Don samun iko, dole ne mutum ya kasance a ƙarƙashin iko. Wannan ce ƙa'idar da ke jagorantar dangantaka a cikin gida. Lokacin da miji ya kasance a ƙarƙashin ikon Kristi, yana da ikon Kristi. Lokacin da mata ta kasance a ƙarƙashin ikon mijinta, tana da ikon mijinta a cikin gida. Amma idan an tsinke matakan ikon a wani gefe, to, iko ya rushe a cikin gida. Wannan ita ce babbar matsala ta yawancin gidaje a yau— a Amurka da kuma wasu ƙasashe. An sami katsewar iko saboda ɗaya daga cikin matakan ya fita daga matsayinsa. Ko dai miji bai bi Kristi ba, ko kuma mata ba ta bi mijinta ba. Sau da yawa duka biyun sun fita daga matsayinsu. Sakamakon: yamutsi, rashin jituwa da tawaye.

An yi ta samun koyarwa mai yawa game da biyayyar mace a cikin gida. Matan Krista da yawa suna jin haushin wannan koyarwa saboda suna jin cewa koyarwar na nuna cewa su " ƙasƙantattu" ne. Amma wannan ya samo asali ne daga rashin fahimtar ainihin dangantakar miji da mata.

Dangantakar Yesu ga Ubansa

Yesu ya fadi abubuwa uku game da dangantakarsa da Uba, waɗanda dukansu daidai suke da dangantakar mata ga miji.

Na farko, ya ce, "Ni da Ubana ɗaya ne" (Yahaya 10:30). Akwai cikakken haɗin kai tsakanin Yesu da Ubansa. Da yake shi ɗaya ne da Ubansa, haka kuma Yesu ya kasance daidai da Ubansa. Filibiyawa 2:6 ta gaya mana cewa yana da ikon zama "daidai da Allah." Shi Allah ne.

Haka kuma, miji da mata ɗaya ne. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa su "jiki daya" (Farawa 2:24; Matta 19:5–6). Babu wani ɓangare na jiki da zai iya zama "ƙasƙantacce" ga dayan; dukan ɓangarorin jiki daidai su ke. Matsayin biyayya ta mata ga mijinta bai nuna ƙasƙkanci ta kowace hanya ba, domin ayar ta bayyana a sarai cewa Allah yana duban miji da mata a matsayin ɗaya a cikin jikin Kristi (Galatiyawa 3:28).

Abu na biyu da Yesu ya ce game da dangantakarsa ga Uba shi ne Allah yana buƙatar "dukan mazaje su ɗaukaka Ɗan kamar yadda suke daukaka Uban" (Yahaya 5:23). Uban da kansa ya ɗaukaka Ɗan ta hanyar sa dukan halitta a ƙarƙashin ƙafafunsa (Afisawa 1:22). Uban yana jin daɗin ɗaukaka Ɗan (Filibiyawa 2:9–11). Yana jin ɗaɗin ɗaga shi sama da kuma sa dukan abubuwa a ƙarƙashin sa. Babu wata kalma ta Uban da ke "ƙasƙƙantar" da Ɗansa, ko kuma ƙoƙarin samun ɗaukaka fiye da Ɗansa. Jin ɗaɗin Uban shi ne ya ɗaukaka, ya fifita da kuma kafa Yesu a bisa dukan halitta.

Ya kamata halin da miji zai nuna wa matarsa ya nuna irin halin da Uba ya nuna ga Yesu. Ya kamata miji ya ji ɗaɗin ɗarjanta da kuma ɗakaka matarsa. Ya kamata ya yi duk abin da zai iya yi don ganin ya sa ta ji cewa yana girmama ta, daukaka ta, yabon ta kuma yana darajanta ta. Allah Uban ba zai yarda da wani rashin girmamawa da za a yi wa Yesu ba—ballantana shi da kansa ya yi masa haka! Ya kamata halin da miji zai nuna wa matarsa ya kasance daidai da haka. Bai kamata mata ta nemi daukakar kanta ko ta kafa matsayinta da kanta ba. Mijin ne ya kamata ya yi mata hakan. Ta haka ne za a kawar da duk wani tunani na ƙasƙanci.

Menene zai faru idan mu mazaje muka ci gaba da bi da matayen mu ta wannan hanyar? A yawan lokaci, za su amince da shugabancin mu cikin jin ɗaɗi kuma da yardar rai. Ba za su sake marmarin faɗan neman suna ko 'yancin kai ba.

A cikin Ibraniyawa 1:3, marubucin ya fada mana cewa “Yesu shi ne "hasken ɗaukakar [Uban] Sa ." A cikin 1 Korintiyawa 11:7, Bulus ya gaya mana cewa "mace [mata] abar taƙamar miji ce." A nan kuma, akwai kamanceceniya tsakanin dangantakar Allah Uba ga Yesu da kuma dangantakar miji ga matarsa. Uban na bayyana ɗaukakarsa a cikin mutuntakar Yesu. Miji kuma na bayyana ɗaukakarsa a cikin matarsa.

Idan mata ta sami kwanciyar hankali, natsuwa, da wadar zuci, hakan yana kawo ɗaukaka ga mijinta. Wannan na nuna cewa mijinta yana kula da ita yadda ya kamata. Amma idan matar na da ɗacin rai, jin an ƙi ta, da rashin kariya, hakan na rashin martaba ga mijinta. Wannan na nuna cewa ya kasa cika haƙƙoƙin sa gare ta. An tambayi wani shahararren mai wa'azi idan ko wane Krista ne nagari. Amsar sa ita ce: "Ban sani ba; ban haɗu da matarsa ba tukuna. Zan gaya muku idan na gan ta!"

Wannan ya kawo mu ga ɓangare na uku na dangantakar Uban da Yesu. Yesu ya ce, "Ubana ya fi ni girma" (Yahaya 14:28). Ga wani abu ne da ya bambanta a fili: Yesu daidai yake da Uban, amma duk da haka ya ce Uban ya fi girma. An faɗa game da Yesu cewa, "Bai maida daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai rike kankan ce ba" (Filibiyawa 2:6 Sabuwar Hausa). Bai yi wata kokuwa don samun karɓuwa ko iko ba, amma ya miƙa kansa ga Ubansa da yardar ransa ya kuma bari Ubansa ya ɗauki matsayinsa na shugabanci. Yayin da ya ci gaba da yin biyayya ga Ubansa, Yesu ya tabbatar da haɗin kai a cikin Allantaka. Da ace ya bar matsayinsa na biyayya na yardar rai, maiyiwuwa ne da an karya haɗin kai da ke cikin Allahntaka.

Haka kuma, ko da yake mata ɗaya take da miji—kuma daidai take da shi—Allah ya kira ta ta mika kanta ga mijinta domin samun haɗin kai da tsari a cikin gida. Idan ta ƙi, za a sami matsalar haɗin kai a cikin gidan, kuma zai haifar da yamusti. Dubban matayen Krista masu farin ciki za su shaida cewa sun sami kariya da lulluɓewa a ƙarƙashin ikon mazajensu, haƙiƙa shi ne wurin da Allah ya shirya don tsaro da salama.

Duk da haka, wannan ya dora babbar nawaya a kan mata. Yana nufin cewa babu wani namiji da zai iya zama shugaban gidansa da gaske sai dai idan matarsa ta amince da ikonsa. Babu kan da zai iya aiki ba tare da wuyan da ya riƙe shi ba; kuma babu namiji da zai iya zama shugaban gidansa da gaske ba tare da miƙa kai da goyon baya na matarsa ba.

Mene ne zai faru idan ɗaya daga cikin abokan tarayyar ya kasa cika matsayin da Allah ya ba shi a cikin gida? Ko wannan zai hana abokin zaman ɗaukar na sa nawayar? A'a! A karshen haƙƙin kowanne abokin zama ga Allah ne, ba ga abokin zaman ba. Kowanne yana da matsayin biyayya da ya kamata ya ɗauka a gaban Allah, kuma halin abokin zaman ba zai canza wannan ba.

Na taba jin wannan ƙa'idar a sarari a kotun masu karya dokar tuƙi. Mai shari'a yana tambayar wani mutum da ake tuhumarsa da wuce adadin gudu bisa doka. "Ko kana gudu fiye da dokar tuƙi?"

"Akwai motocin da suka yi gudu fiye da ni," mutumin ya amsa.

"Ba ruwanka da sauran motoci!" Mai shari’a ya maida masa. "Maganarka kawai a kan motar da kake tukawa ce. Ko ka wuce gudun da dokar tuƙi ta tsara?" Cikin ruwan sanyi, sai mutumin ya amince cewa ya yi!

Haka yake tsakanin miji da mata. Wata rana "Don lalle ne a gabatar da mu a gaban kursiyin shari’a na Almasihu" (2 Korintiyawa 5:10). A wannan ranar, ba za a buƙaci miji ya amsa wa matarsa bisa ga halayenta ba, ba kuma za a buƙaci mata ta amsa bisa ga halayen mijinta ba. Kowane abokin zama zai amsa kai tsaye ga Ubangiji game da rawar da ya taka a gidan.

Ayyukan Uba

A wasikata ta baya, na nuna cewa uba shi ne ainihin "mai gina gida." Sai dai idan uba ya ɗauki matsayinsa, ya amince da haƙƙoƙinsa, ya kuma tsaya yadda Allah ya nufe shi da zama shugaban gidansa,to, shirin Allah na gidan ba zai yi aiki ba. Idan uba bai iya ba da shugabanci mai kyau a gida ba, gidan zai shiga rikici.

A dangantakarsa da Ikilisiya, Kristi yana rike da manyan muƙamai guda uku waɗanda Allah Uba ya wakilta masa su. Shi Firist ne, Annabi ne kuma Sarki (ko Gwamna) ne. A kowane gida, uba yana da dangantaka ta kurkusa da iyalinsa. Akwai manyan mukamai guda uku waɗanda Allah cikin ikonsa ya ba uba, waɗanda ba zai iya rabuwa da su a gaban Allah ba. Kowane uba a kowane zamani Allah ya kira shi don ya zama firist, annabi da kuma sarki na gidansa.

  • A matsayin firist, yana wakiltar iyalinsa a gaban Allah.
  • A matsayin annabi, yana yin akasin haka; a nan yana gabatar da Allah ga iyalinsa.
  • A matsayin sarki, yana mulkin iyalinsa a madadin Allah.

A matsayin firist, an kirayi uba ya yi roƙo ga Allah a madadin iyalinsa, yana kawo buƙatunsu ga Allah cikin addu'a, yana kuma neman kariyar Allah da albarkarsa a kansu. Wannan ba zai yiwu ba in ba tare da bangaskiya ba. Daya daga cikin ƙananan ayyukansa shi ne na yin bangaskiya a madadin iyalinsa.

A cikin Tsohon Alƙawari an bayyana wannan ta wajen bukin Idin Faska. A cikin kowane iyali, aikin uba ne ya yanka ɗan ragon haɗaya kuma ya yayyafa jininsa a saman ƙofa da kuma dogaran ƙofofin gidansa guda biyu (Fitowa 12:3–7). Ta wurin wannan aikin bangaskiya da biyayya, ya sami kariyar Allah ga dukan iyalinsa.

A cikin Sabon Alƙawari an kwatanta wannan ƙa’ida a cikin Markus 9:20–27, inda wani uba da aljani ke wahalsar da ɗansa ya zo wurin Yesu. Yana neman taimako saboda yaron, ya ce wa Yesu, "Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu." Nan da nan sai Yesu ya mayar da alhakin yaron a kan uban sai ya ce, "Ai dukan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya." ‘Yantarwar yaron ta dogara ne a kan bangaskiyar uban. Uban na da haƙƙi da kuma alhakin gaskatawa a madadin ‘ya’yansa.

Mutane sukan kawo mani ƙananan yara don ‘yantarwa, amma na koyi in tambaye su, "Ku ne iyayen yaron?" A wasu lokuta, sai ya zama 'yar uwa ce kawai ko maƙwabciyar kirki. A lokuta da yawa iyayen - musamman uban - ba a samun su. Ba ni da wani tushe a cikin Littafi Mai Tsarki na yin hidima ga yaro idan ba a kan tushen bangaskiyar daya ko dukan iyayen biyu ba.

Mutumin da yakan zama da wuya ya zo wurina neman taimako don yaro shi ne uban.Tsarin mu na gudanarwa gaba ɗaya ba daidai yake ba, sai mu dinga mamakin dalilin da ya sa Allah ba ya sa ma sa albarka. A yayin yin hidima ga yaro, babu wani mai wa'azin da zai iya maye gurbin uba.

Matsayi na biyu da Allah ya ba kowane uba shi ne na zama annabi—ya kamata ya wakilci Allah ga iyalinsa. Uba na yin wanan ko ya sani ko bai sani ba—ko kyakkyawan wakilci ne ko marar kyau. Mutane da yawa da suke hidimar ba da shawarwari ko kuma aiki da yara za su ba da shaida cewa dukan yara suna samun ainihin fahimtar Allah daga tushe ɗaya—ubannin su. Ba abin mamaki ba ne da yawa daga cikin matasan mu ba su damu da Allah ba ko kuma ba ruwan su da shi?

Matsayi na uku na Uba shi ne na zama sarki. A matsayin sarki, ana buƙatar uba ya mulki iyalinsa a madadin Allah. A cikin bayyana cancantar shugaba a Ikkilisiya, Bulus ya bayyana cewa “lalle ne ya sarrafa iyalinsa da kyau” (1 Timoti 3:4). Kalmar nan ta mulki, tana nuna iko irin na gwamnati. Akwai alaƙa ta kai tsaye tsakanin shugabanci a gida da shugabanci a Ikkilisiya. Gida shi ne filin gwaji na rayuwa da hidimar kowane namiji.

Bari mu dubi wani sassaukan bayani, na gaskiya: Idan addinin mu ba ya aiki a gida, to, ba ya aiki—shike nan! Ina rokon ku, kada mu kai wa duniya abin da ba ya aiki a gida! Duniya tana cike da rigingimu da rashin jituwa. Ba ta buƙatar ƙari!

Babban tashin hankali a cikin gidaje a Amurka shi ne namijin da ya canja akida. Ya yiwu wasu maza su ji cewa kalmar nan "canja akida" ta yi ƙarfi sosai— kamar ma cin mutunci. Duk da haka, na more ta a shawarce. Mai canja akida shi ne wanda ya canja matsayinsa, kuma yawancin mazan Amurka sun canja ainihin nawayoyinsu guda uku—a matsayin mazajen aure, ubanni da shugabanni na ruhaniya. Hakan ya bar mu da uwaye mata da suke gudanar da komai a cikin al’umma.

Bari in tambaye ku: Wanene, idan akwai, wanda yakan yi addu’a tare da yara a lokacin kwanciya? Wa ke shirya su don tafiya sundi sukul? Wa ke karanta musu labaran Littafi Mai Tsarki? Wanene mai yin addu’a idan yaro ba shi da lafiya? Mafi yawancin lokuta, uwa ce. Ya kamata uwa ta sa hannu cikin girman ruhaniyar yaro, amma uban shi ne Allah ya kira don ya zama masomi da mai jagorantar rayuwar iyalinsa ta ruhaniya.

Sa’ad da yaro ya lalace, muna son mu dora wa Ikkilisiya laifi... al'umma... makarantu—kowa da kowa amma ban da mutumin da ya fi cancantar laifin—wanda shi ne uban. Yawancin yara suna ganin cewa Ikkilisiya da abubuwan Allah "raunana" ne saboda suna ganin uwayen su ne kawai ake damawa da su. Johnny karami ya girma yana fada wa kansa, "Ina so in zama kamar Baba." Cikin zama kamar Baba " ya yanke shawarar barin abubuwan Allah ga "masu rauni" (1 Bitrus 3:7).

Ana cikin tafiya, yayin da Johnny karami ya gaza a rayuwa—lokacin da ya bar makaranta ko kuma ya zama kangararre—ba Johnny ba ne ya gaza, amma mahaifin sa ne. Na iya gane cewa babu yara masu ƙin ji, sai dai manya masu ƙin ji. A zahiri ba yaran ne suka bar makaranta ba amma iyayensu ne— musamman kuma Ubannin su.

Abokina, bari in tambaye ka: Yaya za ka auna matsayinka na zama miji da kuma uba? Zai iya yiwuwa ka sami nasara a kasuwancin ka ko kuma ka zama sananne a kungiyoyin ƙasa -za ka iya zama shugaban banki, ko kuma ka ci wasan kwallon golf da ta ba abokanka mamaki - amma idan ka gaza a matsayin ka na zama miji da uba, to, a gaban Allah ka zama kasasshe.

2
Raba