Bawa Mara son Kai

Teaching Legacy Letter
*First Published: 2019
*Last Updated: December 2025
10 min read
A cikin binciken mu ya zuwa yanzu, gaskiya ɗaya ta bayyana a sarari: akwai wani abin al’ajibi mai zurfi game da Ruhu Mai Tsarki. Duk da haka, ya zaɓi ya bayyana kansa sosai ta wurin Littafi Mai Tsarki. Wannan shi ne mafarin dukan dangantakar mu da Ruhu Mai Tsarki. Me Littafi Mai Tsarki ya faɗa mana game da shi?
Har ya zuwa yanzu, a cikin wannan jerin, Wanene Ruhu Mai Tsarki, mun koyi cewa shi ne mutum na uku na Murhunniya, inda “ɗayantaka” da “jam’i” suka yi haɗuwa ta ban mamaki. Ko da yake shi ne mutum na uku na Allahntaka, Shi ne na farko da aka fara magana a kansa a cikin Littafi Mai Tsarki:
“Ruhun Allah kuwa yana shawagi bisa ruwaye” (Farawa 1:2)
Littafi Mai Tsarki kuma ya bayyana cewa shi Madawwami ne, ya wanzu tun daga zamani zuwa zamani; Masanin abu duka, Ya san komai; kuma Yana ko'ina, Mai kasancewa a ko’ina a kowane lokaci. Waɗannan halayen, waɗanda ke iza wani yanayi na al’ajabi mai zurfi a cikin mu, suna kuma iya samar da marmarin sanin Sa da kyau.
Na gaskata, duk da haka, cewa ainihin bayyanawar Ruhu Mai Tsarki na ƙunshe cikin sunan Sa: Mai Tsarki ne. Wannan shi ne mizanin da zamu auna kowane wa’azi, dukan bayyanuwar Ruhu, da kowace ƙungiya da ke ikirarin cewa ta Ruhu Mai Tsarki ce: Ko ya yi daidai da Tsarkin Sa?
Daga "Pentecostal" zuwa "Charismatic"
Sananniyar magana ce cewa “Ido yakan raina wanda ya saba gani”. Abin takaici, ana iya amfani da wannan karin maganar a kan al’amuran Ruhu. Kusan ma, irin wannan sabawar ta faru a wani lokacin ci gaban ƙungiyar Petecostal.
Babu irin wannan a lokacin da baftisma da baye-bayen Ruhu Mai Tsarki suka fara yin tasiri cikin Ikkilisiya a shekarun farko na ƙarni na 20. A wancan lokacin, ba wanda ke so ayi masa wani laƙabi da “Pentecostal.” Akwai wani abin ƙyama da ke tattare da wannan lakabin, sakamakon haka, babu mutuntawa ga waɗannan muhimman mafarin tarihi na motsawar aikin Ruhu Mai Tsarki.
A wani mataki, wannan ƙyamatar ta kasance batun “ƙungiya”. ‘Yan Pentecostal na farko, mafi yawa, ba su da ilimi sosai, kuma da yawa sun fito ne “daga ɓangare na dabam.” Wasu daga cikin abubuwan da suka yi, suka kuma faɗa sun zama kamar wauta ne, kuma suna da tsattsauran ra'ayi game da tsarki.
Bayan wani lokaci, yawancin waɗannan ra'ayoyi marasa kyau sun canja - musamman lokacin kafawar Ƙungiyar Charismatic . Sauyawar kalmar “Pentecostal” zuwa “Charismatic” ta kawo ɗan mutuntawa, wanda ya sa ya zama da ban sha’awar zama “Charismatic.” Hakika, kalmar ba ta zama ta Krista kaɗai ba. (Na tuna mamakin da na yi a karon farko da na ji kafar yaɗa labarai sun yi amfani da kalmar ga wani dan siyasa mara mutunci!)
Canji zuwa mutuntawa na da ɓangarori biyu mai kyau da marar kyau. A ɓangare mai kyau, baftisma da baye-bayen Ruhu Mai Tsarki sun zama samammu ga jikin Kristi. Amma a bangare marar kyau, an ɓullo da wasu ƙungiyoyi da ayyuka waɗanda ba za a iya morar kalmar “tsarki” a kan su ba. Ga wasu 'yan misalai kaɗan:
- Kalamai na rashin ɗa’a da ake mora a kan abubuwa masu tsarki na Allah.
- Kungiyoyin da aka kafa ta wurin kwaɗayi a fili, da kuma ƙarfafa ikirarin da ba na gaskiya ba da alkawuran da ba a cikawa.
- Bayanai marasa dacewa da ake jingina su da Ruhu Mai Tsarki.
Cewa ana ci gaba da samun waɗannan batutuwa a cikin kungiyoyin da suke ikirarin su Krista ne ba ya ba ni mamaki ba. Da ma, kwaɗayi da son kai suna cikin halin ɗan adam. Abin da ya ba ni mamaki duk da haka, shi ne miliyoyin masu kiran kansu Krista sun yarda da irin wadannan ɗabi'u a matsayin abin da ke jituwa da tsarkin Allah. Bisa ga irin waɗannan halaye marasa dacewa, ya wajaba mu sake sabon nazari akan Ruhu Mai Tsarki. Wanene shi?
Bawa Mai Tawali'u, Mai Hidimtawa
Zama bawa wani sashi ne na halin Allahntaka. Har yanzu ina iya tuna abin da ya girgiza ni sa’ad da na fara fahimtar wannan gaskiyar. Yawancin mutane a yau na ɗaukar zama bawa a matsayin abin gujewa—wani abin ƙasƙanci. Wannan hali ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da ke lalata al'adunmu na wannan zamani. Bugu da ƙari, ƙarya ne. Zama Mai Hidimtawa bai samo asali a yanzu ba, amma tun fil’azal; ba a duniya aka fara shi ba, amma a sama. Tun fil’azal, Yesu Ɗa ne mai farin cikin miƙa kai, da bawa mai yin biyayya ga Allah Uba. Ruhu Mai Tsarki kuma, shi ne mai yin biyayya, bawa mai hidimtawa ga Uban da Ɗan. Ba ya yin ƙorafin “danniya” ko neman “‘yancinsa.” ba. Ya na cika aikin da aka ba shi daidai. Bawan Allah ne Shi!
An kwatanta wannan gaskiyar da kyau a cikin sura ta 24 ta Farawa, wanda ya bayyana yadda Ibrahim ya umurci bawansa ya nemo wa ɗansa Ishaku mata. Akwai abubuwa na musamman “iri” huɗu a cikin wannan bayanin. Ibrahim misali ne na Allah Uba; Ishaku misali ne na Allah Ɗa, Yesu; Rifkatu misali ce ta amaryar Kristi, wato, Ikkilisiya.
To bawan Ibrahim kuma fa? Ko da yake ba a ba shi wani suna ba, a zahiri shi ne babban jigo a cikin wannan labarin! Shi ne “misalin” Ruhu Mai Tsarki. A matsayinsa na bawa, yana da babbar manufa ɗaya: ya nemo budurwar da za ta zama amarya. Da ya samo ta, aikinsa shi ne ya shirya ta ya kuma ƙawata ta; ya kuma raka ta zuwa wajen ango.
Saboda irin wannan manufa ce Ruhu Mai Tsarki ya sauko duniya a ranar Fentikos. Ya zo da babbar manufa guda ɗaya: ya nemo, ya shirya, ya ƙawata amaryar Kristi, wato, Ikkilisiya. Shi ne wanda zai raka ta lafiya cikin wannan duniyar ya kuma miƙa ta ga Yesu—tsatstsarka, marar aibi.
Daya daga cikin ainihin halin Ruhu Mai Tsarki, kamar bawan Ibrahim, shi ne bai taba jan hankali ga kansa ba. Ga fassarorin zahiri na wasu bayanai da Yesu ya yi game da shi:
- “Zai shaida ni...” (Yohanna 15:26);
- “Ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada...” (Yohanna 16:13);
- “...Zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa, ya sanar da ku.” (Yohanna 16:14).
Abin lura har yanzu, a cikin dukan bayyanin da aka yi mana a cikin Littafi Mai Tsarki, babu wani rahoton da ya nuna cewa akwai wanda ya taɓa yin addu'a ga Ruhu Mai Tsarki. Misalin addu’ar da Yesu ya ba almajiransa ta fara da waɗannan kalmomi: “Uban mu.” A kan wannan, Yesu ya ƙara da alkawarin sa: “Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan” (Yohanna 14:13). Dukan addu'ar da ke bisa ga Littafi Mai Tsarki ana yin ta ne zuwa ga Allah Uba. Aikin Ruhu Mai Tsarki shi ne ya taimake mu mu kai ga Uban ta wurin addu’o’in mu —ba wai ya ba mu wani wuri na dabam ba. Za mu yi addu’a cikin Ruhu, ba ga Ruhu ba (dubi Afisawa 6:18).
Abin Yin La’akari
Duk da haka, a cikin 'yan shekarun nan, wasu bangarori na Ikkilisiya sun kauce daga wannan tsari na Littafi Mai Tsarki. An mai da hankali ga Ruhu Mai Tsarki maimakon Uban da Ɗan. Wasu waƙoƙi da yawa—waɗanda ba su da kalmomin Littafi Mai Tsarki sosai— ana raira su kai tsaye ga Ruhu Mai Tsarki. Sau da yawa a kan fi mayar da hankali a kan abubuwan da suka shafi rayuwar mawaƙin da kuma fifita shi. Wannan kaucewar da wayo na kai mutanen Allah ga haɗari na ruhaniya wanda zai yi wahala a rarrabe.
Muna buƙatar mu rike ainihin ƙa'idodi biyu a zuciyar mu. Na farko, Ruhu Mai Tsarki ba ya taɓa cika muradin ɗan adam. Na biyu, Ruhu Mai Tsarki ba ya taɓa jan hankali ga kansa. A kullum yana mai da hankalin mu ga Yesu.
A duk lokacin da aka yi watsi da waɗannan ƙa’idodin, sakamakon zai iya zama ɗokin jiki da kuma sha’awar zuciya, ba tare da wani tsarki na gaske ba. Wannan zai iya kai mu ƙarƙashin ruɗin shaidan na riya da ayyukan sa. Kamar Ruhu Mai Tsarki, dole ne a koyaushe mu mai da hankalin mu a kan Yesu.
Wuta Mai Cinyewa
Ɗaya daga cikin hanyoyin da Ruhu Mai Tsarki ke bayyana kansa a wasu lokuta shi ne ta wuta. A gaskiya, lokacin ƙarshe da Ruhu Mai Tsarki ya bayyana a fili a cikin Littafi Mai Tsarki a matsayin “fitilu bakwai na wuta... suna ci a gaban kursiyin Allah” (Ruya Ta Yohanna 4:5).
Marubucin Ibraniyawa ya yi magana mai sauƙi, amma mai zurfi:
“Gama Allahnmu wuta ne mai cinyewa” (Ibraniyawa 12:29)
Bai ce Allah kamar wuta ba ne, amma Allah wuta ne. Don haka, “Ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa” (Ibraniyawa 12:28). Ba tsoro na bauta ba, amma “Tsoron Ubangiji, mai-tsarki ne, madawwama ne.” (Zabura 19:9).
Marubucin Ibraniyawa ba magana ya ke a kan Allah Uba, ko kuma Allah Ɗa ba, amma Allah Ruhu Mai Tsarki. Haƙiƙa shi wuta ne—wuta mai cinyewa.
A wurare dabam dabam a tarihin Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki ya sauko cikin mutane a matsayin wuta. Ɗaya daga cikin waɗannan lokatai shi ne a alfarwa a cikin jeji, lokacin da Haruna ya miƙa dukan hadayun da aka ayyana:
“Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta kone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden, da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rub da ciki suka yi sujada.” (Littafin Firisitoci 9:23-24)
Lokacin da wutar ta sauko mutanen suka fāɗi rub da ciki, ba bayyanar ruhun kawai ne ya motsa su ba. Sun yi haka ne saboda kasancewar Allah—Allah Ruhu Mai Tsarki—wanda ya sauko a cikin su a matsayin wuta mai cinyewa. Ba su ma iya miƙewa tsaye a gaban Sa ba.
Domin Tsarkakewa ko Hallakarwa?
Duk da haka, akwai ɗabi’u biyu na wuta masu saɓani. Wuta na iya zama da amfani, amma kuma da haɗari. Wuta na iya tsarkakewa, tana kuma iya hallakarwa. Haka kuma wutar Ruhu Mai Tsarki take. Yana iya sa albarkar Allah da tagomashin sa ga masu biyayya. Amma kuma zai iya sauko da fushin Allah da hukunci a kan masu girman kai da dogara da kansu.
Nan da nan bayan wutar ta sauko a kan hadayar Haruna a cikin alfarwa, bayanin ya ci gaba:
“'Ya'yan Haruna maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umurta ba, sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su. suka mutu a gaban Ubangiji” (Littafin Firistoci 10:1-2) .
Wannan babban darasi ne! Wutar nan da ta kawo albarkar Allah a kan hadayar Haruna ta kawo mutuwar ’ya’yansa biyu nan take sa’ad da suka shiga gaban Allah da “haramtaciyar wuta (marar-tsarki) .”
Allah ya riga ya bayyana hanyar da za mu kusance shi: “tare da girmamawa da tsoro,” (Ibraniyawa 12:28) “... mu duka [Yahudawa da Al’ummai] muna samun dama ta wurin Ruhu ɗaya [Ruhu Mai-Tsarki] zuwa ga Uban” (Afisawa 2:18).
Miƙa “haramtacciyar wuta” ita ce kusantar Allah da riya da isa. Shi ne zuwa gare shi a cikin ruhun da ba Ruhu Mai Tsarki ba. Don haka al'amari ne mai muhimmanci— a gaskiya, na rai da mutuwa—a fahimci Ruhu Mai Tsarki kamar yadda yake bayyana kansa, da kuma bambanta shi da kowane ruhu na karya.
Muhimman Abubuwa Biyu Da Ake Buƙata
A cikin dukan Isra’ilawa, Nadab da Abihu (’ya’yan Haruna) sun ɗauka cewa suna da gata na musamman na shiga gaban Allah ta hanyar da suka zaɓa. Bisa ga matsayin ɗan fari, ya kamata Nadab ya gaji Haruna a matsayin Babban Firist. Amma babu abin musaya biyayya ga Kalmar Allah—ko matsayi na ɗarika, ko mu’ujizai na ban mamaki, ko taron jama’a. Allah ba shi da masana ma su gata waɗanda za su yi watsi da cancantar da ya ke buƙata ba tare da karɓar sakamakon ba.
Hukuncin Allah a kan ɗaukaka kai na Nadab da Abihu tuni ne mai ƙarfi a gare mu mu guji sabawar da aka yi gargaɗin ta a baya. Yana tuna mana cewa Ruhu Mai Tsarki yana ba da albarkarsa ne ga bayi marasa son kai kamar Sa, waɗanda suka cancanta. Ƙa’idarsa ta farko ita ce mai da hankali ga ɗaukaka Ubangiji Yesu Kristi. Ƙa’ida ta biyu da ake buƙata ita ce bin jagoranci da kuma halayen da Ruhu da kansa ya koya mana a cikin Littafi Mai Tsarki
A ƙarshe, bari mu nemi taimakon Ubangiji yanzu don mu cika waɗannan muhimman ƙa’idoji biyu: mu ɗaukaka Ubangiji Yesu, da kuma yin biyayya da Ruhu Mai Tsarki.
*Prayer Response
Ya Uba na Sama, ina kewaye cikin al’adu irin na ruhun Nadab da Abihu - na girman kai da neman suna - kuma ba na son su shiga cikin rayuwata. Idan ka yarda, Ubangiji, ka sa mizani na tsarki a cikina ta wurin tsarkakewar wutar Ruhu Mai Tsarki. Ka koya mani yin tafiya cikin tawali'u a gabanka. Ka ba ni hikima da rarrabewa—ka taimake ni in tsaya da ƙarfi domin yin tsayayya da abokin gaba. Na bada kaina ga Ruhunka Mai Tsarki domin in yi maka hidima da kyau, in sadu da kai ta sabbin karfafan hanyoyi. Na roƙi dukan wannan cikin sunan Yesu. Amin.

*Free download
*This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.
Zazzage PDFLambar: TL-L127-100-HAU