Ko Allah ya yi mana hanyar kuɓuta daga bautar mulkin duhu don mu zama magadan mulkin haske? I, Ya yi. Hanyar da Allah ya yi mana ita ce ta wurin mutuwar Yesu Kristi a madadinmu. A kan gicciye, Yesu ya ɗauki la'anar da ke tamu ta wurin rashin biyayyarmu, don ta haka, mu shiga cikin albarkar da Yesu ya samu ta wurin biyayyarsa. Waɗannan albarkun sun shafi dukan wuraren mulkin haske. Dukan la'anu da albarkun na nan a cikin manyan wurare uku na rayuwar mu: wato, na ruhaniya, jiki da na kayan duniya.

Abubuwan Amfana na Ruhaniya

Waɗanne la'anu ne na ruhaniya da Kristi ya cece mu daga gare su? Haka kuma, waɗanne albarku ne na ruhaniya da Kristi ya ba mu?

Da farko dai, bari mu dubi dalilan da ke kawo albarka da kuma abubuwan da ke kawo la’ana.

“Yanzu kuwa, idan za ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye dukan umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'ummai na duniya. Dukan waɗannan albarkun za su sauko maku, su zama na ku, idan za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku.” (Kubawar Shari’a 28:1–2)

Na gaba, Musa ya koma ga dalilin da ke sa la'ana ta zo.

“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ku kiyaye umarnansa da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau, dukan waɗannan la'ana za su auko ma ku. kuma su same ku.” (aya 15 )

Yana da matuƙar muhimmanci a gare mu mu fahimci takamaiman bambanci tsakanin karbar albarku da karɓar la'ana. An taƙaita wannan bambancin a cikin ‘yar gajeruwar magana mai muhimmanci: “Ku saurari muryar Ubangiji Allahnku.”

Muryar da muke saurara ita ce ke daidaita dukan makomar mu ta jin dadi ko bala’i. Sauraron muryar Ubangiji da yin biyayya ga abin da ya ce zai kawo albarka. Amma rashin sauraron muryar Ubangiji zai kawo la'ana mai yawa. Babu shakka, sauraron muryar Ubangiji kaɗai bai isa ba, sai dai idan mun yi biyayya da abin da ya faɗa. Akasin haka, ba zai yiwu a yi biyayya da abin da Allah ya ce ba sai da farko mun ji muryar sa, saboda muryar sa na gaya mana abin da yake buƙata mu yi.

Babban haɗari na ruhaniya da ke fuskantar Masu Bi shine su zama marasa jin muryar Allah. Da yawa suna iya ci gaba da ayyukan su na ibada, waɗanda suke na al'ada (salon rayuwar da suka yiwa kansu) duk da haka ba tare da ci gaba da sanin muryar Allah ba. A cikin dukan lokaci, abu ɗaya da Allah yake buƙata ga mutanen sa shine mu saurari muryar sa.

Littafi Mai Tsarki Yana Magana

Ubangiji da kansa ya bayyana wannan buƙata a fili cikin Irmiya 7:22–23. A cikin waɗannan ayoyin, Allah ya bayyana ainihin abin da ya buƙata daga Isra’ila.

Gama ban yi magana da kakanninku ba, ko kuwa na umarce su a ranar da na fito da su daga ƙasar Masar a kan hadayun ƙonawa da na sadaka ba. Amma wannan shi ne abin da na umarce su, cewa, ‘Ku yi biyayya da muryata, ni kuwa in zama Allahnku, ku kuwa za ku zama mutanena...’”

Lura da buƙata mai sauƙi da Ubangiji ya zama Allahn mu, mu kuma mutanen sa: “Ku yi biyayya da muryata, ni kuwa in zama Allahnku.”

Kuna iya tunanin cewa Sabon Alkawari ya bambanta, amma hakan ba zai zama gaskiya ba. Ƙa'idar duk iri ɗaya ce. Yesu ya taƙaita wannan a cikin aya ɗaya: “Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna kuwa bina” (Yohanna 10:27).

Alamar da gaske cewa mu na Yesu ne ba shi ne yin waɗansu salon ayyukan rayuwa ko ibada ba ne, amma dai cewa muna jin muryar sa— muna kuma jin muryar sa cewa mu bi shi. Hanya mai sauƙi na samun albarkun Allah ita ce ji da yin biyayya da muryar sa. Ƙarshen rashin ji da yin biyayya da muryar Allah shi ne karɓar la'ana.

Yanzu zan lissafa maku la'anaun da ke cikin duniyar ruhohi (na ciki) na halin mu wanɗanda sune sakamakon rashin biyayya da Allah. Musa ya jera waɗannan a cikin Kubawar Shari’a 28.

  • A cikin aya ta 20, Musa ya ce za mu ɗanɗana ruɗani a cikin duk abin da muke yi.
  • A cikin aya ta 28, bugu da hauka da ruɗewar zuciya.
  • A cikin aya ta 34, abin da muke gani zai sa mu yi hauka.
  • A cikin aya ta 65, rawar jiki da karayar zuciya.

Waɗannan su ne waɗansu daga cikin sakamako a ruhaniya da muke fuskanta a cikin rayuwar mutane a duniya a yau: ruɗewa, jin takaici, ɓacin rai da azaba.

Waɗanne ne albarku a ruhaniya ne a ke samu a sakamakon yin biyayya? Babu shakka, akwai albarku masu yawa. Amma na gaskata cewa za a iya taƙaita su a cikin wata gajeruwar kalma mai kyau: salama.

Sa’ad da Ishaya ya rubuta game da musayar da ta faru lokacin da Yesu ya mutu a kan gicciye, ya ce wannan: “Hukuncin da ya kawo mana salama a kansa ya ke.” (Ishaya 53:5). Yesu ya jimre hukunci da azaba saboda zunubi da kuma rashin biyayyar mu domin mu sami sulhu da Allah. A sakamakon sulhu da Allah, za a iya kuɓutar da mu daga ɓacin rai, azaba, ruɗani da jin takaici. Za mu iya sanin tabbatarciyar salamar gaskiya mai zurfi.

Bari mu duba waɗansu ayoyi biyu a Sabon Alkawari da suka yi maganar wannan salamar.

“To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.” (Romawa 5:1)
“Salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.” (Filibbiyawa 4:7)

Waɗannan kyawawan kalmomi ne! Ba mu da sauran laifi. Ba zamu zama da tsoron cewa wataƙila ba ma faranta wa Allah rai . Muna da salama tare da Allah. Wannan kyakkyawar ayar a cikin Filibiyawa 4 na bayyana sakamakon ɗanɗano a cikin mu. Salamar Allah zata kiyaye zukatan mu da tunanin mu a cikin yanayin wannan zamani.

A haƙiƙanin gaskiya, bisa ga Ibraniyanci, ma’anar kalmar nan salama ta wuce gaban rashin rikici kawai. Tana nufin lafiya ko cikakkiyar lafiya. Irin wannan salama na farawa ne daga cikin zuciyar mutum, amma ma har tana kaiwa ga samun cikakkiyar lafiya gaba daya.Tana shafar kowane wuri na rayuwar mu.

Abubuwan amfana na Jiki

Bari a yanzu mu koma ga Kubawar Shari'a 28 don mu dubi dukan la'anar da za a samu daga sakamakon rashin ji da kuma rashin yin biyayya da muryar Ubangiji. Babu shakka su na da yawa. Yayin da ka ke karanta wannan, ka tuna cewa an bayyana dukan waɗannan cututtukan ne a matsayin la'ana ga waɗanda ba fansassun mutanen Allah ba ne.

Annoba ta manne muku (aya 21); tarin fuka, zazzabi da kumburi (aya 22); marurai, basur, ƙazzuwa, da ƙaiƙayi (aya 27); makanta (aya 28); marurai daga tafin kafar ku har zuwa ƙoƙwan kan ku (aya ta 35).

Yawancin mu a matsayin Krista muna jimre la'anu maimakon mu more albarku. Me yasa? Wataƙila saboda dalilai guda biyu: ko dai domin ba mu san cewa la’anu ba ne ko kuma domin ba mu san cewa Yesu ya cece mu daga la’anar domin mu iya gādon albarkun ba. Karanta aya ta 59 ta Kubawar Shari’a 28 kuma ka duba ka ga ko kana cikin la’ana ko kuma cikin albarka.

“Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan annobai waɗanda ba su kawuwa, har ma da mugayen cuce- cuce waɗanda ba su warkewa.”

Hoto a Fili

Annabi Ishaya ya bamu hoto a fili na sakamakon rashin biyayya da tawaye. Da yake magana da ‘ya’yan Isra’ila, ya kwatanta halin da suke ciki daga sakamakon rashin biyayya, daidai da jiki wanda ke cike da cuta :

“Me yasa kuma za a yi muku duka? Me ya sa kuka dage da tawaye? Dukan kanku ya yi rauni, dukan zuciyarku kuma na ciwo. Tun daga tafin ƙafarku har zuwa saman kai ba a samun lafiya, sai dai raunuka, da ƙujewa, da buɗaɗɗen gyambo, ba a tsabtace ko a ɗaure ba, ko sanyaya da mai ba.” (Ishaya 1:5–6)

Wannan ayar misali ne mai kwatancin sakamakon rashin biyayya. Duk da haka, wata rana da nake karanta wurin, Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani wani abu mai ban mamaki da kyau. Na gane cewa Yesu ya riga ya ɗauki dukan la'anar a kansa saboda shine ya zama madadinmu. Waɗannan ayoyin ba hoto ne kawai na yanayin Isra’ila a sakamakon rashin biyayyarsu ba. Sun kasance kuma ainihin hoton Yesu yayin da yake rataye a kan giciye.

An bugi Yesu da bulala mai tsananin zafi ta Romawa, mai ninki kashi tara. Ya ji rauni a Kansa: an danna ƙaya a kansa. Zuciyarsa gaba daya ta wahala. Na gaskata cewa Yesu ya mutu da karyayyar zuciya. Wannan ayar ita ce ainihin bayani na Yesu yayin da yake rataye a bisa giciye. Me yasa yayi hakan? Domin ya fanshe mu daga la'ana ta wurin zama la'ana a madadin mu. Dukan waɗannan la'anoni da aka gani sakamakon rashin biyayyar mu ne ga Allah da suka zo kan Yesu yayin da yake rataye a kan gicciye.

Bari mu dubi albarkar jiki da Yesu ya saya mana. Za mu sake komawa, da farko, zuwa Ishaya 53:4–5:

“Lallai ya ɗauki ciwutarmu, ya ɗauki raɗaɗinmu, mu kuwa muna tsammani wahalarsa hukunci ne Allah ya ke yi masa. Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, aka doddoke shi saboda muguntar da muka aikata; hukuncin da ya sha ya ƴantar da mu, dukan da aka yi ta yi masa ya sa muka warke.”

Yesu ya ɗauki sakamako a jiki na rashin biyayya domin mu kuma mu sami warkarwa. Mun ga hakan a wannan maganar a ƙarshen aya ta 5, “Ta wurin dukan da aka yi masa muka warke.” A zahiri a cikin Ibrananci an ce, “Ta wurin raunukan sa aka yi warkawa domin mu.” Ko kuma za mu iya cewa, “ta wurin raunukan sa aka samo warkarwa domin mu.” Warkarwa ta zama gādon mu ta wurin raunukan da Yesu ya ji a jikinsa.

Sashi na gaba na wannan ayar an ɗauko ne a cikin Sabon Alkawari a cikin bisharar Matta, na bayyana hidimar Yesu wajen warkar da marasa lafiya da fitar da mugayen ruhohi. Wannan shi ne abin da yake cewa:

“Da magariba ta yi, suka kawo masa masu aljanu da yawa. Ya kuma fitar da aljannun da kalma, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. Wannan kuwa domin ya cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya: ‘Shi da kansa ya ɗauki rashin lafiyarmu, ya ɗauke cututtukanmu.’ (Matta 8:16–17)

Matta ba shi da shakkar wanda aka yi ambatawar a kansa a Ishaya 53. Ya yi amfani da ita ga Yesu. Ka lura kuma cewa Matta (wanda Bayahude ne kuma ya fahimci Ibraniyanci), ba shi da shakkar cewa waɗannan ayoyin na Ishaya 53 na magana ne a kan jiki. Warkar da marasa lafiya ta jiki ce da ta cika annabcin da aka yi a Ishaya.

Ka lura da abin da Yesu ya ce sa’ad da yake amsawa masu sukansa don warkar da mutum a ranar Asabar:

“Idan ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don kada a karya shari’ar Musa, kwa yi fushi da ni don na warkar da mutum sarai ran Asabar?” (Yahaya 7:23)

Yesu ya warkar da mutumin gaba ɗaya. Za a iya warkarda kowane ɓangare na ɗan Adam da halin mutum ta wurin Yesu.

Lura kuma da abin da Bitrus ya faɗa bayan warkar da gurgu a Kyakkyawar ƙofa a Ayyukan Manzanni 3:16. Ga yadda ya bayyana warkarwar:

“Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu, wannan mutumin da kuke gani kuka sani ya sami ƙarfi. Sunan Yesu da bangaskiyar da ke zuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, kamar yadda kuke gani duka.”

Menene sakamakon? "Cikakkiyar warkarwa." Yesu ya ce, “Na warkar da mutumin gaba ɗaya.” Wannan shine aiki a cikin jiki na fansar da Yesu ya yi mana. Muna godiya da aikin likitoci, da likitocin masu tabin hankali da sauransu. Amma akwai mutum ɗaya a duniya da zai iya cewa, “Na warkar da mutumin gaba ɗaya! Zan iya magance dukan matsalolin sa: na ruhaniya, tunani, na zuciya da jiki. " Wanene wannan Mutumin? Ubangiji Yesu Kristi.

Yayin da muke neman Yesu ta wurin bangaskiya bisa ga aikin sa na fansa, irin sakamakon da ya faru aka kuma rubuta a cikin Sabon Alkawari su na samuwa a gare ka da ni a yau ta wurin bangaskiya cikin Yesu.

Abubuwan amfana na rayuwa

Yanzu za mu dubi albarku da la’anoni musamman a gefen abubuwan rayuwa na duniya. Da farko dai, za mu dubi albarkun amfana na rayuwa da aka alkawarta na yin biyayya—kuma babu shakka su na da yawa. (Ba zai yiwu a cikin wannan ‘yar gajeruwar wasiƙar in lissafta su duka ba.) Ga abin da Musa ya ce a cikin Kubawar Shari’a 28:

  • Zaku zama masu albarka, ko kuna cikin gari ko cikin karkara (aya ta 3)
  • Masu albarka ne ‘ya’yan ku, da amfanin gonakin ku, da ‘ya’yan dabbobin ku, da yawan ƙaruwar shanunku, da na ‘ya’yan tumaki da awaki (aya 4)
  • Kwandunan ku, da makwaban zasu yalwata ƙullunku (aya 5)
  • UBANGIJI zai sa albarka a cikin rumbunku, da dukan abin da kuka sa hannunku (aya 8)
  • Za ku yalwata da wadata, da 'ya'ya, da dabbobin ku, da amfanin gonakinku a ƙasar da Ubangiji ya ba ku (aya 11).

Kalmar nan, “UBANGIJI za ya albarkace ku da wadata” na bayyana albarkun da ke fitowa daga ji da kuma yin biyayya da muryar Ubangiji. Musa ya ɗan yi dawowa ga ainihin batu iri ɗaya a cikin Kubawar Shari’a 29:9:

“Saboda haka ku kiyaye zantuttukan wannan alkawari, ku aikata su, domin ku sami albarka cikin dukan abin da kuke yi.”

Kiyaye kalmomin alkawarin Allah yana sa mu ci gaba a duk abin da muke yi. Wannan ba ya barin wurin gazawa ko takaici a kowane fanni na rayuwar mu. Waɗannan ne albarkun da aka alkawarta na yin biyayya.

A yanzu bari mu dubi la'anu na abin duniya domin rashin biyayya. Komawa ga Kubawar Shari’a 28:29, mun karanta:

“Da tsakar rana za ku yi nisa, kamar yadda makaho ke labe cikin duhu, ba kuwa za ku yi nasara a hanyoyin ku ba.”

Kamar yadda yalwar arziki albarka ce, haka kuma rashin wadata a hanyoyin mu la'ana ne. Haka nan kuma gaba ɗaya a fili, Musa ya sake faɗin wannan a cikin Kubawar Shari'a 28:47–48. A nan kai tsaye an jera albarku da kuma la’anu gefe da gefe.

“Domin ba ku bauta wa UBANGIJI Allahnku da farin ciki da murna da zuciya ɗaya ba, saboda yalwar kowane abu; Domin haka za ku bauta wa maƙiyanku waɗanda Ubangiji zai aiko su yi yaƙi da ku da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da rashin kome; Kuma zai sanya muku karkiya ta ƙarfe a wuyanku, har ya hallaka ku.

Ba za ku iya samun hoto mafi kyau fiye da na waɗannan ayoyi biyu ba. Sakamakon yin biyayya: yalwar dukan abubuwa, bauta wa Allah da farin ciki da murna. Sakamakon rashin yin biyayya: bauta wa maƙiya cikin yunwa, cikin ƙishirwa, cikin tsiraici, da cikin rashin komai.

A yayin da nake yin bimbini a kan waɗannan kalmomi wata rana, na ga cewa wannan bayanin talauci ne. Mutumin da yake jin yunwa, ba shi da abin da zai ci; ga ƙishirwa, ba shi da abin sha; tsirara, babu tufafin da zai sa; kuma a cikin rashin komai. Wannan mutumin na cikin matsanancin talauci. Ba shi yiwuwa a kwatanta talauci mafi girma fiye da haka: yunwa, ƙishirwa, tsiraici, da rashin komai. Muhimmiyar gaskiyar da muke buƙatar gani ita ce, talauci la’ana ne. Ba na mutanen Allah ba ne. Na sami wani farin ciki da gamsarwar da ta shiga cikin raina lokacin da na ga wannan a fili wata rana: talauci ba na 'ya'yan Allah ba ne. Ba na fansassun mutanen Allah ba ne. Maimakon haka, nufin Allah na da yawa da za mu bauta masa da farin ciki da murnar zuciya.

Wata rana, sa’ad da nake yiwa taron mutane wa’azi ga a New Zealand, Ruhu Mai Tsarki yayi ta nuna mani wani abu a lokaci daya cikin ruhuna ta yadda tunanin ya kasance tare da ni tun daga lokacin. Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani Yesu a kan giciye. Yana jin yunwa, Yana jin ƙishirwa,Tsirara yake, kuma Yana buƙatar dukan wadannan abubuwan. Me yasa? Dole ne ya kasance haka saboda ya gama kawar da la'anonin a madadin mu kwata-kwata. Me yasa? Saboda ni da kai, Masu Bi waɗanda aka fansa ta wurin jinin Yesu, ba sai mun jure wa wannan ƙarƙiya ta baƙin ƙarfe—wannan la'anar talaucin ba.

Musanya Ta Allahntaka

Talauci ba albarka ce da ke samuwa daga yin biyayya ba, amma sakamakon rashin biyayya ne. Godiya ga Allah, ko da yake dukan mu mun kasance marasa biyayya, Yesu ya ɗauki laifin mu duka. Tawayen mu da dukan munanan sakamakon sa, hade da talauci, an zuba a kan Yesu yayin da yake rataye a kan giciye.

An taƙaita wannan musanya a fili a cikin Sabon Alkawari. A cikin 2 Korinthiyawa mun sami batutuwa guda biyu na musayar a cikin kayan duniya. Bulus ya ce:

“Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, amma sabili da ku ya zama matalauci, domin ku ta wurin talaucinsa ku zama masu wadata.” (2 Korinthiyawa 8:9
“Kuma Allah yana da iko ya sa kowane alheri ya yawaita a gare ku, domin kuna da wadatar kome a kowane lokaci, ku sami wadata ga kowane kyakkyawan aiki.” (2 Korinthiyawa 9:8)

Menene musayar a wannan wurin? Yesu ya ɗauki talaucin mu a kan gicciye domin mu kuma mu samu samin wadata ta arzikin sa. Ta wurin alheri ne. Alheri na zuwa ta wurin Yesu Kristi ne kaɗai. Ba za a iya samun ladan alheri ba. Alheri na samuwa ne kawai ta wurin bangaskiya.

A cikin Hellenanci na asali, wannan maganar ta cikin 2 Korinthiyawa 9:8 na da ban mamaki. Kalmar yawan ta auku sau biyu, kuma kalmar duk ta auku sau biyar! Wannan ne abin da Yesu ya samo mana. Ya kawar da la'anar talauci domin mu gaji albarka.

Albarkun da ke cikin dukan wuraren nan uku da Yesu ya samar mana—na ruhaniya, na jiki da na kayan duniya—an hada su duka a cikin wannan kyakkyawar ayar ta wasiƙa ta uku ta Yohanna, aya ta 2, inda Yohanna ya ce:

“Masoyi, na yi addu’a domin ku sami wadata ta kowace fuska [wannan na abubuwa ne] kuma ku kasance cikin koshin lafiya [wannan na jiki ne], kamar yadda ranku ya wadata [wannan na ruhaniya ne].”

Wannan shi ne nufin Allah. Wannan gadon ku ke nan a matsayin Masu Ba Da gaskiya ga Yesu Kristi.

8
Raba