashirin da ɗaya. Me ya sa sai da ya jira har makonni uku? Ga dalilin da Jibra’ilu ya bayar:
" Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya; amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa." (Daniel 10:13)
Ka lura cewa “sarki mai mulkin Farisa” ba mutum bane; shi ne ruhun da ke mulkin duniyar Farisa. Lokacin da Daniel ya fara addu’a don maido da Isra’ila daga bauta (wanda ya ke da alaka ta kusa da daular Farisa), sai Allah ya amsa nan da nan ta hanyar aiko Mala’ika Jibra’ilu da amsar zuwa ga Daniel, wannan mugun iko da ba a ganinsa ne ya tsare Jibra’ilu a sararin sama har kwana ashirin da ɗaya.
Dabarar Na Gare Mu
Ko ka fara fahimtar dalilin da ya sa amsar addu'arka a wani lokaci take jinkiri? Ka iya gani kamar Daniel cewa, kana cikin yaƙi na ruhaniya? Wannan labarin da ke sama na nuna wata muhimmiyar gaskiya: addu'ar Daniyel a duniya ce ta sa mala'iku aiki a sama.
Aboki, dabarar na hannun Ikkilisiya; ba mala'iku ba. Sakamakon ya danganta ne ga abin da muka yi. Mala'iku “ruhohi ne masu hidima, da aka aiko su don su yi hidima ga waɗanda za su gaji ceto” (Ibraniyawa 1:14). Ba mu ne ke jiran mala'iku ba; mala'iku ne ke jiran mu.
Lokacin da ka fara addu'a, ka na tada mala'iku tsaye—ba nagartattun mala'iku kawai ba har ma da miyagu waɗanda kake dagula mulkinsu. Wataƙila ka fara gane gaskiyar wannan! Ka lura cewa addu'o'in Daniyel ne suka buɗe wa mala'ika Jibra'ilu hanya har ya zo.
Ka fahimci abin da ya kamata mu yi?
Dangane da yaƙi na ruhaniya, mu ne mutanen da da ke da dabarar. Duniya na jiran mu—duniyarr da ba a gani da kuma duniyarr da ake gani. Mu ne mutanen da ke yanke shawara a ƙarshe a kan makomar kasashe. Mu ne gishirin duniya; mu ne hasken duniya.
Almasihu Na Aiki Ta wurin Jikinsa
Akwai wani babban dalili da ya sa muka zama gishirin duniya da hasken duniya. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana a fili, mu ne jikin Yesu Kristi (duba, alal misali, Afisawa 1:22–23), Yesu Kristi kuma yana aiki ta wurin jikinsa. Allah ba zai ajiye Ɗansa Yesu Kristi a gefe ba, domin hakan zai zama ƙasƙantarwa a gare Shi. Haka kuma, ba zai ajiye Ikkilisiya gefe ba, wadda ita ce jikin Ɗansa. A cikin ikonsa, Allah ya iyakace kansa ta wajen yin muhimman abubuwan da suka kamata ayi ta wurin Ikkilisiya. Kuma 'Ikkilisiya' na nufin kai da ni.
Na gaskata ka fara gane wannan gaskiyar: kana da muhimmanci. Ina jin bacin rai a kullum idan na ji Krista na magana game da kansu a matsayin ba su da muhimmanci, mutane marasa gata. Komai ya danganta gare ka. Ƙasar ka na dogara gare ka; shugabanninka na siyasa na dogara gare ka; tarihi ma na dogara a gare ka. Lokaci ya yi da za ka fahimci wannan.
An ƙara nuna mana ayyukan ruhaniya a cikin sura ta ashirin da huɗu ta Ishaya. Wannan ayar na nuna hukunci na ƙarshe mai girma, mai ban mamaki wanda zai kawo ƙarshen wannan zamani. Lokaci ne da duk duniya za ta yi juye-juye ta kai ta komo, za a yamutsa ta, kuma za a girgiza ta kamar ɗaki ko rumfa lokacin girgizar ƙasa. An bayyana zuwan Ubangiji cikin ɗaukaka wanda zai faru dab da ƙarshen wannan zamanin. Ishaya 24:21 tana cewa:
"Za ya zama kuwa a cikin waccan rana, Ubangiji za ya yi wa rundunan maɗaukaka na sama hukunci, da sarakunan duniya a ƙasa."
A nan mun sake ganin mulkokin biyu: “sarakunan duniya” da “taron wadanda aka daukaka” (a cikin sararin sama) waɗanda Allah zai hukunta. Haka wannan yake: a bayan abin da ake gani akwai wanda ba a gani; a bayan halitta ta zahiri akwai ta ruhaniya. Kuma abin da ke faruwa a duniyar ruhaniya tsayayye ne.
Lokacin da ka sami nasara a duniyar ruhaniya, to, ka sami nasara—shike nan. Duk abin da ya biyo baya a duniyar halitta ta zahiri, na zamantakewa, da tarihi sakamako ne na na abin da aka ci nasararsa a duniyar ruhaniya. Shi ya sa Ikkilisiya take da cikakken ikon canza halitta ta zahiri da kuma tarihi. Abin da ake bukata kawai shi ne mu sami nasara a duniyar ruhaniya.
Allah Ya Ba Mu Makamai Na Ruhaniya
Kafin a rufe wannan jawabin, bari in ja hankalinka ga wata aya a ƙarshe. Daya daga cikin abubuwan da nake kauna game da Littafi Mai Tsarki shi ne cewa yana bada bayani daki-daki. Tun da muna cikin wata kokuwa ta ruhaniya, wadanne irin makamai muke buƙata? Makamai na ruhaniya. Kuma su ne abin da aka ba mu:
“Ko da yake cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne. Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu karfi, muna kada masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.” (2 Korintiyawa 10:3–5)
Muna tafiya a cikin duniya, muna rayuwa a cikin jikkuna na duniyar da ke ƙarƙashin ikon lokaci. Amma yakin mu ba a wannan duniyar yake ba. Yakinmu yana cikin duniyar ruhaniya. Daidai ne, makaman da Allah ya ba mu sun daidai suke da duniyar da muke yaƙi a ciki. Ba za mu iya yin nasara da bindigogi, ko tankunan yaƙi, ko harsashai masu linzami ba, domin ba su iya kaiwa ga abokin gaban da muke yaki da shi.
Shugabanni a zamanin mu na cikin takaici domin ba su da hanyoyin shiga tsakani a wurin da an riga an ɗauki shawara. Amma kai da ni muna da hanyoyin. Makaman yakin mu ba na jiki ba ne amma na ikon Allah ne don rushe ganuwar Shaiɗan a duniyar da ba a gani.
Ka lura da kalmomin da ke cikin 2 Korintiyawa 10:5 waɗanda ke nuna yadda makamanmu ke shafar ɗan adam:
“…muna kada masu hujjoji a cikin zace-zacen su, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.”
Maƙamai masu ƙarfi, hujjoji, sani, da zace-zace duk suna cikin duniyar da ba a gani. Wannan duniyar ce ke sarrafa tunanin mutum, zace-zacen da sani. Yaƙin Ikkilisiya na cikin wannan duniyar, Allah kuma ya ba mu makaman ruhaniya da za su tabbatar da nasara ta ruhaniya—idan muka yi amfani da su.
Sa kai don yin Hidima
Za ka iya tambayar kanka, Ta yaya zan yi amfani da waɗannan makaman ruhaniya? Na gaskata cewa ya dace in gayyace ka ka yi addu'a kan wata kan magana ta musamman: cewa Allah ya shirya ka ya kuma ba ka damar taka rawar da yake sa ran ka taka a duniya.
Watakila kana jin cewa har yanzu, ba ka taka rawar da ta kamata ba. Wataƙila ma ba ka san cewa Allah ya kira ka ga yaƙi na ruhaniya ba. Amma yanzu, da ka gani a cikin maganarsa cewa an kira ka, ka zama mai aikin sa kai da yardar rai.
Idan haka ne, to, ina ba da shawara ka je gaban Allah a daidai wannan lokaci da ka san gaskiya ka kuma fada Masa yardarka. Ka miƙa kanka ga Allah a matsayin mai aikin sa kai domin yaƙi na ruhaniya—musamman a matsayin mai aikin sa kai a cikin yaƙi na ruhaniya da zai daidaita makomar ƙasar ka.
*Prayer Response
Uba na sama, ina miƙa kaina gare Ka a matsayin mai aikin sa kai don yaƙi na ruhaniya wanda Ka kira ni. Ina roƙon Ka Ka yi amfani da ni musamman don yin yaƙi na ruhaniya da ake yi a kan ƙasata a cikin sama a yanzu haka.
Ina roƙon ka ka more ni, kamar Daniel, don cika manufarka a duniya ta wurin addu'a da yaƙi na ruhaniya a cikin Ruhu. Ka shirya ni in taka rawa da ta kamata a duniyar da ka shirya mani, yayin da nake dogara gare Ka da ikonKa mai girma. A cikin sunan Yesu, amin.
Lambar: TL-L160-100-HAU