Logo
Logo
Learn
LittattafaiKwasa kwasan nazarin Littafi Mai TsarkiKayan Aiki
HidimomiGame da
Najeriya Flag Icon

Menu

  • Gida
  • Learn +
    • Hidimomi
    • Game da +
      • Haɗa Hannu +
        • Tuntuɓa +

            Samu eBook kyauta

            Fara tarin Derek Prince tare da eBook kyauta lokacin da kuka yi rajista ga wasiƙarmu.

            Koyarwar Littafi Mai Tsarki Kyauta
            Logo
            Logo
            GidaLearnHidimomiGame daBa da gudummawa

            Haƙƙin Mallaka © 2025 Derek Prince Ministries. An kiyaye duk haƙƙoƙin

            TuntuɓaSirriHaƙƙin MallakaLicensesTaswirar Yanar Gizo
            Gida
            Kayan Aiki
            Ruhun Gaskiya

            Ruhun Gaskiya

            Derek Prince

            Teaching Legacy Letter

            11
            Raba
            Saurara
            Hausa

            *Article Language

            Gabatar da Shaida

            Bayar

            Ba da

            *First Published: 2019

            *Last Updated: December 2025

            10 min read

            Bari mu fuskanta—a cikin al’adunmu a yau, ainihin ra’ayin cikakken gaskiya yana fuskantar babban hari. Amma kamar yadda Derek Prince ya nuna a cikin wannan bugu na jerin abubuwan Legacy na koyarwa, ainihin yaƙin gaskiya ba shine wanda ke faruwa "a can ba." Ita ce ke faruwa a cikin zuciyar dan Adam. Taimaka mana fahimtar da cin nasara wannan yakin shine Derek ya mayar da hankali a cikin wannan wasika.

            A cikin wannan jerin wasiƙar Koyarwa, Wanene Ruhu Mai Tsarki?, manufarmu ita ce fahimtar asiri na Ruhu Mai Tsarki. Nazarinmu na maganar Allah zuwa yanzu ya ba mu damar ganin kasancewar Ruhu Mai Tsarki a cikin halitta; Matsayinsa na musamman a cikin Murhunniya; Kasancewarsa madawwami, Masanin komai, da Kasancewarsa a ko'ina. Sashin da muka kammala ba da daɗewa ba, ya mayar da hankali ne kan tsarkin Sa—yana tunasar da mu wannan fanni na halinsa: Shi Ruhu Mai Tsarki ne.

            Kamar yadda nake jaddadawa a koyaushe, tushen dangantakar mu da Ruhu Mai Tsarki shine Littafi Mai Tsarki, wanda ke nuna mana yadda za mu iya saninsa a zahiri. Yesu ya yi magana da almajiransa game da wannan ma'anar sanin a cikin Yahaya 14:16-17:

            “Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai-Taimako, ya kasance tare da ku har abada— shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba; ku kam kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.”

            Sa’ad da Yesu ya yi alƙawari zai roƙi Uba ya aiko da Ruhu Mai Tsarki, ya ba wannan Mai Taimako suna na musamman: “Ruhu na gaskiya.” Alƙawarin Yesu yana ɗauke da gargaɗin cewa duniya ba za ta iya karɓar wannan Mai Taimakon ba.

            Duniya Ba Za Ta Iya Sani Ba

            A waɗannan kwanaki da zamani, a lokacin da maganar “gaskiya” ke fuskantar ƙiyayya, bai kamata ya ba mu mamaki ba cewa duniya ba ta a shirye ta karɓi “Ruhu na gaskiya”—Ruhu Mai Tsarki. Me yasa haka? Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai biyu.

            Na farko, tun daga ranar farkon da maza da mata suka bijire wa Allah cikin tawaye, ba su yarda su karɓi gaskiya ba. Me ya sa? Domin gaskiya na fallasa ayyukansu na rashin adalci. Saboda haka, kamar yadda Romawa 1:18 ta ce, sun ƙudurta su “danne gaskiya cikin aikin muguntarsu.”

            Na biyu, tawaye ga Allah ya kai ’yan Adam ƙarƙashin mallakar allahn wannan zamani: “Shaiɗan, mai ruɗin dukan duniya” (Wahayin Yahaya 12:9). Yaudara ita ce makami na farko da Shaidan ke amfani da shi don rike ’yan Adam a ƙarƙashin ikonsa. Me ya sa maƙiyi ya jajirce a kan ƙoƙarinsa na yaudarar mu? Ya san cewa da zarar an kawar da yaudararsa, duniya za ta ga gaskiyar—cewa Shaiɗan ba shi da wani abu da zai iya ba kowa sai dai kasancewa tare da shi a cikin tafkin wuta na har abada!

            Mecece Gaskiya?

            Karni da yawa, falsafar ’yan Adam ta yi ƙoƙari ta samar da ma’anar “gaskiya” mai gamsarwa. Duniyarmu na yin irin wannan tambayar irin ta Buntus Bilatus sa’ad da ya sadu da Yesu fiye da shekaru dubu biyu da suka wuce: “Mecece gaskiya?” (Yahaya 18:38).

            Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa ta fannoni uku ga tambayar Bilatus. Da farko, Yesu ya ce, “Ni ne gaskiya” (Yahaya 14:6). Na biyu, cikin addu’a ga Allah Uba, ya ce, “Maganarka gaskiya ce” (Yahaya 17:17). Na uku, Yahaya ya gaya mana, “Ruhu [Mai-Tsarki] gaskiya ne.” (1 Yahaya 5:6).

            Saboda haka, a duniyar ruhaniya, akwai shaidun gaskiya guda uku: Yesu; Littafi Mai Tsarki; da Ruhu Mai Tsarki. Yayin da waɗannan ɓangarori suka jeru, za mu sami gaskiyar—cikakkiyar gaskiya. Yana da muhimmanci a dubi dukan waɗannan ɓangarori kafin akai ƙarshen maganar. Dangane da wannan, akwai tambayoyi guda uku da ya kamata mu yi game da kowane al'amari na ruhaniya:

            1. Ko yana wakiltar Yesu da gaske kamar yadda yake?
            2. Yana da muwafaka da Littafi Mai Tsarki?
            3. Ko Ruhu Mai Tsarki yana ba da shaidar Sa?

            A tarihi, da Ikkilisiya ta magance kurakurai da yaudara da yawa idan da ta ci gaba da jaddada waɗannan gaskiyar a cikin gabatar da koyarwa da wahayi. Kafin mu yarda da abin da aka gabatar mana a matsayin gaskiya, dole ne dukan ɓangarorin uku su kasance tare: Yesu, Littafi Mai Tsarki, da Ruhu Mai Tsarki.

            Ba Da Shaida

            Ta yaya Ruhu Mai Tsarki yake aiki a matsayin ɗaya daga cikin manyan bangarorin da ke cikin wannan hanyar sanin gaskiya? Babban aikin Ruhu Mai Tsarki shi ne ba da shaida, kamar yadda aka faɗa a cikin 1 Yahaya 5:6: “Ruhu ne ke shaida.”

            Ruhu yana ba da shaidar Yesu a matsayin Ɗan Allah Madawwami, wanda ya zubar da jininsa a kan gicciye a matsayin wadatacciyar haɗaya ta dukan zunubanmu. A cikin kalmomin waƙar Charles Wesley, “Tashi ya Raina, Tashi”: Ruhu ya yi na’am da jinin da Yesu ya zubar, ya kuma fada mani ni haifaffe ne na Allah.

            Ruhu Mai Tsarki kuma yana bada shaidar gaskiya da ikon Littafi Mai Tsarki, kamar yadda Bulus ya rubuta wa mutanen Tassalonika:

            “domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matukar tabbatarwa.” (1 Tassalunikawa 1:5)

            Hananiya da Safiratu

            Kamar yadda muka gani a Yahaya 14, Yesu ya kira Ruhu Mai Tsarki “Ruhu na gaskiya.” Ya zama cewa babu canjin ra’ayi tsakanin Ruhu Mai Tsarki, wanda shi ne Ruhu na gaskiya, da Shaiɗan, “don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma” (Yahaya 8:44). An nuna wannan sosai a cikin Ikkilisiya ta farko—lokacin da Hananiya da Safiratu suka yi ƙarya game da kuɗin da suka ba Ikkilisiya. Sun yi iƙirarin cewa abin da suka bayar shi ne dukan kudin da suka sayar da ƙaddarar. A gaskiya, sun ajiye wani sashi na waɗannan kudaden don kansu.

            A bayyane yake, ba a ruɗi Ruhun gaskiya da ke cikin Bitrus ba. Ya tuhumi Hananiya da yin ƙarya—ba ga mutane kawai ba, amma ga Ruhun gaskiya Kansa:

            “Sai Bitrus ya ce, ‘kai Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar? Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar, kuma kuɗin ba halalinka ba ne? To, ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa. Da jin wannan magana Hananiya ya faɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su.” (Ayyukan Manzanni 5:3-5)

            Bayan sa’oi uku, Safiratu ta shigo ta sake maimaita wannan ƙaryar. Kamar mijinta, ta biya wannan ƙaryar da ranta.

            Idan aka yi tambaya cewa menene laifinsu, ya yiwu ka ce ƙarya ce. Haƙiƙa, zunubin da Hananiya da Safiratu suka yi shine laifin riya—yin ƙarya da addini. Suna nuna kamar sun fi kowa yin bayarwa da miƙa kai ga Ubangiji fiye da yadda suke.

            Yesu na da kalmomin masu ƙarfi na hukunci a kan wannan zunubi sa’ad da ya gan shi a cikin shugabannin addini na zamaninsa. Sau bakwai a cikin Matta sura 23 ya ce wa Farisawa: “Kaitonku... munafukai!”

            Menene Munafunci?

            Kalmomin Turanci “ hypocrite (wato, munafuki)” da “hypocrisy (wato, munafunci)” sun samo asali ne daga kalmar Helenanci hupokrite, ma’ana “mai wasan kwaikwayo.” Dalilin wannan munafuncin ko riya shine: yin aikin addini na ƙarya. Wataƙila babu wani zunubi da ya zama ruwan dare a tsakanin masu addinin baka kamar yin munafunci ko riya. (Haƙiƙa, waɗansu ayyukan addini sukan buƙaci a yi hakan.)

            Ko ka taɓa lura da yadda halaye da dabi’un wasu ke canjawa idan suka sadu da masu addinin baka? Ba za su kasance ainihin yadda suke ba, a sake, da sakin zuciya. Suna a takure kamar an matsa su dole su zama kamar waɗannan masu addinin bakan. Irin wannan addinin bakan na iya canza fuska, yau dabam gobe dabam. Amma kaɗan daga cikinsu ne ke barin mutane su kasance yadda suke a zahiri.

            Misalin Ayuba

            Allah na Littafi Mai Tsarki ba ya jurewa da munafukai ko masu riya. Wannan ya fito fili a cikin labarin Ayuba. Abokan Ayuba uku sun ba da bayanai irin na masu addinin baka. Sun ce, a zahiri, “A kullum Allah na sa wa adalai albarka; ba sa shan wahala haka kawai.’’ Su ka ce kuma, "A kullum Allah na yi wa miyagu shari'a; ba sa taɓa yin albarka." Amma duk da haka akwai hujjoji a tarihi da ke nuna cewa wannan ba gaskiya ba ne. Maganar addinin baka ne kawai!

            A ɗaya gefen kuma, Ayuba ya faɗi ainihin abinda ke zuciyar sa. Ya ce, “Allah bai yi mani daidai ba. Ban yi wani abin da ya cancanci dukan wannan ba. Amma ko da ya kashe ni, zan dogara gare shi.”

            A cikin Ayuba 42:7 , Ubangiji ya bayyana irin halin Ayuba da abokansa.

            “Ubangiji ya ce wa Elifaz mutumin Teman, ‘Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.’

            Muna buƙatar mu tambayi kanmu: Ta yaya halin munafunci da riya na addinin baka a tsakaninmu ya bambanta da zunubin Hananiya da Safiratu, wanda ya kai su ga mutuwa?

            Lokacin Fuskantar Gaskiya

            A wani lokaci cikin aikinsa, Sarki Dauda ya yi munanan zunubai guda biyu. Da farko, ya yi zina da Bathsheba, matar maƙwabcinsa Uriya. Sa'an nan don ya ɓoye zunubinsa, ya shirya yadda aka kashe Uriya.

            Da fako dai, kamar Dauda ya yi nasara wajen boye dukan waɗannan—har sai da annabin Allah, annabi Natan, ya tunkare shi da zunubinsa. A wannan lokacin, akwai alamar tambaya ga makomar Dauda ta har abada. Ta wurin alherin Allah, Dauda ya yi abinda ya dace. Bai bayar da wasu hujjoji ba, kuma bai yi wani ƙoƙarin ɓoyewa ba. Ya yarda kawai, “Na yi zunubi” (2 Sama’ila 12:13).

            Daga baya, a cikin Zabura ta 51, Dauda ya yi addu’ar furtawa ya kuma yi kukan neman jinƙai. Aya ta 5 da 6 kowace ta fara da kalmar, “Gashi,” wanda nan da nan ke bayyana muhimmiyar gaskiya.

            Aya ta 5 ta ce, “Gashi, cikin mugunta aka siffanta ni, cikin zunubi kuma uwata ta ɗauki ciki na.” Dauda ya fuskanci wani abu wanda Ruhun gaskiya ne kaɗai zai iya bayyanawa. Ba zunubin da ya aikata ba ne kawai, har ma da mugun ikon zunubin da ya gada wanda ke cikin kowane tsatson Adamu.

            Aya ta 6 ta bayyana dalilin da ya sa Allah ya ‘yantar da kai daga ikon zunubi da ke cikin ka: “ Gashi, amintacciyar zuciya kake so.” Ko bayan zunubin da ya yi, Dauda ya ci gaba da nuna halaye na zahiri da suka dace da matsayinsa na sarki. Amma yanzu akwai tazara mai yawa tsakanin halinsa na zahiri da yanayin zuciyarsa. Ya zama mai riya—mai wasan kwaikwayo wanda ke aikata wani abu dabam da abinda ke cikin zuciyar sa. Magani ɗaya ne kacal domin irin wannan riyar: furtawa ta gaskiya da tuba da zuciya ɗaya. Idan akwai riya a cikin mu, to, wannan shine magani iri ɗaya domina da kai.

            Abinda Ke Hana Farkawa

            Krista da yawa a yau suna magana da yin addu’a game da “farkawa.” Amma sau da yawa suna yin watsi da gaskiyar cewa akwai abu ɗaya da ke hana farkawa da ba za a iya kauce masa ba. Menene wannan abun? Zunubi ne. Har in ba a yi maganin zunubi ba, to, farkawa ta gaskiya ba za ta taɓa samuwa ba. Kuma akwai hanya ɗaya tak da za a magance zunubi: “Wanda ya rufe laifofin sa, ba za ya yi albarka ba: amma dukan wanda ya faɗe su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai” (Misalai 28:13).

            A zahiri, yawancin ɗariku na Ikkilisiyun zamani suna cike da “ɓoyayyen zunubi.” Ga wasu zunubai da Krista ke rufewa:

            1. Cin zarafin yara - a jiki, a zuciya, yin fyaɗe - ko duka.
            2. Karya alkawuran aure.
            3. Harkar kuɗi da ba ta dace ba.
            4. Kallon hotunan batsa. (Zai ba ka mamaki idan ka ga yadda wannan ya zama ruwan dare a cikin shugabannin Ikkilisiya.)
            5. Zari da wuce gona da iri na sha'awar jiki.

            Mafita ta Allah — haɗe da Ruhun gaskiya — na da abu biyu: na farko, ka furta; sa’an nan, ka bari. Ba safai ya ke da sauki mu furta zunuban mu ba. Amma babu wani magani. “Idan muka furta zunuban mu, shi mai alkawari ne, mai-adalci kuma, da za shi gafarta mana zunubanmu, shi tsarkake mu daga dukan rashin adalci.” (1 Yohana 1:9). Allah bai taba sa kansa ya gafarta zunuban da ba mu yarda mu furta su ba.

            Amma furtawa kawai ba ta isa ba. Dole ne mu “rabu” da su. Dole ne mu ƙudurta cewa ba za mu ci gaba da yin zunubin da muka furta ba. Dole ne mu bi shawarar kai tsaye da Daniyel ya ba Sarki Nebukadnezzar: “Ka daina zunubinka, ka yi adalci.” (Daniyel 4:27).

            Kai Kuma Fa?

            Idan wannan wasiƙar ta tono wasu ɓangarori na zunubi ko rashin biyayya a rayuwarka, wannan lokaci ne mai kyau da za ka buɗe wa Ruhu na gaskiya zuciyar ka! A shirye yake kuma da ya yarda zai taimake ka. Bari mu nemi wannan taimakon yanzu.

            *Prayer Response

            Ya Uba na Sama, na buɗe zuciyata yanzu ga Ruhu Mai Tsarki—Ruhun gaskiya. Na riga na san akwai wuraren da na ke zunubi da rashin biyayya a cikina. Ina furta su gare ka, na yi alƙawarin rabuwa da su yayin da nake ci gaba cikin alherinka. Na gode da ka ba mu ikon Ruhunka. Bari Ruhun gaskiya ya yi aiki a cikina tun daga yau zuwa nan gaba a kowane fanni na rayuwata da hidimata. Amin.

            Nayi Sallah
            11
            Raba
            Expand Content

            What People Say

            See how Ruhun Gaskiya has impacted lives across the globe.

            "I've applied the Biblical principles on family relationships from this teaching, and it has completely restored harmony in our home. My teenagers and I now have meaningful conversations about faith, and my marriage has been strengthened in ways I never thought possible."
            Elena R., Brazil
            "The teachings on spiritual warfare completely transformed my approach to daily challenges. I used to feel overwhelmed by life's obstacles, but now I understand how to stand firm in faith. This teaching gave me practical tools I use every single day."
            Sarah K., California
            "After 20 years of struggling with unforgiveness, the Biblical principles shared in this teaching helped me release the bitterness I had been carrying. The step-by-step approach to forgiveness wasn't just theory—it actually worked in my life when nothing else had."
            Michael T., United Kingdom
            "As a new Christian, I was confused about many aspects of faith. These teachings provided clear, Scripture-based explanations that helped build my foundation. I'm especially grateful for how the content made complex concepts accessible without watering down the truth."
            Priya M., India
            "The teaching on God's sovereignty during difficult times came to me exactly when I needed it most. After losing my job and facing health challenges, this message reminded me that God remains in control. It gave me hope when I had none left."
            James L., Australia
            "I've applied the Biblical principles on family relationships from this teaching, and it has completely restored harmony in our home. My teenagers and I now have meaningful conversations about faith, and my marriage has been strengthened in ways I never thought possible."
            Elena R., Brazil
            "The teachings on spiritual warfare completely transformed my approach to daily challenges. I used to feel overwhelmed by life's obstacles, but now I understand how to stand firm in faith. This teaching gave me practical tools I use every single day."
            Sarah K., California
            Ad Image

            *Free download

            *This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.

            Zazzage PDF

            Lambar: TL-L128-100-HAU

            Kyauta
            Ba da
            Gabatar da martani