A matsayin zama uba, Allah ya haɗa manyan dama iri iri na shugabanci da manyan nawaya iri iri na shugabanci. Wannan jigon ya bi cikin Littafi Mai Tsarki daga farko har zuwa ƙarshe. A kwanakin nan masu ban tsoro na mugunta, daf kafin ruwan tsufana, akwai mutum guda ɗaya da ya sami alheri a gaban Allah—Nuhu. Allah ya ce wa Nuhu: "Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni" (Farawa 7:1). Adalcin Nuhu ne ya kare dukan iyalinsa. Saboda Nuhu ya ɗauki matsayin sa a gaban Allah da ya dace, a matsayin shugaban gidansa, ya sami damar shiga cikin jirgi da dukan iyalinsa.

To Noah, God said: “Come into the ark, you and all your household, because I have seen that you are righteous before Me in this generation” (Genesis 7:1). It was the righteousness of Noah that provided a covering for his whole household. Because Noah took his rightful place before God as head of his house, he had the privilege of bringing his entire family with him into the ark.

Daukar Shugabanci a Gida

Daga baya—bayan ruwan tsufana— Allah ya fara neman mutumin da zai zama shugaban wata al’umma ta musamman, wanda aka ƙaddara ya kawo albarku na musamman ga dukan 'yan Adam. A ƙarshe Allah ya sami mutumin da yake nema wanda shi ne Ibrahim. Littafin Farawa 18:19 ya bayyana kyawawan halayen Ibrahim da suka sa Allah ya zaɓe shi bisa mazajen zamanin sa:

"Gama na san shi, domin ya umarci ‘ya’yansa da iyalinsa da za su biyo bayansa, su kiyaye hanyar Ubangiji, su aikata adalci da gaskiya, domin Ubangiji ya ba Ibrahim abin da ya faɗa masa."

Allah ya zaɓi Ibrahim saboda ƙwaƙƙwaran dalili ɗaya: Ya san cewa zai iya samun tabbacin horar da 'ya'yansa da iyalinsa a cikin tafarkin Ubangiji. Wane irin muhimmanci ne Allah ya danganta da wannan sashi da halin mutum!

Allah ya so Ibrahim ya "umurci" 'ya'yansa da iyalinsa. Kalmar umurni ta yi tsauri sosai a kunnuwan ƙasashen Yammaci. Amma ita ce muhimmiyar kalma a cikin wannan ayar. Akwai lokutan da mutum yake da dama da kuma hakkin bada umurni. Sa’ad da ya tsaya a matsayin wakilin Allah da mai mulki a gidansa, bai kamata ya zama da rauni ko mai canza ra’ayi ba. Dole ne ya jajirce ya fada wa matarsa da 'ya'yansa, "Ina buƙatar ku yi abu kaza da kaza."

Wadansu maza za su iya yin tambaya, "Me matata da ‘ya’yana za su ce? Ba su saba ji ina magana haka ba!"

Ko in gaya maku ra’ayi na yadda za su mayar da martani? Zai iya ɗaukar su mintuna da yawa kafin su dawo cikin hankalinsu, amma daga ƙarshe za su ce, “Lallai—yanzu kam muna da namiji a gidan nan!” Matar da yaran duk sun san wanda ya kamata ya yi shugabanci, kuma za su bi uban da ya ɗauki matsayinsa da ya kamata. Mata da yawa sun ɗauki shugabanci a gidajen su saboda mijin ya kasa yin haka; kuma za su ji daɗin dainawa idan namijin zai ci gaba.

Gazawar Lutu

Mun ga cewa hali da iya sarrafa gidansa ne ya sa Ibrahim ya sami karɓuwa a wurin Allah. Amma, ɗan yayan Ibrahim, Lutu, ya zama akasin haka. Lutu ya fito tare da Ibrahim. Ya ga albarkun Allah ya kuma ji alkawurran Allah. Duk da haka ya ɗauki muguwar shawara ta wauta. Ya zaɓi ya kai iyalinsa cikin kazantaccen birnin Saduma (Farawa 13:10–13). Darasin Lutu yana taba ni sosai a duk lokacin na yi tunani a kai. Ya kai iyalinsa cikin Saduma, amma bai fitar da su ba! Lokacin da hukuncin Allah ya sauko a kan birnin, Lutu ya rasa dukan iyalinsa, sai dai 'ya’yansa mata biyu (Farawa 19:15–26).

Ubanni, bari in fada muku wannan a fili: Idan kun san tafarkin Ubangiji, kada ku yi wauta kamar yadda Lutu ya yi. Za ku iya kai iyalinku zuwa Saduma—zuwa cikin duniya mai annashuwarta ta zunubi da jan hankali. Kuna iya mayar da duniya ta zama jigon rayuwar gidanku. Rana na zuwa da za ku gaji da duniya ku juyo ga hanyar Allah. Amma ku tuna da wannan: ba lalle Iyalinku su yarda su ci gaba da bin ku ba. Ku da kuka kai su Saduma, ba lalle ku iya fitar da su ba!

Zaɓe Irin Na Joshua

Bari mu dubi wani shugaba na mutanen Allah—Joshua. A ƙarshen rayuwarsa, bayan ya kawo Isra'ila cikin Ƙasar Alkawari, Joshua ya ƙalubalance su a kan yanke shawara:

"Yau sai ku zabi wanda za ku bauta wa, ko gumakan Masar ko Kan’ana, ko Ubangiji kansa, wanda ya fisshe ku. Sai Joshua ya ƙara da cewa, “amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa" (Joshua 24:15).

Na ɗauki shekaru da yawa ina mamakin waɗanan kalmomi na Joshua. A fili, zai iya yanke shawarar kansa na bauta wa Ubangiji. Amma wane tabbaci ya ke da shi na cewa iyalinsa za su bauta wa Ubangiji? Wata rana sai na fahimci tushen tabbacin Joshua. Ya ɗauki matsayin da Allah ya ba shi a matsayin Firist, annabi da sarki a gidansa. Saboda haka ya san cewa zai iya dogara ga amincin Allah na girmama shi a wannan matsayin—ta hanyar amsa addu'arsa ta Firist domin iyalinsa, ta hanyar tabbatar da furucin annabcin da ya yi a madadinsu, da kuma ta hanyar ƙarfafa ikonsa na yin sarauta a kansu. Tabbacin Joshua bai ta'allaka a kan shi kansa ba, amma a kan amincin Allah ga matsayin uba da yake riƙe da shi.

Bangaskiya Ta Uba

Bari mu juya ga ɗaya daga cikin ayoyin da aka ke yawan ambato a Sabon Alkawari - Ayyukan Manzanni 16:30-31. Mai tsaron kurkukun nan na Filibi, da ya sami zurfaffar kashewa, ya tambayi Bulus da Sila, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?” amsar su ita ce, ‘Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

Wata rana da nake fadawa wata mata wannan alkawarin wadda take damuwa a domin ceton iyalin ta, Ruhu Mai Tsarki ya yi magana da ruhuna a hankali amma da nauyi: "Kana kuskure wajen amfani da wannan alkawarin. Ba ga mace aka fada wa wannan ba, amma ga namiji ne. A matsayin miji da kuma uba, Allah ya ba mai tsaron kurkuku na Filibi dama ya nemi ceton dukan iyalinsa." Allah ya ba kowane uba, saboda matsayinsa, haƙƙi da kuma nawayar yin bangaskiya domin ceton iyalinsa.

Ko wannan na nufin cewa waɗansu membobin iyalin za su iya samun ceto sakamakon bangaskiyar uban kawai, ba tare da su kansu sun shaida bangaskiya a matsayin mutum mutum ba? A'a, ba haka wannan yake nufi ba. Abin da yake nufi shi ne, ta wurin bangaskiya da hidimar uban bisa ga matsayin da Allah ya ba shi, kowane ɗaya a cikin iyalinsa zai bada gaskiya ga Kristi da kansa kuma ta haka zai sami ceto.

Hakan ba ya nufin cewa iyali ba za su iya samun ceto ta wurin bangaskiyar uwa ko kuma sauran mutanen gidan ba. Rahab, karuwa a Jeriko, ta ba da kyakkyawan misali na mace wadda bangaskiyarta da ƙarfin halinta sun kawo ceto ga dukan iyalinta. Daga cikin hallakar birnin gaba daya inda take zaune:

"Sai samarin da suka leƙo asirin Kasar suka shiga, suka fito da Rahab, mahaifinta, mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan wadanda suke nata" (Joshua 6:23)

Duk waɗannan sakamakon bangaskiyar Rahab ne.

Duk da haka, uba yana da dangantaka ta dabam da iyalinsa fiye da kowa a gidan. Idan ya ɗauki matsayin da Allah ya ba shi a matsayin shugaban gidansa, hakan yana tafiya tare da damar da Allah ya ba shi ta neman ceton gidansa. Wannan damar ba ta tsaya a kan bangaskiyar uban kaɗai ba, amma a kan matsayin uba da yake riƙe da shi. Allah yana duban matsayin, ba mutumin kaɗai ba.

Sakamakon Fanɗararrun Ubanni

Maganar Allah ta yi gargadi da yawa game da mummunan sakamakon da zai biyo baya lokacin da iyaye—musamman ubanni—suka gaza sauke nawayar da Allah ya ba su a cikin gida. A Maimaitawar Shari’a 28:15–68, mun sami dogon jerin la'anoni da Allah ya gargadi Isra'ila cewa za su auko musu idan suka ƙi yin biyayya da dokokinsa. Yayin da nake karanta wannan jerin wata rana, aya 41 ta taba ni sosai:

“Za ka haifi 'ya'ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba: gama za a kai su bauta”

An fadi wannan musamman ga ubanni, saboda kalmar nan "haifi" na bayanin ɓangaren uba ne na haihuwa.

Tunani mai sauki ya zo mani cewa Allah ne ke ba mu ‘ya’ya domin mu "ji dadin" su. Manufar ita ce su zama tushen jin daɗi na kullum a gare mu a matsayin iyayen su. Amma, a yau, iyaye nawa ne suke jin daɗin ‘ya’yansu da gaske? Na tuna lokacin da na ji wani mai wa'azi na Baptist mai iyali da yawa yana addu'a, "Ya Ubangiji, ka taimake mu mu tuna cewa ya’yanmu albarka ne, ba nawaya ba!" Sai na ji kamar cewa bai sa ran samun amsa mai kyau ga addu'arsa ba.

A matsayin iyaye, za mu iya zama da tabbacin abu ɗaya: Ya’yanmu za su gane ainihin halinmu a gare su—ko muna ɗaukarsu a matsayin nawaya ko albarku. Za su mayar da martani daidai da hakan.

Idan muka gaza yin horon ‘ya’yan mu da kuma yin dangantaka da su ta hanyar da ke nuna muna jin dadinsu, me zai zama maimakon haka? Maimaitawar Shari’a 28:41, ta bayyana mana a fili—"za a kai su bauta." Ko wannan bai faru da milyoyin ‘ya’ya a wayewar mu na ƙasashen Yammaci ba? Sun "je bauta"—ga ƙwayoyi, fasikanci, kungiyar asiri da sauran tarkunan Shaiɗan da ba sa ƙirguwa. Waɗannan irin yara suna cikin bauta kamar dai an kwashe su bauta ne zuwa wata bakuwar ƙasa. Wannan nawaya ta rataya a wuyan ubanni waɗanda suka gaza yin dangantaka mai kyau da ‘ya’yansu da kuma koya musu dokokin Allah.

Sadar da Shari’ar Allah

Malakai 2:7 na nuna Firist a matsayin jagora da mai fassara shari’ar Allah:

“Gama ya kamata leɓunan Firist su kiyaye ilimi,a kuwa nemi shari’a a bakin sa.”

(“Ilimin” da ake magana a nan shi ne ilimin shari’ar Allah.) A matsayin Firist a gidansa, kowane uba na da wannan nawaya—ya yi jagoranci ya kuma fassara shari’ar Allah ga iyalinsa.

To, idan ubanni/firistoci suka kasa daukar wannan nawayar fa? A Yusha’u 4:6, Allah ya taƙaita munin da irin wannan yanayi zai haifar:

“Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tun da yake sun ƙi ilimi, ni ma na ƙi su da zama Firist ɗina, tun da yake kun manta da umurnan Allahnku, ni ma zan manta da ‘ya’yanku.”

Abin tsoro ne sa’ad da Allah da kansa ya ce maka zai "manta" da ya’yanka! Sa’ad da uba ya yi watsi da sanin shari’ar Allah, bai cancanci ya ci gaba da yin hidimarsa ta Firist a madadin iyalinsa ba. Sakamakon haka, ‘ya’yan sun rasa ikon kariyar uba da lullubewarsa, sun zama abin kamu ga duk wani tarko da yaudarar Shaiɗan. Me ya sa a yau ƙasarmu ta cika da ‘ya’yan da suka manta da Allah —’ya’yan da suke zama baƙi ga alkawura da tanaje tanajen Allah? Domin ubannin su sun manta da shari’ar Allah!

Kalmar Alƙawari

A Malakai 4:5–6, kalmar ƙarshe da aka bar mana a cikin Tsohon Alkawari ita ce la'ana—amma kuma alƙawari ne:

"Ga shi, zan aiko muku da Annabi Iliya kafin babbar ranar nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo. Zai sake kawo iyaye da ‘ya’ya wuri ɗaya da ba don haka ba, da sai in zo in hallakar da kasar."

Ta wurin wahayin annabci, Littafi Mai Tsarki a nan na nuna matsalar zamantakewa ta gaggawa wadda ke zuwa daf da ƙarshen zamani: tsatstsaguwa, rarrabuwar gidaje, iyaye da ‘ya’ya suna nesa da juna. Maganar Allah daidai take! Wannan shi ne zahirin yanayin da muke fuskanta a yau. Akwai sakamako guda ɗaya da zai zo, sai dai idan an sauya shi -wato, la'ana a bisa dukan duniya. Duk da haka, Allah ya yi alkawarin samar da wata hidimar da za ta "juyo da zukatan ubanni zuwa ga ‘ya’yansu, da kuma zukatan ‘ya’ya zuwa ga ubanninsu." Godiya ga Allah, matsalar ba ta zama marar bege ba! Har yanzu yin sulhu da maidowa abu ne mai yiwuwa a gidajenmu. Wannan shi ne saƙon Ruhun Allah a gare mu yau.

Amma dole mu lura da tsarin da maganar Allah ta shimfida. Da farko, dole ne ubanni su juyo ga ‘ya’yansu. Dole ne sulhun ya fara daga wurin uba a cikin kowane gida. Idan ubanni suka tuba kuma suka ƙaskantar da kansu a gaban ‘ya’yansu, to, zuciyar ‘ya’yan ma za ta juyo ga ubanninsu. Amma matakin farko na ubanni ne.

Ina ƙalubalantar ubanni, ku zama mazaje! Ku tashi ku ɗauki matsayinku, a ƙarƙashin jagorancin Allah, ka zama shugaba na gidanka! Idan dama ka yi watsi da gidan ka, ka tuba ka roki gafarar matarka da ‘ya’yanka. Ka sulhunta da su. Sa’an nan sai ka jagoranci iyalinka zuwa cikin cikakken tanajin da Allah ya ke da shi domin su.

1
Raba