A cikin wannan jerin koyarwa na tasiri mai sassa uku, wanda ya samo asali daga fitaccen littafin Derek Prince, wato, Rayuwa a Matsayin Gishiri da Haske, muna duba jigon aikinmu da nawayarmu a matsayin mu na Krista zuwa ga al'ummomin da muke rayuwa a cikin su.

Wasikar mu ta baya ta gabatar da yadda Yesu ya bayyana Ikkilisiya, wanda ya bayar a wa’azin da aka sani da suna ‘Koyarwa a kan Dutse,’ wanda aka rubuta a Matta 5:13–14. Mu ne "birnin da aka gina a kan tudu," wanda idanun duniya ke kallonsa. Mu ne kuma 'hasken'—haske ɗaya kacal—wanda ke haskaka Almasihu ga mutane masu mutuwa.

A cikin wannan wasikar, za mu mai da hankali kan aikinmu na uku: mu ne 'gishirin duniya.' Har ila yau, kalmar 'gishirin' (n) a keɓe ta ke. Wannan na nufin cewa duniya ba ta da wani gishiri—mu ne kaɗai gishirin da duniya take da shi. Akwai hanyoyi da yawa da za a iya morar muhimmancin gishiri. Duk da shike, ni ba masanin kimiyya ba ne, zan yi bayani a cikin sauƙi. Bari in nuna wasu tabbatattun abubuwa game da gishiri.

Gishiri Na Ba da Ɗanɗano

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan gishiri shi ne bayar da ɗanɗano ga abin da in babu shi babu ɗanɗanon. A cikin Ayuba 6:6, Littafi Mai Tsarki ya rubuta Ayuba na cewa:

“Amma wanene zai iya cin abinci ba gishiri? Akwai daɗin ɗanɗano ga farin ruwan ƙwai?”

Amsar ita ce a'a. Shi ya sa, idan kana cin farin kwai, idan kai ma kamar ni ne, za ka barbaɗa gishiri a kai don ya ba shi ɗanɗano.

Haka kuma, Krista ne gishirin duniya. Muna nan domin mu ba duniya ɗanɗano a gaban Allah. Da ba domin mu na cikin duniya ba, da babu wani dalili da zai sa Allah ya ci gaba da nuna wa duniya alheri da jinƙai ba. Mu ne kaɗai dalilin da ya sa duniya ta zama karɓaɓɓiya a gare Shi, mu ne kaɗai muka jinkirta hukuncin ƙarshe da fushin Sa a kan duniya mai ƙin Kristi. Muddin muna nan a duniya, hakkinmu ne mu yi rayuwa yadda za mu danƙa wannan duniyar ga Allah.

Domin Ƙwayar Gishiri Goma

A cikin Farawa 18, mun karanta yadda Ubangiji ya tsaya a gidan Ibrahim a kan hanyarsa ta zuwa birnin Saduma. Ubangiji ya faɗa wa Ibrahim abin da yake shirin yi—ya zo don ya kawo hukunci a kan wannan birni. Ibrahim ya damu sosai a kan abin da Allah ya faɗa masa, domin ɗan ɗan’uwansa, Lutu, da kuma iyalin Lutu suna zaune a Saduma. Don haka, Ibrahim ya tafi tare da Ubangiji zuwa wajen Saduma, yana roƙon Sa da gabagaɗi Ya yafe wa wannan mugun birnin. Ya nemi yin “sasanci” da Ubangiji (idan zan mori wannan kalmar) bisa ga yawan mutane, yana cewa, a zahiri, “Ubangiji, idan akwai mutane hamsin masu adalci a cikin wannan birni, za Ka yafe wa birnin?” Ubangiji ya ce i,.

Sai Ibrahim ya ce, “Idan akwai arba'in, za Ka yafe wa birnin?” Ubangiji ya ce i,.

Ibrahim ya ce, “Idan akwai talatin, za Ka yafe wa birnin?” Ubangiji ya ce i,.

Ibrahim ya ce, “Idan akwai ashirin, za Ka yafe wa birnin?” Ubangiji ya ce, i,.

Sai Ibrahim ya ce, “Idan ka yarda, Ubangiji, kada dai Ubangiji ya husata, zan sake yin magana sau ɗayan nan kadai. Da a ce za a sami mutane goma masu adalci a cikin wannan birni, za ka yafe saboda mutane goma masu adalci da ke cikin sa?” Ubangiji ya ce, “I, zan yi.” Abin takaici shi ne, Ubangiji bai sami mutane goma masu adalci a Saduma ba.

Duk lokacin da na karanta wannan labarin, sai in kasa daurewa amma sai in yi mamaki ko Ibrahim ya yi wata ‘yar ƙididdiga a zuciyarsa. Ko wataƙila ya ce wa kansa, "Akwai ɗan ɗan'uwana da matarsa, da 'ya'yansa mata marasa aure, da 'ya'yansa mata masu aure... a tsakaninsu, ashe, ba za su iya kai mutane goma masu adalci ba?" Da a ce Lutu yana yin aikinsa, da sun kai wannan yawan. Amma Lutu yana daya daga cikin Masu Bin da suka kunyatar da Allah. I, shi Mai Bi ne. Ya ji dukan abubuwan da Allah ya faɗa wa Ibrahim, amma bai yi rayuwa bisa ga wannan fahimtar ba.

Kasancewar Mu na Kawo Canji

Mun sami wata dawwamammiyar ƙa'ida a cikin misalin Lutu. Da akwai adalai goma, da Allah ya yafe wa dukan birnin. Wannan kaso zai yi amfani har a yau ma. Ƙwayar gishiri goma na iya ba da shaidar komai game da Allahn da ake bautawa. Kamar yadda na fada a baya, aikin mu shi ne mu zama waɗanda za su danƙa duniya gare Shi. Kasancewar mu na kawo canji. Kasancewar mu na sa Allah ya ci gaba da nuna wa duniya jinƙai ta hanyar da ba lallai ya yi hakan ba.

Ya kamata kowane Mai Bi ya zama ƙwayar gishiri a wurin da Allah ya ajiye shi. Allah bai tara duk Masu Bi a wuri guda ba, kamar yadda ba shi yiwuwa mu zuba dukan gishirin da muke da shi a cikin abinci guda ba. Zai yi ɗaci! An warwatsa kowannen mu zuwa wani wuri na musamman don ya zama gishiri guda mai ba duniya ɗanɗano —ko da wannan wuri zai kai ka inda za ka iya kai ga cika sharaɗin Allah na musamman, bayyananne, mai sauƙi, kai tsaye ne. Idan muka yi hakan, za mu iya canzawa da kuma dakatar da koma-bayan abubuwa. A wani gefen, idan ba mu yi hakan ba, zai zama laifin mu ne, kuma mu ne za mu fara shan wahala mafi muni. Idan muka sha wahala saboda gazawarmu wajen cika ƙa’idar Allah, mun cancanci hakan.

Kafin mu ci gaba, bari in bayyana sauƙaƙƙiyar hanyar amfani da abin da muka tattauna zuwa yanzu. Idan ba ka gamsu da abin da na gabatar ba, ko ta yaya ne, kada ka tilasta wa kanka sai ka amsa. Amma idan ka gaskata cewa abin da na bayyana maka abu ne na zahiri da Littafi Mai Tsarki ya koyar, to, ina gayyatarka ka sake karanta Matta 5:13:

"Ku ne gishirin duniya; amma idan gishiri ya rabu da zaƙin sa, da me zaya gyaru? " Nan gaba ba shi da amfani ga komai ba, sai a yar, a kattake ƙarƙashin sawun mutane.’’

Ina so in sa wannan ayar ta sama ta zama taka a yanzu domin ka iya amfani da maganar Yesu a rayuwar ka. Mun fahimci cewa Yesu na magana da Krista ne, mu ne kuma Kristan. Saboda haka, inda aka ce "Ku..." ina so ku karanta shi a matsayin "Mu..." Kuma, a tsakiyar ayar, inda ta ce, "ba shi da sauran amfani," ina so ku karanta, "Ba mu da wani amfani." Na gaskata cewa wannan canjin ya dace kwarai da gaske.

“Bayan ka faɗi abinda ke ƙasa, za ka amsa ga Allah ko yanzu ko da nan gaba bisa ga abin da ka faɗa. To, idan ka shirya, gwada shi yanzu, da murya mai karfi:

Mu ne gishirin duniya; amma idan gishiri ya rabu da zaƙin sa, da me zaya gyaru? Ba mu da wani amfani, sai a yar, a tattake mu a ƙarƙashin sawun mutane.

10
Raba