A cikin wasiƙar da ta gabata mun ga cewa tsoro na halitta, tsoron aljanu, tsoron masu addini, da tsoron mutum, tsoro ne iri huɗu waɗanda ba tsoron Ubangiji ba ne. Yanzu za mu yi la’akari da menene tsoron Ubangiji. Ana iya bayyana shi ta hanyoyi da yawa, kuma zamu dubi wadansu ma’anonin da aka bayar a cikin Nassi. Amma, a taƙaice, za mu iya cewa tsoron Ubangiji shine maida Ubangiji ya zama Allahnka. Hali ne na girmamawa, cikakkiyar sadaukarwa da mika wuya ga Allah.

A cikin Zabura da Misalai akwai abubuwa biyu da suka bayyana tsoron Ubangiji. Zabura 34:11 ta ce:

“Ku zo, ku yara, ku saurare ni; Zan koya muku tsoron Ubangiji."

A lura, tsoron Ubangiji dole ne a koyar da shi. Na gaskanta cewa Ruhu Mai Tsarki ne yake magana a cikin wannan Zabura yana cewa, “Bari in koya muku tsoron Ubangiji.” Misalai 1:28–29 ta ce:

“Sa'an nan za su kira ni, amma ba zan amsa ba; Za su neme ni da himma, amma ba za su same ni ba. Domin sun ƙi ilimi kuma ba su zaɓi tsoron Ubangiji ba.”

Ina so in nanata maku da cewa dole ne ka zabi tsoron Ubangiji a rayuwarka. Idan ba ka yi ba, akwai lokacin da za ka yi addu'a kuma Allah ba zai amsa ba; za ka neme shi, amma ba za ka same shi ba.

Yanzu bari mu dubi wasu wuraren da suke gaya mana abinda tsoron Ubangiji ke haifar wa. Misalai 1:7, 9:10, 15:33; Zabura 111:10 da Ayuba 28:28 duk sun danganta tsoron Ubangiji da hikima da ilimi. “Duba, tsoron Ubangiji, shi ne hikima; rabuwa da mugunta kuma shine fahimi” (Ayuba 28:28). Tsoron Ubangiji yana sa mu zama masu hikima.

Zabura 19:9 ta ce, “Tsoron Ubangiji da tsabta ya ke, yana dawwama har abada.” Tsoron Ubangiji mai dawwama ne,; yana dawwama har abada. Yana da tsabta kuma zai kiyaye ka cikin tsarki.

“Tsoron Ubangiji ya kan tsawonta kwanaki rai, amma shekarun miyagu za su gajarta.” (Misalai 10:27)

Wannan a fili yake: idan kana son rayuwa mai tsawo da farin ciki, ka kiyaye tsoron Ubangiji.

“Ta wurin jinkai da gaskiya ake yin kaffarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji kuma akan rabu da mugunta.” (Misalai 16:6)

Idan ka na da tsoron Ubangiji, za ka rabu da mugunta. Za ka guje ta.

“A cikin tsoron Ubangiji akwai sakankancewa mai ƙarfi [kamar yadda na faɗa a baya, idan kana tsoron Ubangiji, ba za ka ji tsoron wani abu ba a rayuwa], 'ya'yansa kuma za su sami mafaka [wurin samun tsari na da sharadi: Allah yana kiyaye masu tsoron sa]. Tsoron Ubangiji maɓulɓular rai ne, da za a rabu da tarkunan mutuwa.” ( Misalai 14:26–27 )

A nan an lissafta albarku guda huɗu: amincewa mai karfi, wurin mafaka, maɓulɓular rai, da kubuta daga tarkon mutuwa.

“Ladar tawali’u da tsoron Ubangiji dukiya ne, da girma, da rai” (Misalai 22:4)

Ga Ƙarin albarku guda uku a nan: dukiya, daraja da rayuwa!

A ƙarshe, ban tsammanin akwai wasu alkawura masu girma fiye da waɗanda aka bayar a cikin Misalai 19:23:

“Tsoron Ubangiji mai-kawo rai ne, wanda yake da shi kuma zai zamna da rai a kwanche. Masifa ba za ta ziyarche shi ba.”

Ban san abinda za ka nema da ya fiye ma wannan ba - wato ka zamna da rai a kwanche kuma kada a ziyarce ka da mugunta!

Rayuwa Cikin Tsoron Ubangiji

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ana bukatar tsoron Ubangiji ga waɗanda suke mulki bisa wasu. “Allah na Isra’ila ya ce... ‘Wanda yake mulkin mutane a cikin adalci, mai yin mulki cikin tsoron Allah.” (2 Samu’ila 23:3).

Akwai bukatu guda biyu don jagoranci na ruhaniya. Na farko son Ubangiji ne, na biyu kuma tsoron Allah. Sa’ad da Yesu ya kira Bitrus ya yi kiwon tumakinsa, ya ce, “Kana ƙaunata?” (Ka duba Yohanna 21:15–19.) Ya yi tambaya sau uku! Sa'an nan Ya ce: "Idan ka na sona, to, ka yi kiwon tumakina." Ƙaunar Ubangiji da ta mutanensa wajibi ne. Duk da haka, idan kana ƙoƙari ka yiwa mutane hidima saboda kana ƙaunarsu kawai, zaka iya samun kanka mawuyacin yanayi na kaunar mutumin da ke da wuyar sha’’ani. Kaunar ka zata kasa. Ƙaunar Ubangiji da kansa kaɗai za ta sa ka kasance da aminci a irin wannan yanayin.

Har ila yau, idan dalilinka na yin hidima shi ne ƙauna ga mutane kadai, daga ƙarshe za a jarabce ka da yin abinda mutane suke so ka yi, ba abinda Allah yake so ba. A wannan lokacin muna raba makiyayi da Maaikaci dan haya. Ma’’aikacin dan haya yana ba mutane abinda suke nema; amma makiyayi yana ba su abinda Allah ya ce a ba su. Tsoron Ubangiji ne kawai zai ba ka damar yin haka!

Bari mu dubi tsoron Ubangiji a cikin rayuwar Yesu da hidimar sa. Ishaya 11:1-2 ya ce game da Yesu: “Daga cikin tsutsugen Jesse tofo za ya fito, Reshe kuma daga cikin sauyoyin sa. Ruhun Ubangiji zai zauna a bisansa, Ruhun ilimi da na ganewa, Ruhun shawara da iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji.” Bangare na ƙarshe na Ruhu Mai Tsarki shine Ruhun tsoron Ubangiji. Ya zauna bisa ga Yesu, makaɗaici na Uba. Idan da akwai abu ɗaya game da Yesu da ya bayyana a sarari, shi ne ya yi tafiya cikin tsoron Allah. Ya ce game da Ubansa, “Kullum ina aika abin da ya gamshe ka” (Yohanna 8:29). “Ni bisa ga kai na ban iya komai ba” (Yohanna 5:30). “Ɗan ba shi iya yin komi don kansa, sai abin da ya ga Uban yana yi.” (Yohanna 5:19).

Ishaya 11:3 ta ci gaba da cewa: Ruhun Ubangiji kuma “zai sa shi [Yesu] mai-hanzarin fahimta cikin tsoron Ubangiji.” Ruhu Mai Tsarki a bisan Yesu ya ba shi zuciya mai taushi na musamman ga bin nufin Ubangiji da hanyoyin sa. Idan akwai abu ɗaya da muke bukata a cikin ikilisiya a yau, shine sassauta zuciya ga bin nufin Allah da hanyoyin sa.

Ibraniyawa 5:7 tayi magana game da Yesu:

“Wanda a kwanakin jikinsa [bakuntar sa a duniya], sa’ad da ya miƙa addu’o’i da roƙe roke, da kuka mai zafi da hawaye ga wanda yake da ikon kuɓutar da shi daga mutuwa, aka kuwa ansa masa saboda tsoron sa mai-ibada…"

Allah ya ji addu’ar Yesu domin addu’o’i ne da suka fito daga zuciya mai tsoron Allah. Menene babban tabbacin cewa Yesu yana da wannan tsoron Uban? Na gaskanta cewa wannan nassi yana nuni ne da Getsamani . Wane abu ɗaya ne da Yesu ya faɗa a wurin da ya nuna tsoron Ubangiji? “Amma dai ba nawa nufi ba, naka za a yi” (Luka 22:42). Idan ka yi addu'a a haka, ana jin ka!

Mun kuma gane da cewa tsoron Ubangiji ya kasance a cikin Ikilisiyar farko.

“Sa'an nan ikilisiyoyin da ke cikin dukan Yahudiya, da Galili, da na Samariya suka sami salama, aka gina su. Suna tafiya cikin tsoron Ubangiji da ta’aziyyar Ruhu Mai Tsarki, suka yawaita.” (Ayyukan Manzanni 9:31)

Suna fuskantar abin da Zabura 2:11 ta ce: “Ku bauta wa Ubangiji da tsoro, ku yi farinciki tare da rawar jiki.” Kuna ganin mahadar? Ku yi murna, amma ku yi haka da tsoron Allah. Kada a raba abubuwan nan biyu,, domin yin haka, zai kawo rashin daidaituwa. Sa’ad da muka daidaita murna da rawar jiki—tsoron Ubangiji da ta’aziyyar Ruhu Mai Tsarki—to wannan zai gina ikilisiya.

1 Bitrus 1:17–18 na gaya mana dalilin da ya sa za mu ji tsoron Ubangiji:

“Idan kuma kuna kira bisa gareshi kamar Uba, shi wanda ya ke hukuntawa ba da tara ba, amma gwargwadon aikin kowane mutum, sai ku yi zaman bakontarku da tsoro; domin kun sani aka fanshe ku ba da abubuwa masu lalacewa ba, da su azurfa ko zinariya, daga cikin irin zaman ku na banza abin gado daga ubanninku, amma da jinin Kristi mai daraja.”

Waɗannan kalmomi ba zuwa ga marasa bi ba ne, amma zuwa ga Masubi—waɗanda aka fansa ta wurin jinin Kristi. Me ya sa mu (Masubi) ya kamata mu yi zama cikin tsoro? Saboda farashin da aka biya domin fansar mu. Allah ya sa jinin Dansa ya fanshe mu. Allah ya ba da Ɗansa domin a fanshe mu daga wautar mu, da jahilcin mu, da rashin biyayyarmu, da tawayenmu da girman kai.

Na gaskanta da cewa Allah Ruhu Mai Tsarki ya na shuka tsoron Ubangiji a cikin zukatanmu. Ban yarda da cewa muna da shi ba, sai Ruhu Mai Tsarki ya koya mana shi. Amma idan muka amsa, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, cikin tsoron Ubangiji, sai mu fara jin daɗin alherin Ubangiji. Ga kalamai guda uku game da alherin Ubangiji.

“Gama za ka albarkachi mai- adalchi; Ya Ubangiji, da tagomashi za ka kewaye shi kamar da garkuwa.” (Zabura 5:12)

Alherin Ubangiji kamar garkuwa ce da ke kewaye da kai, tana kāre ka ta kowane gefe. kana da cikakkiyar kariya a ƙarƙashin alherin Ubangiji.

Tagomashi wurin Ubangiji, a wata ma'ana, ana misalta shi da girgije na kasancewar Allah. Misalai 16:15 ta ce:

“A cikin hasken fuskar sarki akwai rai; alherin sa kuma kamar girgije ne na ruwan karshe.”

Saboda haka, idan ka sami tagomashin Allah a kanka, kana tafiya a ƙarƙashin ni’íma kamar girgije a lokacin ruwan karshe.

Misalai 19:12 ta ƙara gaya mana:

“Fushin sarki kamar rurin zaki ne; amma alherinsa kamar raɓa ne bisa ciyawa.”

Don haka, alherin Allah kamar girgije ne na ruwan karshe, kuma kamar raɓa ne a kan ciyawa. Ba za ka sami bushewa ta ruhaniya ba lokacin da kake tafiya ƙarƙashin ni’imar Allah!

Har ila yau, idan ka yi tafiya cikin ni’imar Ubangiji, za ka ɗauki girgije da raɓa tare da kai duk inda za ka je. Kana sanya albarka ga mutanen Allah. Menene zai iya zama babbar gata fiye da wannan?

Duk bawan Allah, mai tawali’u da ke tafiya cikin tsoron Ubangiji a ƙarƙashin girgijen tagomashin Allah “mai kawo albarka ne kamar ruwan sama.” Yana sanya albarka ga duk wanda ya yi hulɗa da shi kai tsaye. Akwai wani kamshi game da shi; Ni’’ima a cikinsa; wani abu da ya lullube shi wanda ke tare da shi duk inda ya je.

Har yanzu Allah yana bincike cikin duniya domin ya nemo waɗanda zukatansu ke cikakku gare shi—waɗanda suka mai da shi Allahnsu—waɗanda suka koyi tsoron Ubangiji. Lokacin da ya sami irin wannan mutumin zai nuna kansa mai ƙarfi a madadinsa, yana nuna tagomashin Allah a cikin rayuwar mutumin. Mu zabi zama irin wadannan mutane.

12
Raba