Allah Yana Nuna Hanya

Teaching Legacy Letter
*First Published: 2012
*Last Updated: March 2026
14 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
“Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyar ta mai wuyar bi ce” (Matiyu 7:14). A nan Yesu yana bayyana rayuwar Krista ta fuskoki biyu a jere: na farko, ƙunƙuntar ƙofa da dole ne mu shiga ta wurin ta, na biyu kuma, matsatsiyar hanya wadda dole ne mu bi cikin ta. “Kofa” na wakiltar ɗanɗanawar shiga guda ɗaya — wanda Littafi Mai Tsarki ke kira “samun ceto” ko “sabuwar haihuwa.” “Hanyar” kuma na nuna irin sabuwar rayuwa da wannan ɗanɗanon shigar ke kai mu gare shi.
A zahiri, Yesu na gargaɗar mu a kan ƙoƙarin raba waɗannan matakai biyu da junan su. Kofa ɗaya tak ta shiga matsatstsiyar hanya ita ce ƙunƙuntar ƙofa. Idan ba tare da maya haihuwa ba, ba za mu iya fara rayuwar Krista ba ma. A wani bangaren, dalilin shiga ƙofar shi ne yin tafiya cikin hanyar. Cikakkiyar rayuwar da Yesu ke gayyatar zuwa gare ta ba ta samuwa haka kawai don an shiga ƙofar, amma sai ta wurin ci gaba da tafiya a cikin hanyar da ƙofar ta buɗe mana.
Hanyar
Yana da muhimmanci sosai cewa kada mu ɗauki rayuwar Krista a matsayin wani yanayi na tsayawa wuri guda ga “samun ceto” ko “zama Krista” kawai. A farkon farawar Ikkilisiya, ba a fara morar kalmar Kristanci ba. Abin da muke kiran Kristanci a yau, a wancan lokacin ana kiransa da suna “Hanyar.” Alal misali, lokacin da Shawulu na Tarsus ya tafi zuwa Dimashka, ya karɓi wasiƙu zuwa Majami’un Yahudawa na Dimashka, “don in ya sami masu bin wannan Hanyar, ...ya zo da su birnin Urushalima a ɗaure” (Ayyukan Manzanni 9:2). Daga baya, bayan Bulus ya yi wa’azi na wani lokaci a Afisus, an rubuta bayanai biyu game da sakamakon: “amma da wasu suka taurare, suka ƙi bada gaskiya, suna kushen wannan Hanya a gaban jama’a,” kuma “a lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan Hanya ba” (Ayyukan Manzanni 19:9,23). (Don wasu misalai na wuraren da aka bayyana Kristanci a matsayin “Hanya,” dubi Ayyukan Manzanni 22:4, 24:14, 22.)
An bayyana irin wannan tunani a wasu wurare da dama a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Bulus ya ce wa mutanen Atina, “Domin ta gare shi [Allah] ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance” (Ayyukan Manzanni 17:28). Idan muna “raye,” za mu yi “motsi.” Rayuwa ba ta tsayawa wuri guda ko ta tsaya cak. A kullum tana nufin girma, motsi, bunƙasa, da ci gaba. Karin Magana 4:18 ta ce, “hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske har ta take tsaka.” A wannan tafarkin na rayuwar Krista, kullum muna matsawa gaba zuwa ga cikakken hasken. A duk lokacin da muka matsa gaba a hanyar, sai hasken ya ƙara haskakawa. Hasken jiya ba zai wadatar da yau ba. Babu damar tsayawa wuri guda, balle a juya baya. Ko yaya hasken baya yake, gaba dai ta fi haske.
Ko wannan ƙalubale na ci gaba da matsawa gaba a cikin hanyar Krista na da wahala da kuma nauyi a gare ka? Bari in ba ka kalmar tabbaci mai albarka: Ba a ce mu yi wannan tafiya mu kaɗai ba. Ubangiji da kansa zai kasance tare da mu a kowane takin da za mu yi. A ƙarƙashin Tsohon Alƙawari, Ya ba mutanensa wannan tabbataccin alƙawari:
“Kada ka ji tsoro, domin Ina tare da kai; Ni ne Allahnka. Kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka. Zan kiyaye ka, in cece ka” (Ishaya 41:10)
A ƙarƙashin Sabon Alƙawari Almasihu da kansa ne ya tabbatar mana da wannan.
“Ga shi, Ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.” (Matiyu 28:20)
Zai Yiwu Mutum Biyu su yi Tafiya Tare?
Don haka, dole ne mu koyi yin tafiya tare da Allah. Wannan na nufin ci gaba da yin dangantaka ta kanka tare da Shi. Amos 3:3 yayi tambaya: “Zai yiwu mutane biyu su yi tafiya tare, in ba su yarda da juna ba?” Ma’anar wannan ita ce, a’a. Don mu iya tafiya tare da Allah, dole ne mu “yarda” da Shi.
Duk da haka, bisa ga halitta, ba mu da jituwa da Allah. Akasin haka, Bulus ya gaya mana a Romawa 8:7 cewa, “halin mutuntaka gaba ne da Allah, gama ba ya bin shariʻar Allah, ba kwa zai iya ba.” Wannan “halin mutuntakar” na nufin tunani da halaye da suke na jiki a gare mu duka kafin alherin Allah ya fara canza mu. Wadannan suna tsayayya da Allah kai tsaye, kuma ba za a iya samun sulhu ba.
A cikin Ishaya 55:8–9 Allah ya bayyana mana a fili: “‘Gama tunanina ba tunaninku ba ne alʻamuranku kuma ba alʻamurana ba ne, in ji Ubangiji. Gama kamar yadda sammai suna da nisa a duniya, hakanan kuma alʻamurana sun fi naku tsawo.” Bugu da ƙari, Allah ba ya canzawa. A cikin Malachi 3:6 Ya ce, “Gama Ni Ubangiji ba mai sakewa ba ne.”
Tun da hanyoyin Allah da tunaninsa sun sha bamban da namu, kuma tun da Allah ba mai sakewa ba ne, to, abu guda ɗaya ne ya rage kawai. Idan muna so mu yi tafiya tare da Allah, dole ne mu ma mu canza: “Bari mai mugunta shi saki hanya ta sa, mara adalci kuma shi bar tunaninsa.” (Ishaya 55:7). Dole hanyoyin mu da tunaninmu su canza. Wannan canjin na buƙatar miƙa wuya gaba ɗaya da cikakkiyar sadaukarwa ta dukan rayuwar mu ga Allah.
Mallakar wanene?
A cikin surori goma sha ɗaya na farko na littafin Romawa, Bulus ya bayyana cikakken tanadin Allah don fansar mu ta wurin bangaskiya cikin Kristi. Daga nan sai ya buɗe sura ta goma sha biyu da waɗannan kalmomin: “Don haka, ina rokonku ’yan’uwa saboda jinƙai na Allah...” Menene “don haka” ke nufi? Yana nuna amsar da ake buƙata daga gare mu bisa ga dukan abubuwan da Allah ya yi mana. Menene wannan amsar? Ta na bayyane a cikin kalmomin da ke biye:
“...ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadar ku ta ainihi. Kada ku biye wa zamanin nan; amma ku bar halinku ya sake, ta wurin sabunta hankalin ku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato, nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.”
Babban batun da Bulus ke magana a nan shi ne na mallaka. A matsayin Krista, ba za mu iya ci gaba da ikirarin cewa mu mallakar kanmu ba ne. “Ashe ba ku sani ba, jikinku haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyar ku, wanda kuka samu a gun Allah? Ai ku ba mallakar kanku ba ne? Sayen ku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku” (1 Korinthiyawa 6:19–20). Wannan “farashi” da aka saye mu da shi shi ne “jinin Kristi mai tamani” (dubi 1 Bitrus 1:18–19). Tun da shike Allah ya saye mu da irin wannan tsadar, mu nasa ne, ba na kanmu ba ne.
Ko da yake dokar haƙƙin mallakar rayuwar mu ta Allah ce, ba zai tilasta mana haƙƙinsa da zai yi gaba da nufinmu ba. Maimakon haka, zai jira har sai mun fahimci dalilinsa na ikirarin hakan, mun kuma yarda mu miƙa jikkunan mu a matsayin hadaya mai rai. Kalmar mai rai na nuna bambancin da ke tsakanin hadayun Tsohon Alƙawari da na Sabon Alƙawari. A Tsohon Alƙawari, dabbobin da ake yiwa Allah hadaya da su kashe su ake yi. Amma a Sabon Alkawari, muna miƙa jikunan mu ga Allah a matsayin hadaya mai rai. Amma a ta kowace fuska, miƙa jikunan mu ga Allah cikakke ne kuma na ƙarshe kamar yadda aka yi da dabbobin da aka miƙa a Tsohon Alkawari.
Wannan miƙa jikkunan namu ga Allah ya kamata ya zama wani tabbatacce kuma tsayayye, wanda za mu iya bayyanawa cikin addu’a kamar haka: “Ya Ubangiji, bisa ga farashin da Ka biya na fansa ta daga zunubi, yanzu na gane cewa ni ba mallakar kaina ba ne, amma naka ne. Saboda haka, ina miƙa kaina gaba ɗaya—jikina da duk abin da ke cikin sa—gare Ka a matsayin hadaya mai rai. Daga yanzu zuwa gaba, ina roƙon ka, kuma na dogara gare Ka, Ka ɗauƙi cikakkiyar mallaka da iko na rayuwata. A cikin sunan Yesu. Amin.”
Sabunta Tunanin mu
Da zarar mun amince da mallakar Allah bisa rayuwar mu, an buɗe masa kofar kawo canje-canje da suka dace a cikin tafark imu da tunanin mu. Za mu fara ɗanɗana “sabunta tunanin mu.” Daga nan, yayin da aka sabunta tunanin mu, za mu fara “tabbatar da [ganowa ta wurin ɗanɗano] abin da Allah yake so, wato, nufinsa kyakkyawa abin karɓa, cikakke kuma.” Mun riga mun ga cewa tsohon tunanin mu wanda ba a sabunta ba “maƙiyin Allah ne” (Romawa 8:7). Allah ba zai taɓa bayyana nufinsa a gare mu cikin irin wannan tunanin da ke gaba da Shi ba. Amma yayin da ake ci gaba da sabunta tunanin mu da kuma samun daidaituwa da Allah, muna samun ikon fahimtar nufin Allah da kuma tafiya bisa ga tafarkin Sa.
Matakan sabunta tunanin mu na shafar manyan wurare uku na rayuwar mu: manufofin da muke son cimmawa, da muradin mu na cimma su, da hanyoyin da zamu cimma su. Bisa ga halitta dukan mu muna da son kai. Duk lokacin da muka so yanke shawara, muna tambayar kanmu irin waɗannan tambayoyi: Ta yaya wannan zai shafe ni? Me zan samu cikin wannan? Ta yaya zan cimma burina? Lokacin da muka daina mulkin rayuwar mu da kanmu, muka miƙa kai ga shugabancin Kristi, duk wannan zai fara canjawa.
Mun koya daga salon addu’ar Yesu a Matiyu 6:9–13 cewa manufar wannan salon rayuwa ita ce “Mulkin Ka shi zo,” kuma manufar ita ce “domin [Allah] ya sami ɗaukaka ta har abada.” Da zarar an sami amsar tambayar manufa da muradin, sai mu fuskanci tambayar ta yaya. Ta yaya zan yi rayuwa domin in ɗaukaka Mulkin Allah da kuma darajanta Shi?
Littafi Mai Tsarki yana koyarwa, kuma ɗanɗanon mu ya tabbatar da haka, cewa babu wani kokari ko ƙwazon mu da zai gamsar. Muna buƙatar wani iko. Amsar Allah ga wannan buƙatar na cikin Zakariya 4:6: “‘Ba da ƙarfi, ko iko ba [ba da ƙarfin jiki ko ƙwazon mutum ba], amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.” Ikon da zai wadatar shi ne ikon Ruhu Mai Tsarki kaɗai.
Tafiya ta wurin Bangaskiya
A farkon tarihin ɗan adam, an gabatar mana da misalin wani mutum da ya koyi yadda zai yi tafiya tare da Allah: “Anuhu ya yi tafiya tare da Allah; Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba” (Farawa 5:24). A cikin ci gaba da wannan tafiyar, Anuhu ya sami dangantaka ta kut da kut da Allah har ya kai ga cewa, a ƙarshe, ya fi masa sauƙi ya ci gaba da kasancewa cikin cikakken zumunci da Allah fiye da zama a gidansa na duniya.
Ibraniyawa 11:5–6 ta bayyana asirin yadda Anuhu ya yi tafiya tare da Allah: “Saboda bangaskiyar sa ce aka ɗauke Anuhu, shi ya sa bai mutu ba, ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi; tun kafin a ɗauke shi ma, an shaide shi da cewa ya farantawa Allah rai. In ba tare da bangaskiya ba, ba shi yiwu a faranta Ma sa rai.” Muhimmiyar kalma a nan, wadda aka maimaita domin jaddada muhimmancin ta, ita ce bangaskiya. Bangaskiya ita ce ginshiƙin da dole ake buƙata na yin tafiya tare da Allah wadda ke faranta Masa rai.
Mecece bangaskiya? Ibraniyawa 11:1 ta fada mana:
“To, bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar [tushe na gaskiya] abubuwan da ake bege a kai, ita ce kuma tabbatarwar abubuwan da ba a gani ba.”
Alʻamarin ruhaniya ne da ke sa mu mu iya rarrabe abubuwan da ba a bayyanawa hankulan mu ba. Yana danganta mu da tabbatattun abubuwa biyu da ba a iya gani: Allah da Kansa da kuma Maganar Allah.
A matsayin mu na Krista, Bulus ya fada mana, “Domin zaman bangaskiya muke yi, ba na ganin ido ba” (2 Korinthiyawa 5:7). A nan, “gani” na nufin ilimin kanmu. Ana gabatar da shi a matsayin akasin bangaskiya. Bangaskiya na ƙin dogara ga tunanin mu. Dogara ga tunanin mu na ƙin bangaskiya. Saboda haka, kowannen mu na fuskantar wannan tambayar: Wanne ne ya fi zama gaskiya a gare ni — Allah da Maganar Sa, ko kuma tunanina da ilimi na?
Bangaskiya ta gaske tana manne wa Allah da maganar Sa ba tantama, tana ƙin yarda da tunani idan har hakan ya saɓa wa maganar Allah. Babban misali na irin wannan bangaskiya a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne Ibrahim. Haƙika, an kira Ibrahim “uban dukan masu bangaskiya,” kuma an ƙalubalance mu da “mu yi koyi da bangaskiyar ubanmu Ibrahim” (Romawa 4:12). Maganar Bulus a nan tana tabbatar da abin da aka riga aka faɗa game da rayuwar Krista. Ba tsayawa wuri guda ba ne, amma “tafiya” ce inda muke yin gaba ta wurin takawa daga wani mataki na bangaskiya zuwa wani.
Yadda Za a yi Tafiyar Bangaskiya
A gaba kaɗan, a cikin Romawa 4:17–21, Bulus ya bayar da misali na musamman game da yadda Ibrahim ya yi tafiya cikin bangaskiya. Allah ya yi wa Ibrahim alƙawari cewa shi da Saratu za su haifi ɗa wanda zai zama uba ga babbar al'umma. Amma dukan su sun kai shekarun da ba zai yiwu su haifi ɗa bisa ga jiki ba, kuma har yanzu ba su sami ɗan ba. Da yake fuskantar wannan matsala tsakanin abin da Allah ya alƙawarta da kuma abin da tunanin sa ke fada masa game da jikin sa da na Saratu, Ibrahim ya zaɓi riƙe alƙawarin Allah, maimakon ya tsaya a kan yanayin jikin sa da na Saratu.
“Ba kuwa wata rashin bangaskiyar da ta sa shi shakkar cikar alƙawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa ya yi, yana ɗaukaka Allah, yana haƙƙaƙewa, cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alƙawari,.” (Romawa 4:20–21)
A cikin wannan tafiyar ta bangaskiya, a kullum muna hulɗa da duniya guda biyu. Ta wurin hankulan mu na jiki muna hulɗa da halitta ta duniya ta da ke kewaye da mu; ta wurin bangaskiyar mu muna hulɗa da duniyar da ba a gani ta har abada da kuma Maganar Sa, A cikin 2 Korinthiyawa 4:18, Bulus ya bambanta wadannan duniyoyi biyu. Ya ce, nufin Allah yana cika a rayuwar mu har ta wurin tsanani, “domin ba abubuwan da ido yake gani muke dubawa ba sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne” Akwai abubuwa masu saɓani da juna da Bulus ya yi amfani da su a nan. Ta yaya za mu iya duban abubuwa marasa ganuwa? Amsar ita ce: ta wurin bangaskiya. Bangaskiya ita ce “hankali” na ruhaniya da muke iya rarrabe tabbacin abubuwa marasa ganuwa, wato, duniya ta har abada.
Yana da muhimmanci mu tantance shaidar hankulanmu da kyau. Allah bai ce mu rufe idanun mu da kunnuwan mu mu yi tafiya kamar dai babu duniya ta zahiri da ke kewaye da mu ba. Bangaskiya ba sihiri ba ce. Ba mu na ƙin gaskata abin da hankulan mu ke bayyana mana ba ne, amma muna tambayar karshen abin.
Ibrahim shi ne cikakken misalin wannan al’amari. Hankalin sa ya gaya masa cewa jikin sa ba zai iya haifar da ɗa ba. Amma Allah ya yi masa alƙawarin samun ɗa. Ibrahim bai yi jayayya kan gaskiyar da hankalin sa ya nuna masa game da jikin sa ba. Ya ƙi amincewa da hakan a matsayin ƙarshen komai. A Inda Maganar Allah ta yi masa wani alƙawari, sai kuma hankalin sa ya gaya masa wani abu dabam, ya riƙe alƙawarin Allah da ƙarfi, ba tare da yarda hankalin sa ya sa shi yin shakka game da wannan alƙawari ba. A ƙarshe, bayan an gwada bangaskiyar sa, sai yanayin jikin sa ya daidaita da abin da Allah ya alƙawarta masa, kuma da gaske ya sami iko da ƙarfin iya haihuwar ɗa.
Haka kuma, bangaskiya na da alaƙa da tawali’u. A cikin Romawa 3:27, Bulus ya bayyana mana cewa alfahari ba ya cikin dokar bangaskiya. A cikin Habakkuk 2:4, an nuna cewa dogara da kai cikin alfahari da kuma bangaskiya mai tawali’u abubuwa ne da ba sa jituwa da juna, waɗanda ba sa kuma haduwa da juna:
“Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fadi, amma adali bisa ga bangaskiya zai rayu.”
Mutum mai girman kai wanda ya ɗaukaka kansa na nufin mutumin da yake dogara da iyawar sa ta halitta da ilimin sa. Amma mai adalci wanda ke rayuwa ta wurin bangaskiyar sa, shi ne mutumin da, kamar Ibrahim, ya ƙi dogara da iyawar sa da abin da hankalin sa ke nuna masa, maimakon haka ya zaɓi ya dogara da abubuwan Allah da Maganarsa waɗanda ba a iya gani amma suna dawwama.
A cikin Mikah 6:8, an gabatar da tawali’u a matsayin zabi da ake buƙatar mu yi domin mu iya tafiya tare da Allah: “Ya kai mutum, ya riga ya nuna maka abin da Ubangiji yake so gare ka; shi ne ka yi adalci, ka kaunaci aikata alheri , ka bi Allah da tawali’u?” Kalmar nan, “ƙasƙantar da kanka,” wadda a asalin Ibraniyanci, na nuna wani zabi da kowannen mu ya kamata ya yi: “Ya Ubangiji, na ƙi dogara da iyawa ta da ilimi na; na zaɓi in dogara gare Ka da kuma Maganarka. Ta wurin alherinka zan yi tafiyar bangaskiya, ba ta ganin ido ba.” Wannan hali na ƙasƙantar da kai da dogara ga Allah yana buɗe hanya don kusanta da ci gaba da tafiya tare da Shi.
A cikin wasikar mu ta gaba, za mu yi magana a kan wasu hanyoyi na zahiri da za su taimaka mana mu sami dangantaka ta kut-da-kut ta tafiya tare da Ubangiji.
Lambar: TL-L088-100-HAU