Ruhu Mai Tsarki Madawwami, Masanin komai, Yana Ko’ina

Teaching Legacy Letter
*First Published: 2019
*Last Updated: December 2025
10 min read
A matsayin mu na Krista, mun fahimci cewa ƙaunar Allah ita ce ginshiƙin dukan rayuwar ruhaniya. Za mu iya sanin Allah da ƙaunar Sa a matsayin Ubanmu, da Yesu, Ɗansa, a matsayin babban yayan mu—mutane biyu na farko cikin Allahntaka. Amma idan aka zo batun sani da ƙaunar Ruhu Mai Tsarki, ta yaya za mu yi dangantaka da wannan mutum na uku mai ban al’ajibi na Murhunniya?
Kamar yadda na fada a wasikata ta baya, manufar wannan jerin Wasikun Koyarwar, Wanene Ruhu Mai Tsarki, ita ce domin a taimake ka ka fahimci Wanene Ruhu Mai Tsarki. Fatana shi ne, yayin da muke binciken Littafi Mai Tsarki tare, za ka ƙaru da sani, da mamaki, da kuma ƙaunar Sa. A wannan bugu na biyu na jerinmu, za mu dubi wasu siffofi uku masu matuƙar muhimmanci da ake mora a kan Ruhu Mai Tsarki: madawwami, masanin komai, kuma yana ko’ina.
Madawwami
Dangantaka ta da Ruhu Mai Tsarki ta fara shekaru da dama da suka wuce, tun a kwanakin farko da na fara bincike game da addinin Krista. A ƙarshen ɗaya daga cikin sujada ta farko da na halarta na masu magana da harsuna, mai wa’azin ya tambaye ni, “Ka gaskata cewa kai mai zunubi ne?” A wancan lokacin, ni ƙwararren masani ne a fannin falsafa kuma na gama rubuta bincike na a kan “ma’anar abubuwa” a Jami’ar Cambridge. Nan da nan, a cikin zuciya ta na tuna dukan ma’anonin da za a iya bayarwa na “mai zunubi.” Dukansu sun yi daidai da ni! Saboda haka na amsa, “I, na gaskata ni mai zunubi ne!”
Sai Mai wa’azin ya tambaye ni, “Ka gaskanta cewa Almasihu ya mutu saboda zunuban ka?” Da na yi tunani a kai, sai na amsa, “ In fada maka gaskiya, ban ga abin da mutuwar Yesu Almasihu shekaru fiye da dubu biyu da suka wuce za ta yi a kan zunuban da na aikata a rayuwata ba.”
Mai wa’azin ya nuna hikima sosai, bai shiga muhawara da ni ba, amma na tabbata ya yi mani addu’a. Bayan wasu ‘yan kwanaki, na sami wata saduwa da Yesu Almasihu sosai wadda ta sauya tafarkin rayuwata gaba ɗaya. Littafi Mai Tsarki ya zama littafi mai rai, mai ma’ana na musamman a gare ni.
Bayan wani lokaci, yayin da nake karanta sura ta 9 ta Littafin Ibraniyawa, na ci karo da wannan sashin magana a aya ta 14: “Almasihu, wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah ta wurin Madawwamin Ruhu.” Nan da nan na fahimci muhimmancin kalmar nan “madawwami.” Ma’anar wannan kalma a sauƙaƙe tana nufin wani abu da ya wuce gaban tsawon lokaci. “Madawwami” na nufin wanzuwar da ta fi gaban iyakar lokaci—wani abu ne da ke haɗa baya, yanzu, da kuma gaba a lokaci guda.
Ka gani, lokacin da Yesu ya miƙa kansa a kan giciye, haɗayarsa ba ta tsaya ga lokacin da ya mutu kaɗai ba. Ta wurin Madawwamin Ruhun, hadayar nan ta magance zunuban dukan mutane na kowane zamani—na da, na yanzu, da na gaba. Na fahimci cewa hadayar sa ta haɗa da zunuban da na aikata fiye da ƙarni ashirin bayan mutuwar sa.
Daga Zamani Zuwa Zamani
A fili yake, kalmar Helenanci ta “madawwami” na da ma’ana mai fadi sosai. An samo ta daga sunan aion, wanda daga gare shi muka sami kalmar Turanci “aeon.” Aion na nufin wani ma’aunin lokaci, kuma yana bayyana a cikin nau’o’in furuci dabam dabam, kamar yadda muka gani a cikin waɗannan fassarori na Littafi Mai Tsarki:
Ibraniyawa 7:24: “Amma shi da yake - zamani zuwa zamani ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani”(YLT). Wannan yana nufin tsawon wannan zamani na yanzu. A fassarar King James wannan ayar na cewa, “ya dawwama har abada.”
Yahuda 25: “Tun fil’azal, da yanzu, da kuma har abada abadin” Fassarar King James ita ce “yanzu da kuma har abada abadin.”
Galatiyawa 1:5: “ɗaukaka ta tabbata a gare Shi har abada abadin.” A fili yake a gare ni cewa wasu daga cikin fassarorin Turanci ba su ma fara bayyana zurfin ma’anar da ke cikin kalmomin Helenanci ba. Irin waɗannan maganganu—da makamantansu—suna cika zuciyata da ban mamaki. Suna kama da ɗan digon ruwa da ke diga a saman wani rami mai zurfi wanda ya raba duwatsu biyu masu tsayi da ba zan iya hawa ba. Hankalina ba zai iya fahimta gaba ɗaya cewa akwai wani zamani da ya kunshi zamanai, balle har a ce akwai zamanai da ke ƙunshe da irin waɗannan zamanai ba. Amma Ruhu Mai Tsarki madawwami ya kunshi dukansu, a miƙe daga farko marar iyaka har zuwa gaba marar iyaka. Na fara sake samun sabuwar fahimtar sunan da ake bauta wa Allah da shi a sama da ba shi da iyaka: Abin da ke na kurkusa da ɗabi’ar kasancewar har abada ta Ruhu Mai Tsarki shi ne saninsa na komai. A cikin Littafin 1 Yohanna, Manzon ya bayyana mana wani wahayi mai zurfi amma mai sauƙi: Allah ya san dukan komai. Babu wani abinda Allah bai sani ba. Daga ɗan ƙwaro mafi ƙanƙanta a cikin ƙasa har zuwa tauraro mafi nisa a sararin samaniya, babu wani abinda Allah bai san shi gaba daya ba. Allah ya san abubuwa game da mu waɗanda mu kanmu ba mu sani ba. Misali, Ya san yawan gashin da ke kan kowanen mu. “Ai ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye suke” (Matta 10:30). Allah ya san yawan mazaunan birnin Nineveh, “ babban birnin Nineveh wanda mutanen da ke cikin ta sun fi zambar dubu ɗari da ashirin” (Yunana 4:11). Ya sani—kuma yana sarrafa—girman itacen da ya ba Yunana inuwa. Haka kuma, ya sani—kuma yana sarrafa—aikin tsutsar da ta sa zurman ta yi yaushi. A cikin 1 Korinthiyawa 2:9–10, Bulus yana magana game da abubuwan da “ abinda ido ba ya gani ba, kunne ba ya ji ba, ba ya shiga zuciyar mutum ba.” Sai ya ci gaba da cewa, “amma mu ne Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu ya na binciken abu duka, i, har zurfafa na Allah.” Ba kawai Ruhu Mai Tsarki na binciko zurfafa ba; yana kuma hawa ƙololuwa fiye da dukan komai, na yanzu, da kuma mai zuwa. Sanin Sa ba shi da iyaka kuma ba ya ƙarewa. Saboda haka, ya san zurfin zuciyar mu sosai, kuma yana so mu san Shi! Bisa ga wannan sani marar iyaka ne ya kamata ni da kai mu kasance a shirye gama za mu ba da lissafin kanmu ga Allah. “Ba wata halitta da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi gabansa” (Ibraniyawa 4:13). Sa’ad da muka fahimci cikar sani na Allah—musamman ma riga-saninsa — wannan na tabbatar mana cewa ko menene ya faru, ba ya ba Allah mamaki. Babu wani abu na gaggawa a mulkin sama. Ba wai kawai Allah ya san ƙarshe tun daga farko ba—Shi kansa ne Farkon da kuma Ƙarshen (Ruya ta Yohanna 21:6). Shi ne mamallakin komai. Musamman ma, Allah ya san waɗanda Ya zaɓa su kasance tare da Shi har abada. Idan, ta wurin jinƙai da alherin Allah, muka kai ga wannan wuri na ɗaukaka ta har abada, Yesu ba zai taɓa marabtar kowa da wadannan kalmomi ba, “Ban yi tsammanin ganin ka a nan ba!”. Maimakon haka, zai ce, “Ɗana, ina ta jiran ka. Ba za mu iya zaunawa yin liyafar auren ba tare da ka iso ba.” A wannan liyafa mai ɗaukaka, na gaskata cewa, kowace kujera za ta kasance da sunan mutumin da aka shirya wa. Har sai yawan fansassu sun cika, Allah yana jira da haƙuri sosai, “ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba” (2 Bitrus 3:9). Bari yanzu mu dubi muhimmiyar siffa ta uku da ke bayyana Ruhu Mai Tsarki: yana ko’ina. Idan muka ce Allah yana ko’ina, muna nufin cewa yana nan a kowane wuri a lokaci ɗaya. A cikin Irmiya 23:23–24, Allah da kansa ya tabbatar da wannan: Ta yaya hakan zai yiwu? Mun san cewa Allah yana zaune a kan kursiyin Sa a sama, tare da Yesu a hannun damansa. To, ta yaya zai iya cika sama da ƙasa da kasancewarsa? A cikin Zabura 139:7–12, Dawuda ya bayar da amsa. Da fari, ya yi tambaya: Wannan yana bayyana cewa ta wurin Ruhunsa ne Allah yake kasancewa a ko’ina a lokaci guda. Sa’an nan Dawuda ya karasa cikakkun bayanai sosai: Ko ina muka je, Allah yana wurin a Ruhunsa—ba a ganinsa, sau da yawa ba a iya fahimtarsa, amma ba a iya guje masa. Ga mara bi, wannan zai iya zama tunani mai ban tsoro. Amma ga mai bada gaskiya, ta’aziyya ce, ƙarfafawa da tabbaci ne. Duk inda muka tsinci kanmu, “har a can hannunka zai bishe ni, hannun damanka kuma zai rike ni.” A cikin Sabon Alkawari, Yesu kansa ya ba mu wannan tabbacin: “Ba zan bar ka ba, har abada kuma ba zan yashe ka ba” (Ibraniyawa 13:5). Wani lokaci, watakila ba ma ko jin sanin kasancewarsa tare da mu. Amma ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana nan. Yanayin da muke ciki na iya zama duhu ƙwarai, amma kamar yadda Dawuda ya ce, “duhu ba zai ɓoye ni daga gare Ka ba...” Ni da kai muna bukatar mu iya jin kasancewar Ruhu Mai Tsarki a cikin mu wanda ba ya dogara ga abin da muke ji a jikinmu ko muke iya gani ko ji ba. Idan bangarorin jikkunan mu ba su nuna mana komai game da kasancewarsa ba, ko ma suka ƙi, za a sami wani wuri a can cikin ruhunmu da ke jin kasancewar Ruhu Mai Tsarki a kowane lokaci. Sa’an nan za mu fahimci dalilin da ya sa aka ba shi sunan “Mai Ta’aziya” ko “Mai Taimako”. (Dubi Yohanna 11:26.) Babu wata hanya mafi dacewa ta rufe wannan wasiƙa fiye da gode wa Uba saboda ya aiko mana da Ruhu Mai Tsarki. Ko za ka yi wannan addu’a tare da ni?“Mai tsarki, Mai tsarki, Mai tsarki, Ubangiji Allah, Mai iko duka, wanda ya kasance a da, da yanzu, mai zuwa ne kuma!” (Ruya ta Yohanna 4:8)
Masanin komai
“Gama Allah Ya fi zuciyar mu girma, Ya kuwa san abu duka” (1 Yohanna 3:20)
“Ubangiji Allah kwa ya shirya ma sa zurman, ya sa kuma ya tsiro har ya rufe Yunana... Amma washegari, sa’ad da safiya tayi, Allah ya shirya tsutsa, tsutsa kwa ta buga zurman har ya yi yaushi.” (Yunana 4:6-7)
Allah ne Mamallakin komai
“ Waɗanda Allah ya riga ya zaba tun tuni, su ne ya ƙaddara su su dauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan ya zama farko a cikin ’yan’uwa masu yawa.” (Romawa 8:29)
Yana ko’ina
“‘Ni Allah na kusa ne kadai, ban da na nesa? in ji Ubangiji, Mutum ya iya ɓoye kansa a wani lungu, inda ba zan iya ganinsa ba?’ in ji Ubangiji; ‘Ashe ban cika sammai da duniya ba?”
“Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka? Ina zan gudu in tsere maka?”
“Idan na hau cikin samaniya, Kana can;
in na kwanta a lahira kana can, in na tashi sama, na tafi na wuce gabas,
ko kuma na zauna a can yamma da nisa, kana can domin ka bi da ni.
Kana can domin ka taimake ni. Da na iya rokon duhu ya boye ni,
ko haske da yake kewaye da ni ya zama dare, amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka.
Dare kuwa haskensa kamar na rana ne.
Duhu da haske, duk daya ne a gare ka?”
*Prayer Response
Ya Uba na sama, na gode maka da ka aiko mani da Ruhu Mai Tsarki, Mai ta’aziya da Mai taimako na. Ko lokacin da bana jin sa, na gode maka domin yana tare da ni kullum, yana ƙarfafa ni kuma yana tabbatar mani da kasancewarsa. Na gode maka saboda ikonSa da kariyarsa a gare ni da kuma waɗanda nake ƙauna. Ya Uba, yanzu ina roƙonka ka ba ni damar yin dangantaka mai zurfi da Ruhu Mai Tsarki. Ka taimake ni in ƙaunace Shi kuma in girmama Shi yadda ya kamata. Kuma na gode maka saboda ka amsa addu’ata, na yi dukan roke roken cikin darajar sunan Ɗanka, Yesu. Amin

*Free download
*This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.
Zazzage PDFLambar: TL-L126-100-HAU