A cikin shekaru da yawa na hidimata, na yi ƙoƙari na taimaka wa mutane da yawa da suke da matsaloli dabam-dabam a rayuwar su. Daga ƙarshe, na fahimci wani abu mai ban mamaki: ainihin matsalar mu a matsayin mu na ’yan adam ita ce rashin fahimtar darajar mu.

Saboda haka, muna yin kuskure mafi ban tausayi. Muna kama da mutumin da ya zama magaji ga dukiya mai yawa, amma muna sayar da dukan gādonmu domin wani abu marar amfani: batsa, yawan shan ƙwayoyi, shaye-shaye, son abin duniya, da yaudara.

Wadansu suna iya ɗaukar kansu da girma, su nemi matsayi mai girma a cikin siyasa, ko a duniyar nishaɗi, ko ma a fagen addini. Amma duk martabar da duniya za ta iya ba ka, ba a kwatanta ta da darajar gadon mu —wanda wasu za su iya watsi da shi don samun martabar duniya.

Idan muna so mu fahimci darajar mu a matsayin mu na ’yan Adam, dole ne mu yi la’akari da yadda aka hallici Adamu ta hanya mai ban mamaki ta mussaman — shi kakan jinsin mu.

This teaching series, Our Value, Our Worth, explores how precious we are to God.

Mu'ujizar Halittar Adamu

A cikin Yohanna 1:1–2, mun gano cewa ainihin wakili a cikin halitta ba Allah Uba ba ne, amma Kalmar Allah wadda ke tare da Allah tun fil’azal—Shi wanda daga baya aka bayyana a tarihin ɗan. Adam a matsayin Yesu Banazare:

“Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi [Kalmar] ne, ba kuwa abin da ya kasance, na abubuwan da suka kasance sai ta game shi.” (Yohanna 1:3)

Halitta gaba daya ta kasance ne tawurin maganar Allah: “Ta wurin bangaskiya mun gane cewa an halicci duniya bisa ga maganar Allah” (Ibraniyawa 11:3). “Gama ya fadi, aka gama; Ya umarta, magana ta tabbata.” (Zabura 33:9). Amma kamar yadda aka bayyana a Farawa 2:7, halittar Adamu na da bambanci na musamman:

“Ubangiji Allah kuwa ya sifanta mutum daga turɓayar ƙasa, Ya hura masa numfashin rai a cikin hancinsa. kuma mutum ya zama rayyayen taliki [a zahiri, mai rai].”

Dubi yanayin! Ubangiji ya durkusa, ya dauki turbaya a hannuwansa, ya hada ta da ruwa, ya siffanta jikin mutum. Ga shi nan-mafi kyakkyawan kira da aka taɓa kerawa-mafi kammala da ya kure aikin kowane makeri. Amma babu rai! Sai wani abin al'ajabi ya faru.. Mahalicci ya jingina gaba, ya sa lebbansa na Allahntaka a kan lebban yumbu, hancinsa na Allahntaka a kan hancin yumbu. Sa'an nan Ya hura numfashinsa a cikin waɗannan leɓuna da hanci. Numfashinsa ya ratsa siffar yumɓu ya mai da shi ya zama mutum mai rai, tare da kowace gaɓar jikin sa tana aiki da kyau, tare da dukkan abubuwan ban al'ajabi na ruhi, da hankali, da tunani waɗanda ɗan Adam ke iyawa. Ba a taɓa yin halitta irin wannan ba.

Numfashi mai Ƙarfi

Kalmomin da aka yi amfani da su don bayyana wannan mu'ujiza suna da haske na musamman. Ibraniyanci na ɗaya daga cikin waɗansu harsunan da sautin wasu kalmomi ke da alaƙa kai tsaye da aikin da suke bayyanawa. Sautin kalmar Ibraniyanci da aka fassara hura, ana iya fassara ta yipakh. Ta ƙunshi ‘yar karamar “fashewa” ta ciki, biye da sakin iska da karfi daga makogwaro. Ta haka, sautin kalmar na bayyana aikin kalmar a sarari.

Sa’ad da Ubangiji ya hura numfashinsa cikin waɗannan leɓuna da hancin yumbu, bai yi hakan da sakaci ba—Ya hura kansa da ƙarfi cikin wannan jikin yumbu, wanda ta haka, mutum ya karbi rabo mai al’ajibi na rai irin na Allah!

Nan take, mutum ya zama kashi uku, wanda ya ƙunshi ruhi, rai, da jiki. Ruhun ya fito daga numfashin Allah, wanda ya mai da jikin mutum, na turbaya, ya zama nama mai rai, mai numfashi. Ransa, wanda aka samar ta hanyar haɗa ruhu da jiki, ya zama halitta ta musamman, mai hali dabam, mai ikon yanke shawarar kansa—ni zan yi, ko ba zan yi ba.

Wakilin Allah

Tare da matarsa ​​da Allah ya ba shi, an naɗa Adamu yayi mulki a duniya a matsayin wakilin Allah. Zaman Adamu Kashi Uku (Jiki, Ruhi da rai ) ya kwatanta yadda Allah yake Matsayin Uba, da Da da Ruhu Mai Tsarki, amma daya ne. Siffarsa ta zahiri ta nuna kamannin Ubangiji wanda ya halicce shi (Farawa 1:26-27). Duka a cikin yanayinsa da sifarsa ta zahiri, ya wakilci Allah ga sauran halitta na duniya.

Bugu da ƙari, Adamu da Hauwa’u sun more zumunci da Ubangiji a kai a kai. A ƙarshen kowace rana yakan zo ya zauna tare da su (Farawa 3:8). Wa ya san irin abubuwan da ya bayyana musu a game da kansa? Mun san dai da cewa, Allah ya ba Adamu gatan zaɓen sunaye ga dukan sauran halittu (Farawa 2:19).

Duk da wannan kyakkyawar dangantaka, babban abun ban tausayi na tarihin ɗan Adam ya biyo baya. Shaiɗan ya ruɗi Adamu da Hauwa’u, suka yi musayar gādon da Allah ya basu da ’ya’yan itace! Wannan rashin biyayya ya shafi kowane sashe na kashi ukun nan na ɗan Adam. Ruhunsa— ya yanke hudda da Allah—ya mutu. A ransa ya zama ɗan tawaye, yana yaƙi da Mahaliccinsa tun daga wannan lokacin. Jikinsa ya koma ƙarƙashin cuta, tsufa, da mutuwa.

Allah ya gargaɗi Adamu game da itacen sanin mugunta da nagarta, “A ranar da ka ci daga gare shi, lalle za ka mutu.” (Farawa 2:17). Ruhun Adamu ne ya mutu nan take; duk da haka jikinsa bai mutu ba har fiye da shekaru dari tara.

Sabuwar Dangantaka

Rashin biyayyar Adamu ta samu sakamako mai muni, amma kuma ta kawo haske ga wani fanni na yanayin Allah wanda da ba zamu taba sani ba: zurfin ƙaunarsa marar ganuwa. Allah bai taba jin kasala akan Adamu da zuriyarsa ba. Yana marmarin ya jawo mu zuwa gare shi.

An bayyana wannan da kyau a cikin Yaƙub 4:5 : “ Ruhu wanda ya zamshe shi a cikin mu yana marmari zuwa kishi”—Ruhun da aka hura cikin Adamu a lokacin halittarsa. Ko da ya ke yana zama kamar abin mamaki, har wa yau Allah yana da marmarin zumuncin da ya taɓa morewa da Adamu. Tawayen Adamu ya karya wannan dangantakar, tawayen da aka dawwamar a cikin dukan zuriyar Adamu.

Bugu da ƙari, a farashi marar iyaka, Allah ya yi mana hanyar da za a mayar da mu zuwa gareshi. Ya aiko Yesu “domin ya nema, ya ceci abin da ya ɓace” (Luka 19:10). Ta wurin hadayarsa ta musanya akan gicciye, Yesu ya ba da damar a gafarta wa kowannenmu kuma a tsarkake mu daga zunubi kuma mu zama ‘yaýa a cikin iyalin Allah.

Darajar Mu Ta Gaskiya

A cikin Matta 13:45–46 , Yesu ya ba da wani misali wanda ya kwatanta da kyau game da wannan abin mamaki na fansarmu:

“Haka kuma, Mulkin Sama yana kama da mutum mai fatauchi yana neman lu’ulu’ai masu kyau, da ya sami ɗaya mai tamani da yawa, ya tafi ya sayasda dukan abin da yake da shi, ya saye shi.”

A gare ni wannan yana kwatanta fansar ran ɗan Adam. Yesu shi ne Mai fatauchin—ba ɗan yawon bude ido ba ne—amma mutum ne da ya saba yin cinikin lu’u-lu’u a duk rayuwarsa. Ya san ainihin darajar kowane lu'u-lu'u. Lu'u-lu'un da ya saya, rai ɗaya ne kadai na mutum, wato naka ko nawa. Yesu ya biya dukan abinda yake da shi—duk abinda ya mallaka.

A zamanin yanzu, ga yadda zan kwatanta irin wannan yanayin dan kasuwa a lokacin da zai ba matarsa ​​labarin.

“Uwargida, na sayar da motar mu.”

“Ka sayar da motar mu! To, aƙalla dai muna da wurin zama.”

“A’a, gidan ma na sayar da shi!”

“Me ya sa ka yi duk wannan?”

Na sami lu'ulu'u mafi kyaun gaske, wanda ban taɓa ganin irin sa ba. Na kasance mai neman irin wannan lu'u-lu'u duk tsawon rayuwata. Ya ci duk abin da muka mallaka-amma ki jira sai kin gan shi!"

Me wannan yake nufi a gare ni da kai? Ya kamata kowannenmu ya ɗauki kan shi a matsayin wannan lu'ulu'u mai daraja.

Mai fansar mu

Ka tuna, Yesu ya bayar da duk abin da yake da shi, ya fanshi ni da kai zuwa gare Shi. Ko da yake shi ne Ubangijin dukan halitta, Ya ajiye komai a gefe, ya mutu cikin cikakken talauci. Bai mallaki komai ba. Tufafin, da kabarin da aka binne shi a ciki duk na aro ne.

“Ko da shi ke mawadachi ne, duk da wannan sabili da ku ya zama da talauchi, domin ta wurin talauchinsa ku zama mawadata.” (2 Korinthiyawa 8:9)

Wataƙila ba ka taɓa ganin kanka da mahimmanci ba. Wataƙila ka raina kan ka. Watakila ka waiwaya baya ga rayuwar baƙin ciki da rashin jin daɗi, ƙuruciya ta rashin jin daɗi, auren da ya ƙare cikin kisan aure, aikin da a ka zata za a samu amma ba a samu ba, ko shekaru da aka yi a cikin hasarar shan kwayoyi da barasa. Rayuwar ka ta baya da wadda ke gaba, duk suna isar da saƙo ɗaya: sakon ka gaza!

Amma a wurin Yesu ! Ya ƙaunace ka har ya bayar da komai don ya fanshe ka don kansa. Don tabbatarwa da kuma karɓar wannan gaskiyar, ka na iya maimaita waɗannan kalmomi na Manzo Bulus: “Ya ƙaunace ni, ya ba da kansa domina” (Galatiyawa 2:20). Ka sake cewa, "Ya ƙaunace ni, ya ba da kansa domina." Ka mai da waɗannan kalmomin naka: “Ya ƙaunace ni, ya ba da kansa domina.”

Yanzu lokaci ya yi da za ka ga kanka kamar wannan lu'u-lu'u a riƙe a hannun Yesu mai tabon ƙusa gicciye. Ka ji muryar shi tana gaya maka cewa, “Kana da kyau sosai! Na bada duk abin da nake da shi, amma ba na nadama. Yanzu kai nawa ne har abada!”

Ba abin da za ka iya yi don samun wannan soyayya da karbuwa. Ba za ka taɓa canza kanka ko ka zama nagari sosai ba. Abin da kadai za ka iya yi shi ne yarda da abin da Yesu ya yi maka, sa’an nan kuma ka gode masa!

Kai nasa ne har abada!

17
Raba