Yawancin Krista sun san cewa muna da gādo daga wurin Allah—alƙawuran da ya yi cewa yana niyar ya yi mana tanadi. Duk da haka, Krista da yawa ba su da cikakkiyar fahimtar ainihin yadda gādon mu ke zuwa gare mu. Wannan ya hana su shiga cikin gadon su, har su karɓi alƙawuran da ke ciki kamar yadda Allah Ya nufa.

Ayar da ke da matuƙar muhimmanci wajen fahimtar wannan maganar ita ce 2 Bitrus 1:2–4:

“Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijin mu. Allah da ikon sa ya yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma bin sa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakar sa da fifikon sa, waɗanɗa kuma ta wurin su ya yi mana baiwa da manyan alƙawuran sa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi’arsa, da yake kun tsira daga ɓacin nan dake a duniya da muguwar sha’awa ke haifa.”

Ina so ku lura da abubuwa guda biyu daga ayar da muka karanta: “Allah da ikonsa ya yi mana baiwa da dukan abubuwan da su ka wajaba ga rayuwa da kuma binsa” kuma “ya yi mana baiwa da manyan alƙawuransa masu ɗaukaka ƙwarai.”

A waɗansu lokuta na kan yi mamakin rubuce-rubucen da Bitrus ya yi, ganin mutum ne wanda ba shi da ilimi mai zurfi. Amma wasiƙun sa na ɗauke da matuƙar gaskiya—tunani da kalmomi masu nuna ilimi mai zurfin gaske. Haƙika, Bitrus ya sami ilimin sa daga wurin Ruhu Mai Tsarki— wato, malamin da har a yau, ya fi kowane malami a duniya.

Muhimman Abubuwan da za a Riƙe

Bin wannan tsarin daki daki, zan so in jawo hankullan mu game da waɗansu abubuwan da Bitrus ke faɗa a wanɗannan ayoyin, farowa daga aya ta biyu: “Alheri da salama su yawaita a gare ku.” Abu na farko shi ne: Tanadin da Allah ya yi domin mu a yalwace yake. Allah ba marowaci ba ne. Ba matalauci ba ne. Ba ya da buƙatar kuɗi. Shi ne mahalicci kuma tushen komai a duniya. Idan ya tanada mana, Ya na tanadawa a yalwace.

Bitrus ya ci gaba da cewa, “Ta wurin sanin Allah da na Ubangijinmu Yesu.” Wannan yana nuna cewa duk wani tanadi na Allah na zuwa ne ta wurin sanin Allah da kuma Yesu. Ina so in sa shi haka: Allah ne kaɗai tushen; Yesu ne kaɗai hanyar samu.

Daga nan za mu zo ga wannan maganar mai ban mamaki wadda aka yi a farkon aya ta 3: “[Allah] ya( riga ya) ba mu dukan abin da muke buƙata.” Mu lura da salon maganar–ba ta ce Allah zai ba mu ba; ta ce Allah [ya riga] ya ba mu duk abin da muke buƙata. Ka riƙe wannan gaskiyar da kyau, domin idan ta kuɓuce maka, ba za ka iya fahimtar yanayin tanadin Allah ba.

A sashi na biyu na aya ta 3, Bitrus ya sake komawa ga jigon cewa kasancewar komai na cikin Yesu: “Ta wurin sanin wanda ya kiraye mu ga samun ɗaukakarsa da nagartar sa [mafificin hali]. ” Wannan ra’ayi yana da matuƙar muhimmanci har ya sa Bitrus ya ambace shi sau biyu. Amma, kalmar da aka fassara a matsayin “sani” a aya ta 3 ta bambanta da kalmar da aka fassara a matsayin “sani” a aya ta 2. A aya ta uku, kalmar ‘’ sani’’ a Helenanci na nufin “amincewa.” Bitrus ba magana yake akan sanin Yesu, irin wanda ake samu a makarantun Tauhidi ba, amma ga amincewa da Shi—fahimtar ko shi wanene da kuma ba shi matsayin da ya cancanta a cikin rayuwar mu.

Bari mu maimaita waɗannan abubuwa guda huɗu:

  1. Tanandin da Allah ya ke yi mana a yalwace ya ke.
  2. Allah ne kaɗai tushe; Yesu ne kadai hanyar samu.
  3. Ikon Allah ya riga ya ba mu duk abubuwan da za mu taɓa buƙata. Allah ya riga ya yi wannan!
  4. Dukan komai na cikin sanin Yesu da kansa tare da ba Shi matsayin da ya cancanta, wato, matsayin sa na Ubangiji a rayuwar mu.

Menene Ba Mu Gane Ba?

A wannan wurin za ka iya duban rayuwar ka ka ce, “To, idan har Allah ya bayar, ni dai ban gani ba. Akwai buƙatu a rayuwata waɗanda ba a biya mani ba— amma kuma ni mai bi ne. Ina iyakar ƙoƙarina don in yi tafiya a matsayina na Krista kuma in zama ɗaya daga cikin mutanen sa.”

Idan Allah ya riga ya ba mu komai, to ina su ke? Me ya sa ba mu da su? Bari in ba ku wata muhimmiyar ganewa da Ruhu Mai Tsarki ya ba ni wasu shekaru da suka wuce game da wannan rikicin. Ya danganta ne akan aya ta 4 na wurin karatun mu:

“Ta wurin waɗannan [ɗaukaka da nagarta na Yesu] Allah ya ba mu alƙawuransa masu girma da daraja.”

Ayar da ta gabata na cewa: “Allah ya bamu duk abin da muke buƙata”. Wannan ayar na cewa, “Allah ya bamu alƙawuran sa masu girma da daraja.” Mecece ƙarshen maganar? Ai abin na da sauki kuma yana nan daki-daki. Dukan abubuwan da muke buƙata na ƙunshe a cikin alƙawuran Allah. Allah ya ba mu alƙawuransa—kuma a cikin su Ya ba mu dukan abubuwan da za mu buƙata domin rayuwar yanzu da har abada. Ina so in sa shi haka: “ Tanadin na cikin alƙawuran.”

Krista da yawa suna zaman rashi domin ba su iya gano wurin da tanadin Ubangiji yake ba. Yana cikin alƙawuran Sa. Kafin ka iya samun tanadin da Ya yi maka, sai ka san alƙawarin da Ubangiji yayi. Kuma dole ne ka san yadda za ka karɓe su– da yadda za ka shiga ka mallake su.

Canzawa ta wurin Alƙawura.

Sa’ad da muka sami alƙawuran da muke buƙata kuma muka fara karɓan su kuma muka yi amfani da su a rayuwar mu, zamu samu sakamako biyu masu ban mamaki. Aya ta 4:

“...domin ta wurin waɗannan [alƙawura] ku zama masu tarayya da Allah wajen ɗabi’arsa, da yake kun tsira daga ɓacin nan da ke duniya, da mugayen sha’awoyi ke haifa.”

Akwai sakamako guda biyu da za a samu daga karɓar alkawuran Allah-na daya za mu samu wani abu, na biyu kuma zamu rasa. Sakamako na farko ya ƙunshi yin tarayya da Ubangiji da kansa cikin ɗabi’arsa. Wannan magana mai ban mamaki ce sosai! Da Littafi Mai Tsarki bai yi wannan magana ba, da ba zan yi karambanin yin ta ba. Amma an yi ta dalla dalla: ta wurin karɓar alƙawuran Ubangiji mu ke tarayya da shi a cikin ɗabi’arsa. Sai ainihin ɗabi’ar Ubangiji ta shigo cikin mu, sa’an nan za mu ƙara zama kamarsa.

Wannan ya kawo mu ga sakamako na biyu, wato, “ mun tsira daga ɓacin nan da ke duniya da mugayen sha’awoyi ke haifarwa.” Tsohuwar ɗabi'ar mu na cike da gurɓataccen hali–na ruhu da kuma jiki. Amma yayin da ɗabi’ar Ubangiji ke shigowa, sai ta maye gurbin nan na gurɓatar da tsohuwar ɗabi’ar mu ta haifar domin tashi ɗabi’ar ba ta lalacewa. Ta haka mu ke samun sabuwar ɗabi’a, ta rayuwa da hali, yayin da muke karɓar alƙawuran Allah.

Wannan ya kai mu ga karshe mai muhimmanci kuma mai ban mamaki: Daga ƙarshe, Allah da kansa Shine gadon mu. Ba albarku ba, ba abin da muke ɗanɗanawa ba—amma ainihin gadonmu shine Allah da kansa! Ɗanɗanon mu, albarku da baye-baye duka suna da kyau. Amma ainihin manufarsa ita ce mu gaji Allah da kansa ta wurin alƙawuransa.

Gaskiya Guda Bakwai Game da Tanadi

Waɗannan bayanai guda bakwai sun taƙaita gaskiya game da tanadin Allah, da ke cikin jigon ayoyin da muka karanta, 2 Bitrus 1:2:

  1. Tanadin Allah a yalwace ya ke.
  2. Allah ne kaɗai tushen; Yesu ne kaɗai hanyar samu.
  3. Ikon Allah ya riga ya ba mu dukan abubuwan da muke buƙata.
  4. Komai na ƙunshe cikin sanin Yesu da kuma amimcewa da shi.
  5. (Kuma wannan ita ce hanyar fahimtar komai) tanadin na cikin alƙawuran.
  6. Ta wurin karɓar alƙawuran, muna yin tarayya da Allah da kansa a cikin ɗabi’arsa.
  7. Gwargwadon daidai yadda muke yin wannan, muna kuɓuta daga ɓacin da ke duniya ta wurin mugayen sha'awoyi, domin ɗabi’ar Allah da ɓacin da ke duniya ba sa jituwa.

Shiga Cikin Gadon Mu

Ainihin matakan da zamu bi domin mu shiga cikin gādon mu na samuwa a cikin littafin Joshua a Tsohon Alkawari, wanda ya bayyana yadda mutanen Allah, Isra’ilawa, suka shiga ƙasar da Allah ya yi musu alƙawari. Mun fahimci cewa, Joshua ya ba da misalin yadda mu ma za muyi koyi da shi. Bari mu fara da ayoyi uku na farko na Joshuwa sura ta 1:

“Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki, ya ce, ‘Bawana Musa ya rasu. Sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'ar nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba su, su Isra'ilawa. Duk inda tafin sawun ku ya taka, na riga na ba ku, kamar yadda na faɗa wa Musa.” (Joshua 1:1–3,

Ka lura da kalmomin da Allah ya yi amfani da su a cikin waɗannan ayoyi. A aya ta 2 ya yi amfani da kalmar da ke nuna abin da ke faruwa a lokacin da ake maganar, “Da ni ke ba su,” amma a cikin aya ta 3 ya yi amfani da kalmomin da ke nuna abin da an riga an yi a lokacin da ake magana, “Na riga na ba ku ƙasar.” Darasin shi ne wannan: Da zarar Ubangiji ya ce, “Na ba ku,” to, daga wannan lokaci an riga an bayar. Abu na biyu shi ne, Allah ya buƙaci dukan jama’ar su haye zuwa ƙasar da yake ba su. Na gaskata cewa akwai wani abu makamancin haka domin mutanen Allah a nan gaba, lokacin da dukan Masu Bi za su sami damar shiga cikin cikakken gadon su.

Daga lokacin da Allah ya furta alƙawarin sa, Isra'ilawa na da cikakken haƙƙin doka da Allah ya basu ga dukan ƙasar. Amma duk da haka ba su da mallakar ƙasar ta wurin ɗanɗanawar shiga da kansu. Ina so ku ga wannan muhimmiyar ƙa’idar: akwai bambanci tsakanin haƙƙi na doka da kuma ainihin mallakar abin da Allah ya yi mana alkawari a matsayin gadonmu.

Shiga Cikin Alƙawuran

Ainihin matakan da Isra'ila su ka bi domin shiga ƙasar sun fara ne da nasarorin su biyu na farko, waɗanda suka zo ta hanyar mu'ujizai. Mu’ujiza ce ta buɗe musu hanyar haye Urdun, kuma ta hanyar mu’ujiza suka ci birnin na farko, wato, Jericho. Amma ku saurara da kyau—bayan waɗannan, sai da suka yi yaƙi kafin suka sami sauran. Allah ya ce, “Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku.” (aya 3). Hanya ɗaya ƙadai da suka samu na ɗanɗana mallakar ƙasar ita ce ta hanyar sa tafin sawun su a ƙasa a inda su ke son su mallaka.

Wannan ya yi kama da abin da ke faruwa yayin da muke samun gādon mu. A cikin Tsohon Alƙawari, a ƙarƙashin shugaba mai suna Joshuwa, Allah ya jagoranci mutanen sa zuwa ƙasar Alƙawari. A cikin Sabon Alƙawari, a ƙarƙashin shugaba mai suna Yesu (mai ma’ana daya da Joshuwa), Allah yana bi da mutanensa zuwa ƙasar alƙawura. Sa’ad da aka sake haihuwar mu kuma muka zama ‘ya’yan Allah, bisa doka, mun zama masu gadon dukan abin da Allah yake da shi. Abin da Bulus ya faɗa ke nan a Romawa 8:16–17:

“Ruhu da kansa ma, tare da na mu ruhu suna yin shaida cewa mu ’ya’yan Allah ne. In kuwa ‘ya’ya muke , ashe, magada ne kuma—magadan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu…”

Wannan abin farin ciki ne. Mu abokan gādo ne tare da Yesu Almasihu a matsayin ’ya’yan Allah. Amma akwai ‘’idan’’ mai muhimmanci da ke biye:

“...idan dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa daukaka mu tare da shi.” (aya 17)

Don haka mu magada ne na dukan gādon - magadan dukan albarkun, amma kuma magadan shan wuyar. Ba za mu iya kauche wa shan wuya sa’annan mu sa ido ga samun albarkun ba. Sharadin shine “idan mun sha wuya tare da shi.”

Abin Da Ya Zama Dole Mu Yi

Domin samun mallakar gādon mu a matsayin mu na Masu Bi, muna buƙatar mu yi amfani da darasin da muka koya daga Joshua. Zan ba da shawarar waɗannan a matsayin manyan ƙa'idoji:

  1. Allah zai yi mu'ujizai. Amma Allah ba zai yi mu'ujizai a inda ba su da amfani ba.
  2. Kamar Isra'ila, dole ne mu yi yaƙi domin samun yawancin gādon mu. Ba za mu iya shiga cikin gādon mu ba, sai mun kasance a shirye mu ja ɗamarar yaƙi da ikokin duhu, da kuma yin nasara da su.
  3. Sai kowanen mu ya sa tafin sawun sa a kan abin da Allah ya alƙawarta ma na, kowa kuma ya samo wa kan sa. Sa’ad da muka yi hakan, za mu ga cewa babu makawa, muna tarayya cikin shan wuya ta Kristi.

A taƙaice, akwai abubuwa guda biyu da ya kamata mu yi: na farko, dole ne mu shirya yin yaƙi, na biyu kuma, mu na buƙatar sa sawun mu a wurin da muke karɓa a matsayin gadon mu.

Wato,— YI YAKI! SA TAFIN SAWUN KU!

Dukan Alƙawuran

Dukan gadon mu ya ƙunshi daidai dukan alƙawuran da Allah ya yi. Ayar da ke bayyana wannan gaskiyar sosai ita ce 2 Korinthiyawa 1:20, wadda za mu karanta a cikin fassarori biyu: Fassarar King James, kakkawar fasara, da kuma Fassarar NIV, wanda ya fito da ma’anar wannan ayar sosai.

“Gama dukan alƙawuran da Allah ya yi, a cikin sa [Yesu Kristi] akwai ‘I’, domin wannan fa ta wurin sa akwai Amin, zuwa darajar Allah ta wurin mu.” (King James)
“Komai yawan alƙawuran da Allah ya yi, “I” ne cikin Kristi. Ta haka ne ta wurinsa muke faɗar “Amin” domin ɗaukaka Allah.” (NIV)

Koda wace fassarar muka bi, waɗansu muhimman maganganu sun fito waɗanda zan yi bayanin su nan gaba. Da farko, gadon mu ya ƙunshi dukan alƙawuran Allah. Ba wasu daga cikin su ba — amma dukan su.

I, kuma Amin!

Na biyu, alƙawura ne masu yin aiki a halin yanzu. Dukan alƙawuran Allah ‘ I ’ ne da kuma AMIN — ba abin da ya wuce ba, ba kuma na nan gaba ba. A waɗansu lokuta akan fassara ayoyi ta hanyar da ke hana mana samun muhumman abubuwa masu yawa. Ga waɗansu misalai: “Mutuwar Manzanni ta kawo karshen yin Mu’ujizai,” ko kuma “samun wadata dai sai a lokacin mulkin Shekaru Dubu.’’ Wannan ya sa muna rayuwa a takure kuma da ƙyar. Amma waɗannan ayoyin sun nuna a bayyane cewa alƙawurran na yanzu ne.

Allah ba ya yin alƙawari daga baya ya canza zuciyar sa. Ba ya cewa,"Zan yi wannan ," daga nan kuma yace ‘’na fasa’’ a lokacin da muka je wurinsa domin karɓar abin da ya alkawarta. A nan muna da ɗaya daga cikin ayoyin Littafi Mai Tsarki masu nuna jaddadawa da ƙarfafawa: “Komai yawan alƙawuran da Allah ya yi, ‘I’ ne cikin Kristi.” I ne kawai, mai sauki, a bayyane.

Duk da haka, akwai wani abu da aka ƙara ga “I” na Allah. Fassarar (NIV) ta ce, “… ta wurin sa [Yesu] ‘Amin’ ne muke faɗa zuwa ga ɗaukakar Allah.” Kalmar nan Amin na nufin “bari ya zama haka,” ko kuma “bari ya tabbata.” Sa’ad da Allah ya ce, “I, ”muna sa ya zama haka da cewa “Amin!” Wannan ya sa alƙawarin ya zama namu a daidai wannan lokacin.

Wani ya ƙirga cewa akwai kusan alƙawuran Allah 8,000 a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma dukan su samammu ne a gare mu a duk lokacin da muke buƙata. Ga yadda na taƙaita muhimmiyar ayar mu, wato, 2 Korinthiyawa 1:20: “Kowane alƙawari da ya dace da yanayi na, ya kuma biya buƙata ta, nawa ne a yanzu.”

Cika Sharadi, Ci gaba da Gaskatawa

A ƙarshe, ina so in nuna wani muhimmin al’amari na samun alƙawuran Allah da Krista da yawa suka yi watsi da shi. Yawancin alƙawuran Allah suna da sharaɗi. A mafi yawan lokuta, idan Allah ya yi alkawari yana cewa: "Idan za ku yi haka-da-haka, to, ni zan yi-da-haka." Ba mu da ikon karɓar alƙawarin sai dai idan mun fara cika sharaɗin.

Kuma muna buƙatar mu fahimci cewa cikar alƙawuran Allah ba ya danganta ga yanayin mu. Ya danganta ne da cika sharuɗɗan Allah. Muna mai da hankalin mu akan sharuɗɗan kuma mu tabbata mun cika su maimakon mu ƙyale yanayin mu ya rinjayi bangaskiyar mu. Sau da dama abin da yakan faru shi ne Mai Bi na samun alƙawarin da yake buƙata. Sa’ad da ya fara karɓa, sai ya dubi yanayin sa marar kyau ya ce, “To, gaskiya ne, Allah ya yi wannan alƙawarin. Amma wannan ba zai yi aiki a halin da nake ciki ba. " A nan ne yawancin mu ke rasa gadon mu.

Bari mu dubi misalin Ibrahim. Allah ya yi wa Ibrahim alƙawarin ɗa, magaji, amma Ibrahim ya kai shekaru 99 bai haifi ɗan ba.

Me ya sa Allah yakan bar mu mu zo wurin da ake ganin ba zai yiwu ba kafin ya cika alƙawuran da muke nema ? Na gaskata cewa akwai dalilai guda biyu masu amfani. Da farko dai, sai an kawar mana da kwarin gwiwa. Sai mun kai ga inda muka san cewa idan hakan zai faru, Allah ne kaɗai zai yi shi. Wannan ne wurin da Ibrahim ya kai. Ya san cewa idan dai ta jikin sa ne, babu yadda alƙawarin zai cika. Don haka dole ya mayar da hankalin sa ga Allah kaɗai.

Na gaskata cewa dalili na biyu shine, idan alƙawarin ya cika, Allah ne zai sami ɗaukaka. Lokacin da akwai yiwuwar cewa za mu iya yin haka ta ƙoƙarin kan mu, to, za mu iya ɗan yaba wa kan mu. Amma idan muka zo wurin da muka san cewa ba za mu iya yin komai da ƙoƙarin mu ba—ƙoƙarin kan mu ya gaza—to, da gaske ɗaukakar ta Allah ce. Bari mu ɗauki Ibrahim ya zama misali a gare mu.

Bari mu kawar da yanayin da muke ciki domin mu cika sharuɗɗan Allah—kuma mu karɓi gado mai daraja da ke ƙunshe cikin alƙawuransa.

17
Raba