Nasara wata sananniyar kalma ce a wayewar Ƙasashen Yammaci. Bisa ga yanayin da muka tashi a cikin da kuma tarbiya, a kodayaushe ana kalubalantar mu a kan neman nasara a cikin duk abin da muke yi—a ayyukan mu, a wasanni, a siyasa, a rayuwar mu. Wannan izawa ce da ta zarce misali. Amma nasara a wurin Allah, ana auna ta ne da ma'aunin da ya bambanta da namu. Allah ya ba ni wannan fahimta a hanya ta musamman. Na taɓa jin wani abokin hidima ya ba da ma’anar gwani a matsayin "mutum wanda ya bar gida da ‘yar jakar aiki a hannu." Tunda ina yin tafiye tafiye sosai, kuma koyaushe ina ɗauke da ‘yar jakar aiki a hannu na, bisa ga wannan ma'aunin, ni gwani ne.

Amma, a yayin da nake tunani a kan wannan wata rana, Ubangiji ya yi magana da ruhuna ya ce, "Za ka iya yin tafiya ko'ina a duniya da ‘yar jakar aikin ka a hannu, ka kuma yi wa dubban mutane wa’azi, ka sa su tattaru a gaban bagadi, amma idan gidan ka ba shi da lafiya— to, a idona, kai kasasshe ne." Da shike ina da marmari sosai in zama da nasara a wurin Allah, sai na sa wannan a zuciya ta. Sakamakon haka, sai na sami sabuwar fahimtar rayuwar gida da nawayar iyaye.

"Ina Rubuta Muku, Ubanni”

Cikin 1 Yahaya 2:13, manzon ya ce, "Ina rubuta muku, Ubanni...” Bari ni ma in maimaita haka. Bari in yi magana da kowannen ku da yake Uba kai tsaye: Za ka iya yin nasara a kowane bangare na rayuwa, amma idan ka kasa a matsayin Uba, to, a gaban Allah kai kasasshe ne a rayuwa.

A cikin Afisawa 6:4, Bulus ya taƙaita ainihin nawayar Ubanni a cikin aya daya:

"Ku ubanni, kada ku sa ‘ya’yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji."

A cikin Kolosiyawa 3:21 Bulus ya maimaita gargadin nan na farko. “Ku Ubanni, kada ku ƙuntata wa ‘ya’yan ku,” ya ƙara, “domin kada su karai”. Hakika, Uwaye mata dama su ne masu kulawa da kuma horar da yara. Ammai dai babban aikin ya rataya ne a wuyan Ubanni.

Uba na da haƙƙoƙi guda biyu ga yaran sa: na farko, yin sadarwa; na biyu, ilmantarwa. Wannan tsarin na da muhimmanci. Idan hanyoyin sadarwa tsakanin Uba da yara ba a bar su a bude ba, to, Uba zai ji takaici a aikinsa na ilmantarwar. Bayar da umarni daga Uba kawai bai isa ba. Dole ne yaron ya kasance da niyyar karɓar koyarwar Uban.

Don a ci gaba da samun sadarwa, dole ne Uba ya kiyaye kada a sami saɓanin ɗabi’u biyu a tsakanin ‘ya’yansa: tawaye a gefe ɗaya, da kuma karayar zuciya a wani gefen. Saboda haka, dole ne ya ba da lokaci da kulawa ga kowane yaro. Dole ne ya gina kowane yaro a daidai yadda yake bisa ga halittarsa. Babu yara biyu a cikin iyali da suke iri daya. Horon da zai taimaki ɗaya zai iya zama lahani ga ɗayan. Wani yaron zai iya karɓar gyara, amma a wata fuskar wannan na iya sa wani ya yi tawaye.

A lokutan da na ke ba manya shawarwari, sai na gano cewa yawancin matsalolin su sun samo asali ne daga wani yanayi inda Uba— a cikin fushi, rashin adalci ko kuma rashin kulawa—ya harzuƙa ɗansa.

Gida Ne Cibiya

Ba Sabon Alƙawari ne kaɗai ya dora wa Ubanni wadannan nawayoyin ba. Ƙa'idar duk iri ɗaya ce a cikin Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya. Kamar dai a kowane lokaci, Allah ya nufi cewa rayuwar ruhaniyar mutanen sa ta sami tushe daga gidajen su. Kubawar Shari'a 11:18–21, ta yi mana magana kai tsaye game da wannan a matsayin mu na iyaye:

“Sai ku rike zantattukan nan nawa a zuciyar ku da ranku... Za ku koya wa ‘ya’yanku su, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, da sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. Za ku rubuta su a madogaran ƙofofin gidajen ku da bisa ƙofofinku, don kwanakinku da kwanakin ‘ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su, kamar kwanakin sama a bisa duniya.”

A matsayin iyaye, Allah ya ɗora mana nawayar koyar da maganar Sa da hanyoyin sa ga ‘ya’yan mu a gida. Ba za a iya canza wannan aiki zuwa ga wata ma’aikatar addini ta musamma ba—haikali, Ikkilisiya ko Sandi sikul. Kuma ba za a iya ɗora nauyin ga wasu ƙwararrun malamai ba—firistoci, masu wa'azi ko malaman Sandi sikul. A matsayin mu na iyaye, dole ne mu koya wa ‘ya’yanmu maganar Allah da tafarkun sa a gida.

Wannan ba zancen a kafa "bagadin addu’a na iyali" ba ne kawai ko kuma gudanar da "addu’ar tare" ba. Domin ya zama da tasiri, dole ne a ci gaba da yin koyarwa da horarwa ta ruhaniya. Allah ya ce, "A lokacin da kake kwanciya da kuma lokacin da ka tashi." Wannan ya ƙunshi dukan sa'oin da muke a farke. Aikin mu ne mu sa koyarwar maganar Allah a cikin dukan ayyukan mu na yau da kullum na rayuwar iyali.

Marigayi Dr. V. Raymond Edman, shugaban Kwalejin Wheaton a wani lokaci can baya, ya taɓa rubutawa: "Idan na waiwayi yadda na reni ‘ya’yana, idan da zan sake maimaitawa, zan ɗauki lokaci sosai tare da su a wasu ƙananan ayyukan da ba na addini ba." Ya gano cewa abubuwan da ‘ya’yan suka fi tunawa da su lokacin da suka girma su ne lokutan da ake tare kawai. Yin sadarwa ta ainihi da yaro ba ta samuwa a cikin mintuna biyar. Sau da yawa, abubuwan da suka fi muhimmanci ana koya wa yaro ne a lokacin da ba a sa ran yin haka ba - a cikin wasa ko lokacin da ba a shirya ba. Idan babu irin wannan hulɗar, ba za a taɓa faɗin waɗannan abubuwan ba.

Jin Daɗi Na Sama a Duniya

Lokacin da nake yin binbini a kan ayar nan ta Maimaitawar Shari’a 11:18-21 a cikin fassarar ‘King James’, an jawo hankali na ga kalmomin karshe; “kamar kwanakin sama bisa duniya.” Mukan ji mutane suna magana sosai a kan “Jin daɗi na Sama a duniya,” amma ina fada maku ban san cewa waɗannan kalmomin daga Littafi Mai Tsarki a ka ɗauko su ba. Na ƙara cika da mamaki da na gane cewa an mori wannan a kan rayuwar gida na mutanen Allah. Gidajen Krista nawa ne a yau za a iya cewa lallai gidan su ‘jin daɗi na sama ne a duniya’?

Duk da haka wannan shi ne ainihin nufin Allah. Yana son kowane gida ya zama mai wakiltar yadda sama take a nan duniya, mai maimaita dangantakar ƙauna ta har abada da ke cikin Allahntaka—Uba, Ɗa da Ruhu Mai Tsarki.

Sau da dama mukan yi zaton cewa rayuwar gida na farawa ne da ɗan adam, amma ba haka ba ne. A cikin Yahaya 14:2, Yesu ya ce, "A gidan Ubana akwai wurin zama da yawa."Ma’anar Gida a Littafi Mai Tsarki na da zurfi fiye da ginin da a ke gani a zahiri; ana morar sa don nuna iyali gaba daya a ƙarƙashin shugabancin Uba. Ba wai mutane kima kawai da ke zaune tare a karkashin rufi ɗaya ba. Allah na da ma'ana da ta fi haka, wanda ke haɗe tare a cikin Allahntaka.

Zama Uba, Yin Shugabanci, Zumunta

Dangantakar da ke tsakanin Uba da Ɗa da Ruhu Mai Tsarki a sama ta ƙut da ƙut ce, tana ƙunshe da ɓangarori uku marar matuƙa. Waɗannan sune ɓangarori uku da Allah yake so su kasance a cikin gidajen mu a nan duniya.

Na farko shine Zama Uba

‍Allah Uba, shi Uban Ubangijinmu Yesu Kristi ne tun fil azal, Kristi kuma ya kasance Ɗansa tun fil azal. A cikin Afisawa 3:14–15 Bulus ya ce: "Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda yake sa wa kowace ƙabila ta Sama da ta Ƙasa suna."

Kalmar Girkanci da aka fassara ta "iyali" a nan ita ce patria, wadda aka samo kai tsaye daga pater, ma’ana "Uba." Sabon juyin ‘King James’ ya ce "iyali," amma fassarar J. B. Phillips ta juya shi a matsayin "zama Uba," wanda ita ce fassarar da ta fi dacewa da ta Girkanci. Wannan ayar ba kawai tana nuna mana Allah shi ne Uban Kristi ba, har ma da matsayin zama Uba a duk duniya ya samo asali ne, an kuma kafa shi bisa wannan tsari na matsayin da Allah Uba yake rike da shi a cikin Allahntaka. Dukan wani zama Uba hoto ne mai nuna matsayin Allah Uba.

Ɓangare na biyu na madawwamiyar dangantaka a cikin Allahntaka shine yin shugabanci

‍Cikin 1 Korintiyawa 11:3 Bulus ya ce, "Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum [ma'ana namiji] shi ne Almasihu, shugaban kowace mace kuwa [mata] mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne." A cikin tsari na duniya, mun fahimci cewa shugabancin Uban a bisa Kristi na har abada ne—haka yake a koyaushe.

Ɓangare na uku na dawwamammiyar dangantaka a cikin Allahntaka shine Zumunci

‍Cikin Yahaya 1:1, mun gane cewa Almasihu (Kalmar) an bayyana shi a matsayin wanda ya kasance tun fil azal "tare da [ pros a Girkanci] Allah [Uban]." Kalmar Girkancin tana nufin "zuwa ga" ko "fuska da fuska da." Yahaya 1:18 ta fada mana cewa Almasihu yana "a ƙirjin Uban." Wannan yana nunawa da kyau ƙauna da matukar jin daɗin juna da ke tsakanin Uban da Ɗan, wanda Ruhu Mai Tsarki yake ci gaba da tabbatarwa a kullum. Hakika, wani ya bayyana Ruhu Mai Tsarki a matsayin "dangantakar ƙauna tsakanin Uba da Ɗan."

Ta wurin Bishara, da kuma ta wurin Ruhu Mai Tsarki, Allah yana son ya nuna wannan zumunci na Allahntaka a cikin rayuwarmu a duniya—kuma, musamman, a cikin gidajen mu. Cikin 1 Yahaya 1:3, manzo ya gabatar mana da gayyatar da Allah ya yi mana na samun zumuncin har abada na sama:

“To, shi wannan da muka ji muka kuma gani shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.”

Mun gani, kenan, cewa Allah ya tanadar da kamanni na yadda gida ya kamata ya zama, kuma a cikin wannan kamannin akwai manyan ɓangarori uku na dangantaka: Zama Uba, Yin shugabanci da zumunta. Idan gidajen mu na duniya za su cika manufar Allah su kuma zama da nasara, dole ne su kasanace da waɗannan dangantaka guda uku.

A cikin al’ummar mu ana duban mace a matsayin "mai gina gida." Duk da haka, wannan zai iya zama gaskiya amma ba lallai ba. Bisa ga tsarin Allah, namiji shi ne ainihin mai gina gida—domin shi ne zai sa gidan ya zama abinda ya kamata ya zama. Uba shi ne makasudin kafa gida. A bisa kafaɗun sa ne Allah ya sanya dukan nawaya da ikon kafa gida da zai cika shirin Uban mu na sama mai ƙauna. Lokacin da namiji ya ɗauki matsayinsa da ya dace da shi, to, daga nan ne matar za ta ɗauki nata matsayin a gefensa na "mataimakiya" (Farawa 2:20).

Jerin Matakai na Iko

Za mu iya fara ganin dangantakar miji da mata tana da muhimmanci wadda ta wuce kowane lokaci, saboda ita ce hoton madawwamiyar dangantaka da ke tsakanin Uba da Kristi. Idan muka koma ga 1 Korintiyawa 11:3, za mu gane cewa akwai tabbataccen matakin iko da ya samo asali daga Allahntaka ya kuma isar da shi cikin gida. Allah shi ne shugaban Kristi, Kristi shi ne shugaban namiji, namiji kuma shi ne shugaban mace ko mata. Dukan Ikon na fitowa ne daga wurin Uba kuma yana kasancewa a wurin da ya kamata a cikin jerin da ke komawa gare shi. Kristi na da iko saboda ya miƙa kai ga Uba; Miji na da iko saboda ya miƙa kai ga Kristi; mata na da iko saboda ta miƙa kai ga miji.

Wani Jarumin Roma mai hikima yana da marar lafiya sai ya zo wurin Yesu yana neman a warkar da bawan wanda ba shi da lafiya. Da shike ya kula da rayuwa da kuma mu'ujizan Yesu, ya gabatar da kansa da cewa, "Don ni ma a ƙarƙashin wani nake, da kuma soja a ƙarƙashi na, " (Luka 7:8). Bai fadi matsayinsa kamar yadda wasunmu za su yi ba, "Ni mai Iko ne!" A'a, ya gane cewa ikon da yake da shi a bisa sojojin da suke ƙarƙashinsa ya danganta ne akan cewa shi ma yana ƙarƙashin wani iko. A matsayinsa na sojan Roma, ya zama mahaɗi a matakin iko da ya koma ga Sarkin kan sa. Saboda haka, duk wanda ya ƙi yin biyayya da umarnin shugaban sojoji, a zahiri, yana ƙin biyayya ga ikon sarki ne.

A lokacin da yake gabatar da kansa ga Yesu, Jarumin ya ce, "Don ni ma a ƙarƙashin wani nake”." Me ya sa ya mori kalmar "ni ma"? Saboda yana kwatanta kansa da Yesu. Ya gane cewa irin ƙa’idojin da ake amfani da su a sashin bada umarni a aikin soja su ne ke aiki ta fuskar ruhaniya a hidimar Yesu. Yesu, kuma, "mutum ne da ke ƙarƙashin iko." Kamar yadda ikon jarumin ya dogara ga dangantakarsa da sarki, haka kuma ikon Yesu ya dogara ga cikakkiyar biyayyarsa ga Uba. A kowane sashi, ka’idar duk daya ce: domin samun iko, dole ne mu kasance a ƙarƙashin iko.

5
Raba