A cikin shekaru daga 1950 (danganin farkon hidimata) na yi rikon wata Ekilisia a London, Ingila. A lokacin, a kai a kai muna samun masu tuba, da masu samun warkaswa da baftisma a cikin Ruhu Mai Tsarki. Duk da haka, a cikin waɗannan albarkun, ina da matsala ta samun bakin ciki mai sauko mini akai akai, kamar gajimare mai duhu, da nauyi. Lokacin da duk wannan gajimare ya rataye ni, sai in nuna wannan matsin lamba ga mutanen da ke kusa da ni - musamman iyali na.

Na yi gwagwarmaya da wannan ta kowace hanya a cikin ikona wanda na sani . Na yi addu'a, na yi azumi, na yanke shawarwari na rayuwa. Na yi sammakon tashi don yin addu’a. Na yi jinkirin barchi don yin addu'a. Na yi duk abin da na sani amma ban sami sauki ba. Asali ma idan na yi addu’a da azumi, sai ya tsananta. Wata rana na kai ƙarshen iyaka ta sa’ad da wani furci a Ishaya 61:3 – “ mayafi na yabo maimakon ruhu na nauyi” ya ɗauki hankalina.

Nan take sai na gane cewa da wani ruhu ne nake fama da shi - wanda ya karance ni, ya san kasawa ta, ya san yadda zai kai mani hari da kuma lokacin da zai kawo harin. Sai na gane fama ta ba tunani yayi min yawa ba. Sai na fahimci dalilin da ya sa matsin ke kara tsanani in nayi yunkurin bauta wa Ubangiji: domin aikin wannan ruhu shi ne ya hana ni hidima ga Allah. Wannan ruhun ya san lokutta da zai matsa mani..

Gane ainihin maƙiyina babban ci gaba ne. Na bincika Nassosi kuma na sami ayar da na yi imani za ta kawo mini maganin matsala ta. Joel 2:32 ta ce:

“Za ya zama kuwa, duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji, za ya tsira.”

Na haɗa Ishaya 61:3 da Joel 2:32 kuma na yi addu’a ta musamman: “ Ya Allah, cikin sunan Ubangiji Yesu Kristi – bisa ga maganarka, ina roƙonka ka cece ni daga wannan ruhun na bacin rai." Kuma lokacin da na yi wannan addu'ar ta musamman, addu'a da nassi, na samu yanchi. Wannan matsin duk sai ya ficce.

Daga baya na koyi cewa samun yanchi shine mataki na daya, mataki na biyu shine yadda zan dawwama a cikin yanchin. Allah ya fara nuna mani cewa ya ‘yantar da tunani na daga wannan matsi na aljanu, amma yanzu ya rage gareni in sake tarbiyyar da hankalina – in samu ra’ayi da tunani daban. Abin da ban iya yi ba kafin in samu kubuta.

Bayan samun kubuta, yanzu hakki na ne in yi wannan.

Sagala Kwalkwali

A cikin wannan yaƙi na kiyaye kuɓuta ta daga baƙin ciki, na fahimci cewa sashen da ya fi matsala a rayuwata fiye da sauran shine sashen tunani na. Shaidan ya ci gaba da kai mani hari a cikin tunani na. Ni mutum ne wanda ya sami ingantaccen ilimin sosai a rayuwa. Sai Na gane cewa hankalin mutum mai ilimi yana da wani rauni da shaidan yake amfani dashi ya kawo hari. Da zarar ka dogara ga zurfin ilimin ka da tunanin ka, haka nan Shaidan zai yi amfani da shi a kanka.

Na koyi cewa ya rage gare ni na koya wa hankalina da tunanina cewa su bayi a gare ni ba uban gida na ba. Sa’ad da na ga cewa ina bukatar kāriya ga tunani na, na tuna cewa a cikin Afisawa 6:14–18 akwai kayan aiki guda shidda—ɗamarar gaskiya, sulke na adalci, takalma na shirin kai bisharar salama. , garkuwar bangaskiya, da kwalkwali na ceto da kuma takobin Ruhu—waɗannan makamai suna da tasiri ta wurin makamin addu’a.

Yayin da nake nazarin wannan jerin , na lura da abu guda daya daga cikin kayan aikin da aka tsara don kare tunani: wato kwalkwalin ceto. Kwalkwali yana rufe kai, wanda yawanci yana da alaƙa da bangaren tunani. Na ga cewa Allah ya riga ya yi mani tanadin kariya ga tunani na.

Na san ina da ceto. Amma na yi tunanin ko hakan yana nufin cewa ina da kwalkwalin ceto kai tsaye. Ko kuwa abin ya wuce haka? A cikin Littafi Mai-Tsarki, makamantun ayoyin ga Afisawa 6:17 ita ce 1 Tassalunikawa 5:8, wadda ta ce:

“Amma da ya ke mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna sa zuciya ga samun ceto, ita ce kuma kwalkwalin mu.”

An kira kwalkwalin begen ceto. Bege. Na gane cewa ban maida hankali sosai ga tunani ko nazari akan matsayin bege a rayuwar mai bi ba. Ruhu Mai Tsarki ya bishe ni daga Littafi zuwa Littafi na Sabon Alkawari yana nuna mani cewa rayuwa ta, ta ruhaniya ta sami rashin daidaita da kuma kasawa saboda rashim fahimtar matsayin bege a rayuwa ta. Samun kyakkyawar fahimtar matsayin bege wajen kare tunani na, na da muhimmanci ainun.

A cikin 1 Korinthiyawa 13:13, Bulus ya ce:

“Yanzu kuwa bangaskiya, bege, ƙauna, sun tabbata, su uku...”

A cikin mahallin babin, a bayyane yake cewa abubuwan nan uku su ne ci gaban (dauwama) tabbatattun abubuwan ruhaniya da ke kasancewa a cikin rayuwar Kirista. In ji Bulus Wasu abubuwa, na ɗan lokaci ne. Suna da manufa, kuma idan manufarsu ta cika ba za a ƙara buƙatar su ba. Amma ya ce tabbatattu guda uku na gogewar ruhaniya sune bangaskiya, bege, da ƙauna.

Na ƙara yin nazari kuma na koyi cewa akwai bambanci a nassi tsakanin bangaskiya da bege. Suna samuwa a wurare daban-daban na halayen ɗan adam. Bangaskiyar Littafi Mai-Tsarki tana da alaƙa da faruwa a halin yanzu, daga duniyar zuciya. Bege yana da alaƙa da nan gaba, wato daga fagen tunani.

Kwalkwalin bege shi ke kare tunanin mai bi. Don haka, na gaskanta dole ne kowane Kirista ya kasance mai kyakkyawar sa zuciya. Idan Kirista ya zama marar bege - a zahiri - yayi musun bangaskiyarsa ne. Bege yana ba da kyakkyawar fata.

Tunani na - wanda ruhun nauyi ya danne - yanzu ya sami 'yanci. Kuma Allah ya nuna ma ni na sami yanci don in sake horar da tunani na. Ba shi zai horar da ni ba. Wannan hakki nawa ne. Dole ne in dasa ra'ayi daban da na da - hali daban, yanayin tunani daban. Romawa 8:28 na ɗaya daga cikin ayoyi da yawa da ke goyan bayan imanina cewa kowane mai bi, ya zama mai kyakkyawan fata:

“Mun sani cewa dukan al’amurra suna aikatawa zuwa alheri ga waɗanda ke ƙaunar Allah, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.”

Idan ka na ƙaunar Allah kuma ka na neman tafiya cikin nufin sa da gaske, to, dukan abubuwa za su zama alheri a gare ka. Kuma idan dukan abubuwa suna zama alheri, ai babu dalilin zaton mugun abu ko bakar fata.. Kowane yanayi, lokaci ne na kyakkyawan fata. Sirrin shine, mu horar da tunanin mu ya rungumi wannan gaskiyar kuma mu yi rayuwa a cikin ta.

Shaidar Nassi

Bege yana ɗaya daga cikin jigogi masu kyau a cikin Littafi Mai Tsarki. Romawa 4:18 tana gaya mana game da Ibrahim sa’ad da ya karɓi alkawarin Allah game da haihuwar ɗansa, Ishaku, wannan ya kasance bayan lokacin sa zuciyar samun yaya ya riga ya wuce.

“Sabanin bege [ya] yi imani da bege.”

Ibrahim ya gaskata kuma, a sakamakon haka, ya sa zuciya. Gaskatawa shine farko. Sa zuciya ya kasance mataki na biyu - ko kuma sakamakon bangaskiya. Kuma Ibraniyawa 11:1 ta kara bayyanawa:

“Yanzu bangaskiya ita ce hakkakewar abubuwan da ake bege...”

Bangaskiya ita ce tushen tabbaci wanda bege ke goyan bayansa. Bangaskiya tana haifar da bege. Dukansu biyu sun halalta, amma dole ne mu same su a wurin da ya dace—an tsara su don yin tafiya tare. .

Ba za ka iya rayuwa ba tare da bege ba. A cikin Romawa 15:13, Bulus ya ce:

“ Allah mai kawo sa zuciya ya cika ku da matukar farin ciki da salama cikin bada gaskiya, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.”

Allahnmu, shine Allah na salama, da farin ciki, da adalci. kuma shine Allah mai iko duka. Bugu da kari Shi ne kuma Allah na bege. To, idan ka cika da farin ciki da salama ta wurin badagaskiya (imani), sakamakon zai zama cewa za ka cika da bege.

Akasin haka, a cikin Afisawa 2:12 Bulus ya ba da kwatancin waɗanda ba su da bege:

“...A lokacin nan, a rabe ku ke da Almasihu, kuna bare daga jama’ar Isra’ila, baƙi kuma ga alkawuran da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya.”

Bulus ya ce batattu ba su da abubuwa uku: ba su tare da Kristi, ba su da Allah, ba su da bege. Lokacin da ba ku da bege, ba ku da Almasihu kuma ba tare da Allah. Bege na da babban mahimanci a cikin cetonmu.

A cikin Kolosiyawa 1:27, a lokacin da yake magana game da asirin bishara da ya wuce ganewa, Bulus ya rubuta game da masu bi:

“Wandanda Allah ya nufa ya sanarshe su ko minene wadatar darajar asirin nan... watau Kristi a cikin ku, begen daraja ke nan.”

Dukan bisharar ta kasance cikin wannan babban wahayi mai ban al'ajabi wanda aka ɓoye daga dukan annabawa da masu hikima da manyan mutane na zamanin dā. Kuma abin ban mamaki shi ne cewa yanzu an bayyana wannan asiri ga masu bi masu tawali’u kamar ku da ni: cewa Kristi yana cikinmu da gaske, kuma Kristi a cikinmu shi ne ainihin begen ɗaukaka.

Daukakar tana a gaba. Wanda ke da Kristi a cikin sa yana da begen gobe - bege na madawwamiyar daukaka tare da Allah Maɗaukaki. Abin da kuke da shi ke nan lokacin da kuke da Kristi a cikin ku.

A cikin Ibraniyawa 6:18–20, marubucin ya nanata babban tushe da muke da shi na bangaskiyarmu ga Kristi:

“...domin bisa ga abu biyu da basu sakewa, inda ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu mu sami abin karfafawar zuciya mai ƙarfi, mu da muka gudu neman mafaka domin mu kama begen da aka sanya a gabanmu. Wanda muke da shi kamar anchor na rai, tabbatachen bege, mai tsayawa, mai shiga kuma cikin abinda ke daga cikin labulen, inda yesu kamar shugaba ya shiga dominmu, da ya rigaya ya zama Babban Firist har abada, bisa ga tsarin Malkisadik.

Begenmu ginshiƙi ne na ruhu, tsayayye kuma tabbatacce. Anka ne wanda a zahiri ke zarcewa daga yanzu zuwa har abada kuma yana rike a cikin labulen, a cikin Ubangijin Zamanai—Yesu Kristi, Babban Firist ɗinmu kuma shugaban mu.

Jirgin ruwa yana buƙatar anka domin yana shawagi ne a kan ruwan da ba tsaye suke wuri daya ba. Ana jefa anka daga cikin jirgin, ta hanyar ruwan, zuwa cikin barga na dutse. Sa'an nan kuma a daidaita kuma a tabbatar da shi. Lokacin da ka wuce anka ta cikin ruwa (lokaci) zuwa cikin dutsen (dauwama), za ka iya zama babbar kariya.

Lokacin da kuka saka kanku a cikin dangantakarku da Yesu, kuna jefa anka cikin Dutsen Zamani. Kuma duk guguwa da babban iska da ke kadawa ba za su taba raba ku daga wannan Dutsen ba. Hanyar da muke shigar da ita ita ce ta bege.

Koyarwar Niyya

Ya rage namu mu horar da tunaninmu zuwa ga bege. A rayuwata, bambancin ya kasance kamar dare da rana. Bai zo cikin mintuna biyar ba, ko da yake; ya dauki fiye da shekaru biyar. Amma wannan horar da tunani na ya kawo mani babban sakamako.

Ceto zai ba ku kyauta don yin rabonku. Amma alhakin ku ne ku yi gwagwarmaya don kubutar da tunaninku. Kuma da yawa daga cikinmu (idan ba yawancin mu ba), hankali shine abin da ya fi rauni.

Ɗauki kwalkwali na ceto - kwalkwali na bege. Saka shi. Rufe tunanin ka. Kare tunaninka; Ka mai da su a karkashin iko da kuma daidai da Kalmar Allah. Kuma ku sami sakamako mai kyau.

12
Raba