Dole Ne Mu Yi Tafiyar

Teaching Legacy Letter
*First Published: 2012
*Last Updated: December 2025
14 min read
Duk wata dangantaka mai ƙarfi tsakanin mutane biyu na buƙatar yin sadarwa a koyaushe. Idan ba tare da wannan ba, wannan dangantakar ba za ta daɗe ba. Aure kyakkyawan misali ne a nan. Namiji da mace za su iya yin aure da ƙauna ta gaskiya da burin ganin aurensu ya yi nasara. Amma idan ba su kafa dangantakewa tare da ci gaba da sadarwa mai kyau a tsakanin su ba, auren su zai rushe cikin ƙanƙanen lokaci. Haka yake ga dangantakar Krista da Allah. Idan babu buɗaɗɗiyar sadarwa akai akai tsakanin bangarorin biyu,ba za a taɓa sumun nasara ba, ko kaɗan. Dole ne mu koyi yin magana da Allah akai akai, kuma mu bar Allah ya riƙa magana da mu akai akai.
Yadda Allah Ke Yin Magana
Ta yaya Allah ke magana da mu? Da farko, ta wurin Maganar sa da ke a rubuce —Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki shi ne tushen duk abin da Allah ke so ya faɗa wa dukan Masu Bi. Fiye da wannan, Allah yana da wasu takamammun abubuwa da yake so ya faɗa wa kowane ɗayan mu ɗaiɗai da ɗaiɗai. Amma ba mu da ikon mu sa ran ji daga wurin Allah ta wata hanya ta musamman idan ba ma binciken dukan abin da Allah ya faɗa mana baki ɗaya a cikin Littafi Mai Tsarki ba.
Littafi Mai Tsarki ne tushen kowace tabbatacciyar sadarwa daga wurin Allah kuma shi ne ma’aunin da za a gwada kowace irin sadarwa da ta fito daga wani wuri. Amma, karanta Littafi Mai Tsarki kawai ba ya wadatarwa. A cikin 2 Korinthiyawa 3:6 Bulus ya ce, “..don kuwa rubutacciyar ƙa’ida, kisa take yi, Ruhu kuwa rayarwa yake yi.” Idan ba tare da Ruhu Mai Tsarki ba, duk abin da muke gani da idanuwan mu a shafukan Littafi Mai Tsarki matattun haruffa ne. Amma idan waɗannan haruffa suka zama hanyar Ruhu Mai Tsarki, to, ba gani kawai muke yi ba. Muna jin su a cikin zukatan mu a matsayin muryar Allah, shi da kansa ya na magana da mu kai tsaye.
Shekaru da dama da suka wuce, na tabbatar da wannan a fili cikin ɗanɗano na. A matsayina na masanin Falsafa, na shiga nazarin Littafi Mai Tsarki ta hanyar tunani mai zurfi da nazari, kamar yadda nake yi wa kowanne aiki na Falsafa. Sai na ga ba abin sha’awa ba ne, mai gundura, littafi wanda ba a iya fahimta . Na ci gaba da karantawa kawai domin ya zama mani dole. Bayan kusan watanni tara, Allah ya bayyana Yesu a gare ni a matsayin Ɗan Allah, kuma ya cika ni da Ruhu Mai Tsarki. Washegari da na sake buɗe Littafi Mai Tsarki domin ci gaba da karatu, na yi mamakin canjin da na gani. Kamar dai mutane biyu ne kaɗai a duniya - Allah da kuma ni. Kowace kalma da na karanta, Allah ne ke magana da ni kai tsaye. Haka ya kamata kowanne Krista ya karanta Littafin sa Mai Tsarki.
Domin mu ji Ruhu Mai Tsarki na magana da mu a cikin Littafi Mai Tsarki, akwai wasu muhimman sharuɗɗa da za mu cika.
Kawar Da Munanan Ɗabi’u
Da fari, dole ne mu kawar da kowace irin mummunar ɗabi’a ko dangantaka marar kyau. Yakubu ya ce, “Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyar ku, ku yi na’am da ita a cikin tawali’u” (Yakubu 1:21). Ana iya bayyana ƙazamta a nan da “rashin tsarki, miyagun tunanin zuciya”; halin ƙin ji shine son yin jayayya da Allah ko mayar masa da martani. Wannan kuwa akasin tawali’u ne. Haka ma Bitrus ya ce, “Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha’inci, da munafunci, da hassada da kuma kowane irin kushe, ...ku yi marmarin shan madara marar gami” (1 Bitrus 2:1–2). To, a nan, ga jerin munanan halaye da dole ne mu magance su kafin mu iya jin Allah na magana da mu yadda ya kamata a cikin Littafi Mai Tsarki. Kawar da irin waɗannan halaye ne zai ba mu damar kusantar Littafi Mai Tsarki da ruhun tawali’u da na son koyo.
A cikin Markus 10:14–15, Yesu ya sa ƙaramin yaro a matsayin misali na yadda za a karɓi gaskiyar Mulkin Allah. Muhimmin halin da yaro ke da shi na yin abu—wanda Yesu ya jaddada a wannan ayar—shi ne sauƙin yin koyo: nuna yardar yin koyo a fili ba tare da nuna son zuciya ko ra’ayin kai ba. A cikin Zabura 25:5, Sarki Dauda ya yi addu’a wadda za ta iya zama abin koyi gare mu a duk lokacin da muka buɗe Littatafan mu masu Mai Tsarki: “Ka bishe ni cikin gaskiyarka, ka koya mani; gama kai ne Allah na cetona, a gareka ni ke sauraro dukan yini.” Kalmar nan “sauraro” na nuna halin yin shiru, haƙurin sa zuciya. Sauraron Allah ta wurin maganarsa na da matuƙar muhimmanci har da yake buƙatar matsayin gaske mai fifiko a jerin al’amuran mu.
Kula Da Hidimomin Ka
An bayyana wannan ra’ayi ma sosai a cikin addu’ar wani babban bawan Allah, Musa: “Ka koya mana mu sani ranmu na dan lokaci ne, domin mu zama masu hikima” (Zabura 90:12). Wato, Musa yana cewa, ka taimake mu mu tsara ayyukan mu da hidimomin mu na kowace rana domin mu bar lokacin da muke buƙata don sauraron Allah da kuma karɓar hikima ta gaskiya wadda daga gare Shi kaɗai take fitowa. “ Ubangiji ne yake ba da hikima; ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa” (Karin Magana 2:6).
Zama Masu Aiki Da Maganar Allah
Duk da haka, kamar yadda Yakubu ya gargaɗe mu a cikin wasiƙarsa, jin Maganar Allah kaɗai ba ta isa ba. “Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai ba, kuna yaudarar kanku” (Yakubu 1:22). Ya ci gaba da cewa jin maganar Allah kamar kallon madubi ne. Yana nuna mana wurare a cikin rayuwar mu da Allah ba ya jin ɗadin su. Amma za mu amfana da hakan ne kawai idan muka yi gyare-gyare bisa ga abin da madubin ya nuna mana da mu ke buƙata.
A cikin Yahaya 7:17, Yesu ya ba mu alƙawari wanda shi ne muhimmi na fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki: “Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwar nan ko ta Allah ce ko domin kaina nake yi.” Sanin koyarwar nan ga waɗanda suke a shirye su yi abin da aka koya musu ne kawai. Yin biyayya na kai mu gaba cikin gaskiya, amma rashin biyayya na rufe gaskiyar kuma tana karkatar da mu ga yin kuskure.
Addu'a
Karanta Littafi Mai Tsarki ta wannan hanya na sa mu jin muryar Allah. Amma wannan rabi ne kaɗai na sadarwar mu da Shi. Ɗaya rabin kuma shi ne addu’a. A cikin Littafin Waƙar Wakoki, ango ya ce wa amarya: “Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryar ki; gama muryar ki tana da daɗin ji, fuskarki kuma tana da kyan gani” (Waƙar Wakoki 2:14). Wannan na bayyana halin Kristi zuwa ga mutane masu bada gaskiya gare Shi: yana marmarin jin muryar mu da kuma yin sadarwa ta sosai da mu. Yayin da muke zuwa wurin Allah cikin addu’a, a koyaushe mu tuna cewa ba shi da halin ko in kula ko kuma mai wuyar samu. Akasin haka, yana ƙaunar sauraron addu’o’in mu kuma yana son ya amsa su.
Dangantaka Ita Ce Muhimmiya
Addu’a ta ƙunshi abin da ya wuce roƙo kawai—wato, jerin buƙatu da muke gabatar wa ga Allah. Idan muka sake duban salon Addu’ar Ubangiji, za mu ga cewa rabin farko na wannan adduʻar na taimakawa mu daidaita kanmu don saduwa da Allah. Bayan haka ne sa’annan aka ƙarfafa mu mu gabatar da buƙatun mu. Da yake da ma, Yesu ya tunatar da mu, “Ubanku ya san buƙatunku tun kafin ku roƙe Shi” (Matiyu 6:8). Abu mafi muhimmanci a cikin addu’a ba wai sanar da Allah buƙatun da ya riga ya sani ba ne. Maƙasudin shi ne mu kafa dangantaka da Shi, ta yadda mu na da gaba gaɗin cewa zai biya mana buƙatun mu.
Idan muka dogara ga iyawar mu kawai, babu wanda zai iya yin addu’a yadda ya kamata. Sanin haka, ya sa Allah ya tanadar mana da taimakon da muke buƙata wajen addu’a ta wurin wannan Mutum ɗaya da Ya sa wajen fassara mana Littafi Mai Tsarki—wato, Ruhu Mai Tsarki. A cikin Romawa 8:26–27, Bulus ya bayyana aikin da Ruhu Mai Tsarki ke yi a cikin addu’o’in mu:
“Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da Kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishe da ba su hurtuwa. Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.”
Bulus yana magana a nan game da rashin ƙarfi (kumamanci). A wannan wurin, ba yana nufin wani rashin lafiya na jiki ba, amma yana nufin wani rashin ƙarfi da ke cikin halin ɗan adam tun asali. An bayyana wannan rashin ƙarfin ta hanyoyi biyu. A wani lokaci mun san cewa ya kamata mu yi addu’a, amma ba mu san abin da za mu roƙa ba. A wasu lokuta kuma, mun san abin da za mu roƙa, amma ba mu san yadda za mu yi addu’a a kansa ba. Bisa ga ainihin yanayin mu, Ruhu Mai Tsarki na ba mu taimakon da muke buƙata, yana koya mana yadda za mu yi addu’a da kuma abin da za mu roƙa. Addu’a guda ɗaya kaɗai da ya kamata mu yi ga Allah ita ce wadda Shi da kansa da farko ya ba mu ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
Bishewar Ruhu
Dogaron mu ga Ruhu Mai Tsarki ya wuce haka. Bai tsaya a kan fahimtar Littafi Mai Tsarki ko sanin yadda za a yi addu’a kawai ba. Ruhu Mai Tsarki shi ne zaɓaɓɓen Jagoran da Allah Ya tanada don ya bishe mu a kowane sashi na rayuwar mu ta Krista. “ Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne ’ya’yan Allah” (Romawa 8:14). A haka, muna da dangantaka da Ruhu Mai Tsarki ta fuska biyu, wanda ya yi daidai da kalmomi biyu “ƙofa” da “hanya” da muka ambata a wasikar da ta gabata (dubi Matiyu 7:14). Don mu zama ’ya’yan Allah, dole ne mu sami maye haihuwa daga Ruhu Mai Tsarki (dubi Yahaya 1:12, 13; 3:1–8). Wannan ne shiga “ƙofar.” Bayan haka, don mu rayu a matsayin ’ya’yan Allah, dole ne Ruhu Mai Tsarki ya bishe mu. Wannan ce tafiya ta cikin “hanyar.”
Wata jaraba ta wayo da sau da yawa ta ke fuskantar mu bayan mun shiga ƙofar maye haihuwa ita ce musanya dokokin addini da bishewar Ruhu Mai Tsarki. “Idan na yi addu’a kuma na karanta Littafi na Mai Tsarki na tsawon sa’a guda a kowace rana”, haka muke fadawa kan mu, kuma “idan ina zuwa sujada da ina bayar da zakka a koyaushe— idan kuma na kaurace wa wasu abubuwan jin daɗi ko nishaɗi—to, zan yi rayuwar Krista mai nasara.” Amma ba haka abin yake ba! Irin waɗannan dokoki—da wasu da dama—duk suna iya zama masu kyau kuma abin so. Amma ba za su iya maye gurbin zumunci da kuma bishewar Ruhu Mai Tsarki ba.
A gaskiya, idan muka dogara ga dokokin addini, to, muna raina Ruhu Mai Tsarki ne. Idan da dokoki za su iya yin dukan abin da ake buƙata, me zai sa Allah ya ba mu Ruhun Sa Mai Tsarki? Wannan shi ne kuskuren da mutanen Galatiyawa suka yi lokacin da Bulus ya rubuta musu, “Ashe rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku karasa?” (Galatiyawa 3:3). Aikin da Ruhu Mai Tsarki ya fara yi a cikin rayuwar mu, Shi kaɗai ne zai iya kammala shi.
Muryar Ruhu Mai Tsarki
Ta wajen neman buƙatar samun bishewar Ruhu Mai Tsarki, sau da yawa Krista na cewa, “Amma ta yaya zan tabbatar da cewa lalle Ruhu Mai Tsarki ne ke bishe ni? Ta yaya zan iya gane muryar sa?” A wani lokaci, ina haɗa wannan tambayar da wata tambaya: “Idan wayar salula ta yi ƙara na ɗauka, ta yaya zan san cewa matata ce ke kira? Ta yaya zan gane muryar ta?” Amsar babu shakka ita ce: na san muryar matata ce saboda na san matata. Shaƙuwar da na yi da matata ya sa ya zama da sauki a gare ni in gane muryar ta.
Haka ma abin yake a dangantakar mu da Ruhu Mai Tsarki. Domin mu iya gane muryar Ruhun, dole ne mu kulla dangantaka ta kut da kut da Ruhu kansa. Krista da yawa ba su fahimci halin Ruhu Mai Tsarki ba. Sun san cewa Allah Uba mutum ne, kuma Kristi Ɗan shi ma mutum ne, amma ba su gane cewa Ruhu ma haka yake ba. Duk da haka, shi ma Ruhu mutum ne kamar Uban da Ɗan. Muna buƙatar mu san shi kai tsaye kamar yadda muka san Uban da Ɗan.
Yadda muke ƙara sanin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma za mu ji muryar sa a fili da kuma gane hanyoyin bishewar sa dabam dabam. Idan ma’aurata suka zauna tare na tsawon lokaci, suna koyon yadda za su yi sadarwa da juna ba tare da morar kalmomi ba. Yin shiru, ɓata fuska, murza yatsu a hankali, kallo na musamman—duk waɗannan suna isar da saƙonni fiye da yadda yin magana za ta iya yin sadarwa.
Haka ma zai iya faruwa a dangantakar mu da Ruhu Mai Tsarki. Ba a koyaushe yake bayar da umarni cikin kalmomi ba. Yana da hanyoyi dabam dabam na nuna mana ko jagorantar mu: gargaɗin zuciya, shiru na nuna ƙin yarda, haskakawa na ƙarfafawa, ko kuma izawa da ke sa mu aikata abin da ba a yi shiri ba. Yayin da muke ƙara sauraron bishewar Ruhu Mai Tsarki, ta haka zamu iya ƙara yin tafiya cikin duniya da salama da tabbaci a matsayin ‘ya’yan Allah na gaskiya.
Idan muka yi tuntuɓe fa?
To a ce mun yi tuntuɓe a tafiyar mu ta Krista—har muka faɗi! Ko wannan na nufin mun kasa kuma babu abin da za mu iya yi game da hakan? Lallai, ba haka ba ne! Ga waɗansu kalmomin ƙarfafawa daga Sarki Dauda:
“Ubangiji yakan bi da mutum lafiya, a hanyar da ya kama ya bi. Ya kan ji daɗin halinsa. In ya faɗi, ba zai yi warwar ba. Gama Ubangiji zai taimake shi ya tashi tsaye.” (Zabura 37:23–24)
Dauda ya rubuta waɗannan kalmomi ne daga ɗanɗanon sa. Ya san yadda ake faɗuwa. Akwai lokacin da ya yi zina da matar abokin sa; sa’anan, domin ya ɓoye laifin sa, ya sa a kashe mijin matar da ya yaudara. Ya yi ƙoƙarin ɓoye zunubin sa na ɗan lokaci, amma Allah cikin jinƙansa ya bayyana komai ta wurin annabi Natan. Ta wurin furtawa da tuba, daga ƙarshe, Dauda ya sami gafara kuma aka maido da shi. (Dubi 2 Samaʼila, sura 11 da 12.)
An bayyana azaba ta jiki da ta zuciya da Dauda ya sha sosai kafin ya amince ya furta zunubin sa a cikin Zabura 32:3–5:
“Sa’ad da ban hurta zunubaina ba, na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini. Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji, ƙarfina duka ya ƙare sarai, kamar yadda laima take bushewa, saboda zafin bazara. Sa’an nan na hurta zunubaina gare ka, ban ɓoye laifofina ba, na ƙudurta in hurta su gare ka, ka kuwa gafarta dukan laifofina.”
Godiya ga Allah saboda wannan kalmomi na ƙarshe, “Ka gafarta!” Kada ka taɓa barin shaiɗan ya yaudare ka da cewa ka yi nisa sosai ko kuma zunubinka ya yi yawa fiye da yadda Allah zai iya gafarta maka. Ka tuna, shaiɗan shi ne “mai zargin” dukan Krista. (Dubi Wahayin Yahaya 12:10.) Manufarsa ita ce ya sa mu ji kasawa, rashin cancanta, da rashin yin nasara. Amma Allah ya tanada mana cikakkiyar gafara da kuma maido da mu.
An bayyana tanajin Allah guda biyu don zunubi a rayuwar Mai Bi a cikin 1 Yahaya 2:1: “’Ya ku Ya’yana ƙanana, ina rubuta muku wannan ne domin kada ku yi zunubi.” Wannan ne sashi na farko na wannan tanajin: “Domin kada ku yi zunubi.” Ta wurin bangaskiya cikin alherin Allah da ikon Sa, yana yiwuwa mu yi rayuwa cikin ‘yanci daga mulkin zunubi. (Dubi Romawa 6:1–14.) Amma, Yahaya ya ci gaba da cewa: “ In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu Mai adalci.” Wannan ne sashi na biyu na tanajin Allah: Idan muka yi zunubi, abin da ya kamata mu yi kawai shi ne mu juya ga Mai Taimakon mu da tuba da tawali’u, wato, Yesu Almasihu. Zai ɗauki matsalar mu zuwa gaban Allah Uba, ya kuma samar ma na da cikakkiyar gafara da tsarkakewa. “In kuwa muka bayyana zunuban mu, to, Shi mai alƙawari ne mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukan rashin adalci” (1 Yahaya 1:9).
Ta wannan hanyar gafartawa da tsarkakewa, za mu sake ci gaba da tafiyarmu ta Krista ba tare da jin kasawa ko rashin cancanta ba, tare da sa zuciya da dogara ga amincin Allah ba bangaskiyar mu ba.
“Na tabbata Shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.” (Filibiyawa 1:6)
“ Wanda yake kiran ku ɗin nan, zai kuwa zartar.” (1 Tasalonikawa 5:24)
Addu’ar Miƙa kai
A wannan lokaci, ya yiwu kana jin buƙatar ƙara miƙa kanka gaba ɗaya a cikin dangantakarka da Ubangiji. Wannan buri ne mai kyau, kuma ka tabbata cewa Shi ma yana so ya yi tafiya tare da kai cikin dangantaka ta kurkusa. Domin ka sa wannan burin cikin kalmomi, bari mu rufe wannan koyarwar da yin wannan addu’ar tare:
*Prayer Response
Ya Ubangiji, burina shi ne in yi tafiya tare da Kai a kurkusa. Ina so in ji Kana magana da ni ta cikin maganarka. Ina so in ji muryar Ruhu Mai Tsarki, kuma Ruhu ya bishe ni cikin duk abin da Ka ke so in yi. Na miƙa kaina wajen kawar da duk waɗansu halaye da ke hana wannan tafiya, in kuma kusance ka da maganarka da ruhu mai tawali’u da shirin yin koyi.
Da taimakon Ka, zan ɗauki matakan da suka dace don in kusance Ka a cikin dangantakar mu, in kuma bar Ruhun Ka ya jagorance ni cikin samun ƙarin kusanci, cikin zumunci da jagoranci. Kuma, Ubangiji, idan na yi tuntuɓe, na gode maka domin za Ka rike ni da hannun Ka yayin da na zo gare Ka cikin tuba.
Ubangiji, na gode domin za Ka kammala kyakkyawan aikin da Ka fara a ciki na. Za Ka cika shi. Ina murna da amincin Ka, tare da godiya mai yawa cewa za Ka ci gaba da jawo ni kusa da Kai kullum. A cikin sunan Yesu. Amin.

*Free download
*This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.
Zazzage PDFLambar: TL-L089-100-HAU