A cikin wannan jerin mai fanni huɗu na kan maganar fahariya da tawali’u, muna yin nazari akan madawwamiyar doka ta bai-ɗaya da Yesu ya fada a cikin Matta 23:12:

“Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi; mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”

Ci gaba a Ruhaniya

A cikin wannan takardar Koyarwa, za mu ɗauki kashi na uku daga cikin kashi hudu da ke magana a kan muhimmin batu na yin nasara da girman kai da tafiya cikin tawali’u. Mun fara jerin da sanin cewa yanayin gwagwarmayarmu da girman kai sha’awa ce ta ɗaukaka kai da neman ’yancin kai daga Allah—hali ne da ya zama ruwan dare a duniya a yau, sai dai yana kai wa ga tawaye da halaka. Maganin wannan halin shi ne tsayawa ga ƙa’idar da Yesu ya faɗa a cikin Matta 23:12: “Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi; mai ƙasƙantar da kansa kuma ɗaukaka shi za ayi.” (Sabuwar Hausa) Kuma za mu bincika sakamakon da ke biyo bayan ɗaukaka kai da ƙasƙantar da kai. Game da Lucifa, wanda ya zama Shaiɗan, mun ga cikakken misali na ɗaukaka kai da sakamakon sa. Game da Yesu kuma mun ga kyakkyawan misali na ƙasƙantar da kai da sakamakon sa. Derek yana tabbatar mana da cewa waɗannan dokokin suna aiki daidai a cikin rayuwar kowane ɗayan mu.

A cikin koyarwarmu guda biyu na farko da suka gabata, mun yi nazarin rayuwar Yesu a matsayin cikakken misali na cin nasara a kan fahariya ta wurin ƙasƙantar da kai. Koyarwarmu ta gaba ita ce aiwatar da wannan tsari—mataki ne da dole ya faru ga kowanen mu domin mu fara shiga cikin rayayyiyar dangantaka da Ubangiji. Wannan ya kawo mu ga koyarwar mu ta yanzu, wadda a cikin ta za mu fahimci yadda ake buƙatar tawali’u domin mu kai ga girma a cikin rayuwar Krista. Ga kowanen mu, ci gaban mu zai kasance ne gwargwadon matakin da muke ci gaba da dauka na ƙaskantar da kanmu.

Roko Gabagaɗi

Da farko, ina so in mai da hankali a bangaren shugabanci na jikin Almasihu, a tsakanin mutanen Allah, almajiran Yesu. Za mu ɗauki misali daga wani abu da ya faru kusa da ƙarshen hidimar Yesu a duniya, wanda ke rubuce a Matta 20:20-28. A yanayin da aka kwatanta a wannan nassin, uwar almajiransa biyu—Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zabadi—ta zo wurin Yesu da roƙo na musamman a madadin ’ya’yanta biyu. Bari mu mai da hankalin mu ga roƙon da kuma amsar da Yesu ya bayar. Labarin ya fara a cikin Matta 20:20:

“Sa’an nan uwar ’ya’yan Zabadi ta matso wurinsa tare da ’ya’yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu. Sai ya ce mata, ‘Me kike buƙata?’ Ta ce masa, ‘Ka yi umurni wadannan ‘ya’yana biyu su zauna, ɗaya a daman ka, ɗaya a hagun ka a mulkinka.’ Amma Yesu ya amsa ya ce, ‘Ba ku san abin da kuke roƙo ba. [A lura, bai dora alhakin a kan uwar ba, amma a kan 'ya'yan. Ya yi musu magana. Sun kasance, a wani mataki, na ɓoyewa a bayan mahaifiyar su. Amma ya fito da su a fili, ya fallasa kuskuren manufarsu.] “Sai ya ce musu, Lalle za ku iya shan ƙoƙon da ni zan sha,?” Suka ce, ‘Za mu iya. Yesu ya ce musu, ‘Hakika za ku sha daga ƙoƙona, amma ku zauna a damana ko haguna ba nawa ba ne in bayar. Waɗannan wurare na waɗanda Uba na ya riga ya shirya wa ne.’ Da goman nan suka ji haka, sai suka ji haushin ’yan’uwan nan biyu.” (Sabuwar Hausa)

Babbar Buƙata

Me yasa suka fusata? Dalili ɗaya ne kawai zai iya zama dalilin fushinsu. Su da kansu su ma suna ɗokin samun wadannan wuraren ɗaukaka biyu na zama dama da hagun Yesu. A nan an bayyana dalilai da yawa a cikin wannan sassaukan al’amari.

“Yesu ya kira su ya ce musu, ‘Kun sani sarakunan al’ummai sukan nuna musu iko, hakiman su ma sukan gasa musu iko. Ba haka zai zama a tsakanin ku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikin ku, dole ne ya zama bawanku, wanda kuma yake so ya zama na farko, dole ne ya zama baranku...’” (aya 25-27,)

Wannan kalmar, “bawa” - kalma ce mai muni, ko ba haka ba? Amma duk da haka babbar buƙata ce aka bayyana. Idan kana son zama babba, dole ne ka zama bawa. Idan kana son zama na farko-mafi girma-dole ka ƙasƙantar da kanka. Dole ne ka zama bawa.

“...kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa. (aya 28,)

Don haka a nan mun ga ƙa’idar samun ɗaukaka cikin mulkin Allah. Ita ce dokar da muke ta dubawa a cikin koyarwarmu a kan girman kai da tawali'u. Hanyar yin sama ita ce kaskantar da kai. Idan kana son yin sama, to, ka sauko kasa. Idan kana so ka zama mai mulki - idan kana so ka zama shugaba - ka zama bawa. Idan kana son zama sarki, ka zama bawa.

Har yanzu kuma, ina so in jaddada cewa wannan ƙa'ida tana aiki a cikin kowace rayuwa, a kowane bangare na duniya. Babu wasu wurare da wannan doka ta ƙyale. Kamar yadda muka saba cewa a cikin duniyar da ake gani ba wani wurin da babu moganadiso (dokar nauyi), haka kuma ya ke a cikin duniyar ruhaniya. Wannan ita ce dawwamammiyar doka ta bai-ɗaya da Yesu ya fada a cikin Matta 23:12, “Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi; Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”. Babu wata halattacciyar hanya ta samun ɗaukaka cikin Mulkin Allah don zama shugaba, sai ta wurin ƙasƙantar da kai.

Bari in ba ku shawara cewa sau da yawa muna yin watsi da wannan doka a cikin ƙa'idodinmu na samun girma a cikin Ikkilisiya. Muna zabar mutane saboda sun je makarantar Tauhidi, saboda iliminsu, saboda baiwar wa’azi. Sau da yawa, irin wannan zaɓe yakan zama da haɗari ga Ikkilisiya domin mun yi watsi da asalin ƙa’idar—duk wanda bai koyi ƙasƙantar da kansa ba bai cancanci ya zama shugaban mutanen Allah ba.

Ƙayar da ke cikin Jikin Bulus

A wannan sashin, ina so in nuna muku yadda wannan ƙa’idar ta yi aiki a cikin abin da manzo Bulus ya ɗanɗana. Bari mu karanta shaidar Bulus game da abin da ya faru da shi cikin 2 Korinthiyawa 12:7-10. Kafin waɗannan ayoyin, Bulus yana magana game da manya-manyan wahayu na musamman da ya karba game da Bishara da Ikkilisiya daga wurin Ubangiji. Sa’anan ya bayyana yadda Allah ya bi da shi saboda wadannan wahayu.

“Don kada kaina ya kumbura, kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don ya rika wahalshe ni.”

Bari in fadi cewa ba lalle haka ne za mu yi tunani ba. Za mu yi tunanin cewa idan muna da manyan wahayu, komai zai tafi daidai. Rayuwa za ta kasance da sauki. Duk da haka, sau da yawa ba lallai ya zama gaskiya ba. Mutumin da yake da babban wahayi shi ne mutumin da ya fi shan wahala. Sai Bulus ya ce:

“Sau uku nake roƙon Ubangiji a kan wannan abu ya rabu da ni.”

Mu sani a nan cewa idan muka yi addu’a, muna buƙatar mu tuna da tabbataccen abu guda ɗaya. "A'a" amsa ce kamar "i." A wannan yanayin, Bulus ya yi addu’a sau uku—kuma duk lokacin da ya sami amsa iri ɗaya ce: “A’a.” Mun ga bayanin Ubangiji a aya ta 9:

“Amma ya ce mini, Alheri na ya ishe ka, domin ta wajen rashin karfi ake ganin cikar ikona. [Sai Bulus ya ci gaba:] Don haka (a wani ɓangaren, wannan shi ne sakamakon wannan ƙa’idar] saboda haka sai ma in ƙara yin fahariya da raunana ta da farin ciki, domin ikon Almasihu ya zauna tare da ni. Saboda haka, sabili da Kristi, ina fahariya da rauni na, cikin zagi, cikin ƙunci, cikin tsanani, cikin wahalu. Don sa’ad da nake rarrauna, a sa’an nan nake da karfi,.”

Zan yi mamaki ko za ka iya fadar haka. A gaskiya, ina tambayar kaina, "Zan iya faɗin haka?" Mutane nawa ne za su iya cewa, “Ina jin daɗin rauni, da zagi, da kunci, da tsanani, da wahala”? Ko ka fahimci cewa dalilin da ya sa Bulus ya ji daɗin waɗannan abubuwa shi ne don ya koyi ƙa’idodin— ƙa’idodi iri ɗaya da muke koyo a nan? Duk abin da yake ƙaskantar da ni, duk abin da ke kawar mini da ji da kai ko faɗin rai, ko dogara ga kai -wannan ita ce hanyar zuwa ɗaukakata. Daidai yadda na ƙaskantar da kaina, haka kuma Allah zai ɗaukaka ni. Yadda nake jin bani da komai, ta haka zan karɓi mai yawa daga wurin Ubangiji. Yayin da nake da rauni, to, ina da ƙarfi. Me ya sa haka? Domin ikon Allah yana cika cikin raunin mu.

Muddin muna ganin muna da komai, ba ma bukatar wani abu daga wurin Allah. Amma sa’ad da mu ka zubar da komai, lokacin ne muke da bukatar dukan abin da Allah ya tanadar mana—kuma same ya ke a kyauta.

Tawali'u a cikin Yohanna Mai Baftisma

A sashin mu na gaba, ina so ku ga yadda aka bayyana ƙa’idar da muke magana a kai cikin rayuwar Yohanna Mai Baftisma: Shi ne mutumin da yake da hidima ta musamman ta shirya hanyar zuwan Almasihu. A daidai wani lokaci cikin hidimar Yohanna, mutanen da suke bin sa sun ba shi labari mai ban mamaki game da Yesu, mutumin da ya zo ya shirya masa hanya. Wanda ya furta cewa shi ne Almasihu yana samun mabiya da yawa, mutane suna tuba ta hannunsa ana kuma yi masu baptisma fiye da na Yohanna kansa. Ina tsammanin mutanen da suka gaya wa Yohanna Mai Baftisma wannan labari sun sa ran zai ji ba dadi—ya ji takaici. Su na tunanin ransa zai baci ya kuma ji zafi. Su na tsammanin ba zai so ganin ɗan’uwansa ba—wanda kanensa ne kuma shi ne ya bude masa kofar fara hidima, yana samun nasara haka. Sun ɗauka cewa Yohanna ba zai so ya ga an ɗaukaka Yesu fiye da shi ba. Za mu iya gode wa Allah domin wannan ba shi ne tunanin da Yohanna Mai Baftisma ya yi ba. Bari mu ga abin da ya fada game da wannan magana a cikin Yohanna 3:30:

“Shi [wato Yesu] lalle ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa."

Akwai wani sirri a cikin wannan maganar! Kana son Yesu ya ƙaru a rayuwarka? To, dole ne ka ƙasƙantar da kanka. Kana buƙatar ƙarin ikon Allah? To, dole ne ka ga rauninka. Kana buƙatar shafewar Allah? To, dole ne ka watsar da dogaro ga kanka da kuma iyawarka. Idan ka ƙasƙantar da kanka sai Yesu ya ɗaukaka a cikin ka. Ikonsa yana cika a cikin rauninka, da kuma cikin rauni na.

Zuba Idanun mu

Wannan ya tuna mini da maganar marigayi mai bishara, Dwight L. Moody; "Da ina zaton cewa baye bayen Allah suna kan kantar ajiye litattafai ne wani kan wani; muna ƙara girma cikin halayen Krista abin na zama da sauƙi mu iya kaiwa gare su. Yanzu na ga cewa baiwar Allah tana kan kantar ajiye litattafai wata na ƙarƙashin wata. Ba zancen girma ba ne, zancen saukowa ƙasa ne; wajibi ne mu ƙasƙantar da kai, kodayaushe a ƙasa, don karɓar kyawawan baye-bayen sa.¹

A cikin dukan matakan da muke tattaunawa a cikin wannan koyarwa, ainihin sirrin shi ne mu zuba idanun mu a kan Yesu, shi kansa. Dole ne mu tuna cewa shi ne abin koyi—wanda a cikin sa ne wannan ƙa’idar ta cika sarai. Ibraniyawa 12:2 ta ce:

“Muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta [Ka tuna: Yesu ba fara sa mu bisa hanyar bangaskiya kaɗai ya yi ba, shi ne zai kai mu ƙarshen ta. Me yasa muke zuba ido a kansa? Saboda misalinsa.] Wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.” (Sabuwar Hausa)

Har yanzu, wace ƙa'idar muka gani an kwatanta a nan? Hanyar yin sama ita ce saukowa ƙasa. Kamar yadda ya kasance ga Yesu, haka yake a gare mu. Hanyar zuwa kursiyin ta wurin gicciye ne.

Aikin mu shi ne mu yarda da mutuwar duk wani girman kai, duk wani dogaro da kai, da duk abin da muke gani na jiki da zaton zama wani abu. Yayin da muka bar duk wannan son kai ya mutu a kan giciye da Allah ya tanada, hanyar zuwa kursiyin a bude ta ke. Don haka bari mu zuba idanun mu ga Yesu, shugaban bangaskiyarmu da mai kammala ta.

¹ ¹ Bayanan kula na Edita: Ainihin wannan maganar an danganta ta ne ga F.B. Meyer, wanda D. L. Moody ya yi tasiri sosai a rayuwarsa da hidimar sa ta bishara.

12
Raba