Hasken Duniya

Teaching Legacy Letter
*First Published: 2024
*Last Updated: December 2025
8 min read
A duk faɗin duniya, al'ummomi na fuskantar rikice-rikice iri-iri. A kokarin cika nayawar mu a matsayin mutanen Allah, muna da muhimmiyar rawa da za mu taka a matsayin gishiri da haske a cikin sauye-sauyen da ake buƙata a ƙasashen mu.
A cikin gabatarwar wannan littafi mai inganci wanda aka samo wannan jerin daga cikinsa, wato, Yin Rayuwa a Matsayin Gishiri da Haske, Derek Prince ya rubuta waɗannan kalmomi:
“Na amince sosai da cewa ƙasashen mu na buƙatar canji kuma za a iya canza su… kuma mu ne mutanen da ya zama dole mu kawo wannan canjin. Manufata ita ce in nuna maka yadda za mu iya cimma hakan daga cikin maganar Allah.”
Manufar da aka bayyana a sama za ta zama tsaikon da za mu mayar da hankali a kai cikin jerin koyarwarmu ta Legacy mai sashi guda uku, 'Yin Rayuwa a matsayin Gishiri da Haske'. Sashi na 1 ya fara da binciken abin da Yesu ke nufi da kalmomin, "Ku ne hasken duniya" (Matta 5:14).
Hasken Duniya
Krista gaba ɗaya sun amince da koyarwar kan Dutse a matsayin ma'aunin bangaskiya da rayuwar da Yesu ya tanadar don dukan Masu Bi. Ba koyarwa ce ta musamman ga waɗanda suke shugabanci kaɗai ba, kamar malamai, manzanni, annabawa, masu bishara, ko masu wa'azi. A cikin wannan ayar ta Littafi Mai Tsarki, Yesu ya bayyana nufin Allah, ko ma'aunin Allah, wanda ya shafi kowane amintaccen Krista.
A ayar mu ta buɗewa, ina so in gabatar da abin da Yesu ya fada a Matta 5:13–14:
“Ku ne gishirin duniya; amma in gishiri ya sane, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani sai dai a zubar mutane kuma su tattake. Ku ne hasken duniya. Ai birni da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa.”
Da yake magana da dukan Krista, Yesu ya fada mana abubuwa uku masu muhimmanci game da kan mu: mu ne...1) Gishirin duniya. 2) Hasken duniya. 3) Birnin da aka gina bisa tudu da ba shi ɓoyuwa. A matsayin gabatarwa ga kan magana ta, ina so in nuna wasu daga cikin bayyanannun sakamakon waɗannan maganganu uku. Za mu canja tsarin bisa ga yadda Yesu ya faɗe su, da farko a wannan wasiƙar za mu fara da ayyuka biyu daga cikin ayyuka ukun da Ya ba mu. A wasiƙarmu ta gaba, za mu tattauna bayanin farko.
Addinin Krista a Fili
Da farko, mu ne “birni da aka gina a kan tudu [kuma] ba shi ɓoyuwa” (Matta 5:14). Wannan tabbatacce ne a kan kowane mutum da ya bayyana bangaskiyarsa ga Yesu Kristi a bainar jama’a a matsayin Mai Ceto da Ubangiji. Da zarar ka yi wannan furuci a bainar jama’a, ka zama birnin da aka gina a kan tudu. Ba ka ɓoyuwa. Ka fito fili: za a zuba maka idanu daga kowane ɓangare, a kowane lokaci, ko a makaranta, ko a wurin aiki, ko a masana'anta ko a ofis. Za a sa maka idanu don ganin ko addinin ka na gaskiya ne. Me wadanda ke kallon ka ke tambayar kansu game da kai? Ko bangaskiyarka ta ainihi ce? Ko da gaske ka gaskata abin da ka ke ikirari ka gaskata? Ko ka na aikata shi a rayuwar ka?
Mutane za su yi nazari kan kowane bangare na rayuwar ka—rayuwar iyalin ka, rayuwar kasuwancin ka, rayuwar zamantakewar ka, da sauransu. Haka kuma, za su yi nazari a kan halin ka da shaidar Ikkilisiyar da kake halarta. A mafi yawan lokuta, za su yanke hukunci kan addinin Krista daga abin da suka gani a gare ka. Kai ne birnin da aka kafa a kan tudu.
A lokacin da na ke matashi a cikin Ikkilisiyar Anglican a Biritaniya, na yanke shawara cewa addinin Krista kasasshe ne. Na samo ra'ayina ta hanyar kallon mutanen da ke kewaye da ni kuma na yanke shawarar cewa ba su gaskanta abin da suke cewa sun gaskanta ba.
Saboda haka, dole ne ka gane cewa da zarar ka furta bangaskiya ga Yesu Kristi, ka fito fili. Ba za ka iya kauce wa wannan gaskiyar ba. Idan ba ka son fitowa fili—idan ba ka son a kalle ka, a shar’anta maka, ko kuma bincike ka—to, kada ka furta bangaskiya ga Yesu Kristi. Amma idan ka furta bangaskiya ga Yesu Kristi, wannan shi ne zai biyo baya: mutane za su fara lura da kai. Daga wannan lokacin zuwa gaba, za ka zama birni da aka gina a kan tudu wanda ba ya ɓoyuwa.
Babu Wani Haske
Na biyu, Yesu ya ce, “Ku ne hasken duniya” (Matta 5:14). A lokuta da wurare dabam dabam a rayuwata, na koyar da harshen Turanci. Na fahimci Turanci sosai har da na san cewa idan Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ku ne hasken duniya,” yana nufin mu ne hasken. A wata fuskar, babu wani haske dabam. Kalmar “the” (A turanci) da aka yi amfani da ita a nan keɓantacciya ce. Mu kaɗai ne hasken.
Yesu ya furta ya ce: “Muddin ina duniya, ni ne hasken duniya” (Yohanna 9:5). Amma yanzu da ba ya cikin duniya a jiki, mu ne wakilansa. Saboda haka, a madadin sa, mu ne hasken duniya. Idan ba mu bayar da haske ba, babu wani wurin da duniya za ta juya ko ta nemi haske. Wannan na nufin cewa duniya gaba ɗaya tana dogara a kan Krista don haske.
Sabon Mai
Akwai wani misali mai sauƙi a cikin Tsohon Alkawari da ke koya mana muhimmancin kasancewar mu hasken duniya. A cikin alfarwa da Allah ya umurci Musa ya gina, akwai ɓangarori biyu. Na farko ana kiransa Wuri Mai Tsarki, na biyu kuma ana kiransa Wuri Mafi Tsarki. A cikin Wuri Mai Tsarki, akwai kayayyakin aiki uku kawai, kuma ɗaya daga cikinsu ita ce fitila mai rassa bakwai.
A cikin Littafi Mai Tsarki, fitila a koyaushe na wakiltar Ikkilisiya. Za mu yi kuskure idan muka dauki wannan fitilar daidai da irin wadda muke da ita a yau—fitilar kandur da ke tsaye a cikin waɗansu irin mazauni. A cikin alfarwar, "fitilun" kwanoni ne da ke da kwararo cike da mai. Akwai ƙananan igiyoyi a cikin man, wanda ke samar da haske ta hanyar kunna man da ke jikin igiyar, idan babu mai a cikin fitilun, kuma idan ba a kunna ba, fitilun ba za su bayar da haske ba. Kuma, a cikin Wuri Mai Tsarki, fitilar ita ce kadai ke samar da haske. Idan babu hasken da ke fitowa daga fitilar, babu haske kwata-kwata.
Ka ga yadda wannan ya zama gaskiya game da Ikkilisiya? Haka mu ma, mu ne kaɗai hasken. Babu wani haske na dabam. Mu ne fitila mai rassa bakwai. Muna bayar da haske idan an cika mu da mai idan kuma an kunna man da ke cikin mu.
A cikin Littafi Mai Tsarki, a koyaushe alama ne na Ruhu Mai Tsarki. Wannan alamar tana nuna mana cewa Ikkilisiya za ta iya bayar da haske ne kaɗai idan an cika ta da Ruhu Mai Tsarki, Allah kuma ya kunna mata wuta.
Ainihin Manufar mu
Aikin fitilar shi ne ta ba da haske kan kayan da ke fuskantar ta, wanda shi ne teburin zinariya na gurasar ajiyewa a cikin Wuri Mai Tsarki. Gurasar ajiyewa, babu shakka, na wakiltar Yesu Kristi, wanda ya ce,
“Ni ne gurasa mai ba da rai…. Ni ne gurasar rai da ya sauko daga sama. Kowa ya ci gurasar nan, zai rayu har abada; har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.” (Yohanna 6:48, 51)
Dukan manufar fitilar ita ce ta yi abu ɗaya tak abu guda kawai: ta haskaka teburin gurasar ajiyewa. Wannan gaskiyar ta yi daidai da Ikkilisiyar Yesu Kristi. Muna nan a duniya don manufa ɗaya tak manufa daya kawai: mu haskaka Yesu, Gurasar Rai. Kuma za mu iya yin wannan ne kaɗai idan mun cika da Ruhu Mai Tsarki idan kuma Allah ya kunna mana wuta.
A nan muna da babban misalin Ikkilisiya. Idan babu fitila, babu wurin samun haske a Wuri Mai Tsarki. Idan babu Ikkilisiya, babu haske a duniya. Kamar yadda fitila za ta iya bayar da haske ne kaɗai idan an cika ta da mai an kuma kunna mata wuta, Ikkilisiya za ta iya bayar da haske ne kaɗai idan an cika ta da Ruhu Mai Tsarki an kuma kunna mata wuta. Fitilar tana da abu guda daya kaɗai da take haskawa—teburin gurasar ajiyewa. Ikkilisiya na da “abu” guda daya kaɗai da za ta haskaka—wato, Ubangiji Yesu Kristi.
Dalili guda ɗaya da ya sa ni da kai, a matsayin Krista, muke a nan shi ne mu haskaka Yesu Kristi, Gurasar Rai. Wannan ita ce babbar manufar kasancewar mu a duniya. Duk wani abin da za mu iya yi na biyu ne ga wannan. Mu ne hasken duniya.
Bari mu roƙi Ubangiji yanzu ya taimake mu mu cika manufarsa a gare mu:
*Prayer Response
Ya Ubangiji Yesu, muna sake miƙa kanmu gare Ka. Ka sake cika mu da man Ruhu Mai Tsarki, ka kunna mu, Ubangiji, domin hasken mu ya haskaka. Muna miƙa kanmu sosai don mu nuna Yesu Kristi ga duniya da ke kewaye da mu, mu haskaka ɗaukakar ka ta yadda za ta jawo mutane da yawa zuwa gare Ka. Amin.

*Free download
*This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.
Zazzage PDFLambar: TL-L158-100-HAU