Zuciya Cikakkiya Ga Allah (Kashi Na 1)

Teaching Legacy Letter
*First Published: 2001
*Last Updated: December 2025
9 min read
“Gama idanun Ubangiji suna kai da komowa cikin dukan duniya, domin ya nuna kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyar su ta kamalta gareshi.” (2 Laba. 16:9 KJV)
Ruhun Ubangiji yana kaiwa da komowa ko'ina cikin duniya don wani irin mutum-wanda zuciyar sa ta kasance cikakka ga Allah. A duk lokacin da Ruhu Mai Tsarki ya sami irin wannan mutum, Allah yana jin daɗin nuna kansa mai ƙarfi a madadinsa, yana bayyana ikonsa da amincewarsa a cikin rayuwar mutumin da kuma hidimarsa. Yana jiran ya motsa a fili ko ya nuna iko da albarka a bayyane ta wurinsa.
Cikakkar Zuciya Ga Allah
Mutane biyu a cikin Littafi mai tsarki waɗanda aka ce suna da irin wannan zuciyar su ne Ibrahim da Ayuba. A cikin Farawa 17:1 mun sami wannan ƙalubale da aka yi wa Ibrahim: “Lokacin da Abram yake da shekara tasa’in da tara, Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce masa, Ni ne Allah Maɗaukaki; Ka yi tafiya a gabana, ka zama marasa aibu.’ Ibrahim ya yi tafiya tare da Allah har shekara ashirin da huɗu. kiran Allah ya zo wa Ibrahim yana da shekara saba'in da biyar. Amma yanzu ya kusanto ga kai ƙarshen girman sa na ruhaniya, wato, wurin da Allah zai cika, a hanya mai ɗaukaka da ban al’ajabi, alkawuran da ta wurin su ne ya fitar da Ibrahim daga Ur ta Kaldiyawa shekaru da yawa da suka shige. Ibrahim ya fuskanci sabon ƙalubale daga wurin Allah. Wato, Allah yana cewa, “Daga yau idanuna za su kasance a kan ka a hanya ta musamman. Zan sa ido ga duk wani motsi da kake yi. Zan ji kowace kalma da kake furtawa. Kuma ina bukatar duk abin da za kayi, ka yi cikin cikakkiyar biyayya, imani, da sadaukarwa gare ni.”
When Abram was ninety-nine years old, the Lord appeared to Abram and said to him, "I am Almighty God; walk before Me and be blameless [or perfect].” Abram had walked with God for twenty-four years; the call of God came to him when he was seventy-five years old. But now he was reaching the climax of his spiritual growth—that place where God was going to fulfill in a glorious and wonderful way the promises by which he had drawn Abram out of Ur of the Chaldees many years previously. Abram was confronted with a fresh challenge from God. In effect, God was saying, “From now on My eyes are going to be upon you in a very special way. I am going to watch every move you make. I am going to hear every word you speak. And I ask that everything you do be done in an attitude of perfect obedience, faith, and commitment toward Me.”
Ibrahim shi ne uban dukan waɗanda suka ba da gaskiya (dubi Romawa 4:11–12). Wato rayuwarsa da imaninsa abin koyi ne ga dukkan masubi. Na yi imani cewa abin da Allah yake bukata a kan kowannenmu yana cikin waɗannan kalmomi ga Ibrahim, “Ka yi tafiya a gabana, ka zama [cikakke] kuma zan yi alkawari tsakanina da kai, in riɓanya ka da yawa.”
Muna zuwa kuma muna tafiya cikin zamanin karshe, lokacin da Allah zai cika alkawalinsa akan zamani. Kuma sakon Allah ga duk wanda zai dauki mazauninsa a cikin abin da Allah yake aikatawa shi ne, “Ka yi tafiya a gabana, ka zama cikakke”.
A cikin littafin Ayuba mun ga wani mutum wanda zuciyar sa ta kasance kammalalla ga Allah. Abokan Ayuba ba su dauke shi da wani girma ba, amma menene abin da Ubangiji ya fadi game da Ayuba:
“Ka lura da bawana Ayuba, cewa babu kamarsa a duniya, kamilin [cikakken] mutum, adali, mai tsoron Allah, mai ƙin mugunta?” (Ayuba 1:8).
Don haka za mu iya cewa kamaltaka zuwa ga Allah ta kunshi tabbatacciyar dabi'a zuwa ga Allah da halin da ya dace zuwa ga mummunan ayukka. Babu tsaka-tsaka cikin kamala ga Allah. Ba a iya yin sulhu da abin da ba ya so. Dole ku himmantu ga yin biyayya - komai tsadar ta. Kuma a tuna, samun yardar Allah na da tsada!
Idan muka karanta littattafan Sarakuna da Tarihi, za mu ga cewa an fi tantance sarakuna ta hanyar sanin matsayin zuciyarsu a gaban Allah. Game da Asa, Yehoshafat, Hezekiya, da sauransu, an ce suna da cikakkiyar zuciya ga Allah. Amma babban misalin mutumin da zuciyar sa ta kasance cikakka ga Allah shi ne Dauda. Shi ne ma'aunin da ake tantance sauran sarakuna da shi.
Ku tuna cewa ba zuciya marar aibi muke magana ba, amma zuciyar da take cikakkiya ga Allah. Dauda ba ko yaushe ne ya kasance da ɗabi'a marar aibi ba. Kamar yadda ka sani, ya yi zina. Ko da yake Nassi bai yarda da zina ba, a nan yana magana ne, ba game da kamalar ɗabi'a ba; maimakon haka,, yana magana ne game da halin Dauda zuwa ga Allah.
A cikin Fitowa 20:1-3 mun sami buƙata ta farko don samun zuciyar da take cikakka ga Allah. ‘’ Allah kuwa ya faɗi waɗannan kalmomi duka, yana cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.” Kammala zuwa ga Allah yana nufin babu wani abin bautawa da shi, sai Shi. Ainihin zancen zuwa ga Dauda, da kowanne mu, shine “Wanene Allahnka?”
Wannan tambaya ta asali, "Wane ne Allahnku?" ita ce wadda Musa ya sake sawa a gaban Isra'ilawa a Kubawar Shari'a, kafin su shiga ƙasar alkawari. Amsar da suka ba shi ita ce ta zama makomar rayuwar su. Daga baya, sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko kan Isra’ila a hadayar Iliya a kan Dutsen Karmel, abin da kadai suke bukata su furta shi ne, “Ubangiji, shi ne Allah” (1 Sarakuna 18:39). Lokacin da za ka iya furta haka - Ko da yake kana da wasu matsaloli, ko kayi kuskure, ko ma ka aikata zunubi - amma za ka samu nasara.
Wannan ya kawo mu ga maƙasudin tantance kan mu dangane da wannan tambaya ta asali. Dole ne mu tambayi kanmu, “Ta yaya za mu san wanene Allahnmu?” A cikin Farawa sura 31, Yakubu, yana magana da Laban, ya ce, “Ka sauya ladar aiki na sau goma.” Amma Allah bai bar Laban ya zalumce shi ba. Ya ci gaba da cewa, “Da ba domin Allah na ubana, Allah na Ibrahim, da Tsoron Ishaku, yana tare da ni ba, hakika , da yanzu ka sallame ni hannu wofi” (aya 42). Ka lura da lafazin—“Allah na Ibrahim, da Tsoron Ishaku.” Yakubu ya yi amfani da kwatancin “Tsoron Ishaku” sa’ad da ya yi magana akan Allah na Ishaku. A zahiri, duk abin da ka ke jin tsoro, shine Allahnka!
Wasu suna maida cutar ciwon daji Allahnsu. Suna jin tsoron ciwon daji har suna tsoronsa fiye da tsoron Allah. Haka nan, mutanen da su ke shiga cikin maita, duba da sihiri suna shiga cikin tsananin bautar tsoro ga waɗannan ikokin shaidan har su zama Allahnsu. Ba na so in ji tsoron komai sai Allahn Ibrahim, da Ishaku da Yakubu! Idan da gaske mutum ya na jin tsoron Allah, to shi kadai ne abin jin tsoro a rayuwa.
Bayyana Tsoron Ubangiji
A cikin bayyana ma’anar tsoron Ubangiji ina so in fara nuni da Kashin tsoro guda hudu wadanda ba tsoron Ubangiji ba.
1. Tsoro na halitta
A wani yanayi, jin tsoro halin mutunkata ne. Alal misali, mutum yana tuƙi a kan babbar hanya sai taya ta fashe. Motar ta fice daga hanya zuwa wani rami. Amsa ce ta halitta mutun ya ji tsoro a cikin wannan yanayin. Ba tsoron Ubangiji ba ne, amma ba shi da illa. A gaskiya, irin wannan tsoro yana da kariya. Tsoro da jin zafi dabaru ne guda biyu da Allah ya sanya a cikin mutum domin ya kare shi. Idan ka sanya hannunka cikin ruwan zafi, zafin da kake ji zai sa ka janye shi. Idan babu jin ciwo, ruwan zafin za su kone hannunka . Don haka akwai jin zafi na halitta kuma akwai jin tsoro na halitta wadanda su ne hanyoyin kariya da Allah ya sa.
2. Tsoro daga shaidan
Timothawus ta biyu 1:7 ta ce, “Allah bai bamu ruhun tsorata ba.” An bayyana alamar wannan ruhu a cikin 1 Yohanna 4:18, “Tsoro ya ƙunshi azaba.” Ruhun tsoro na sa azaba; Tsoron Ubangiji ba ya azabtarwa.
3. Tsoro na addini
Irin wannan tsoro shi ne wanda mutum ke koyarwa. Ishaya 29:13 tace: “Saboda haka Ubangiji ya ce, “Tun da wannan jamaá suna gusowa kusa da ni da bakinsu, suna girmama ni da leɓunansu, amma sun nisantadda zukatansu daga gare ni , tsorona da suke ji kuma dokar mutane ce da an koya masu.” Na ji irin wannan tsoron na shekaru da yawa. Wani irin tsoro ne da aka san yawancin mu da muka girma a majami’a. Shi ne tsoron saba wa addini. An koya mana da cewa akwai dabiár da ta dace da majamiá, wata kuma ba haka ba. Alal misali, na yi shekaru da yawa ina tsammanin zunubi ne in yi tari ko yin magana da babbar murya ko nuna wani irin jin dadi a majamiá!
Wata siffa ta tsoron addini ita ce neman a tsare matsayin da ake da shi. Yesu ya tsauta wa shugabannin addini a zamaninsa domin sun ƙi su amince da abin da Allah yake yi a tsakaninsu. Sun ji tsoron sakamakon canji da zai zo a halayensu.
4. Tsoron mutum
Ana samun irin wannan tsoro a cikin Misalai 29:25. "Tsoron mutum yana kawo tarko, amma wanda ya sa dogarar sa ga Ubangiji zai zamna lafiya." Ka lura da bambanci: Idan kana tsoron mutum, ba ka dogara ga Ubangiji ba; Idan ka dogara ga Ubangiji, ba ka buƙatar ka ji tsoron mutum. “Tsoron mutum yana kawo tarko.”
Yawancin lokaci, masu waazi da hidima ikilisiya suna zuwa wurina suna cewa, “Ya ɗanʼuwa Prince, an yi mini baftisma cikin Ruhu Mai Tsarki. Har ma ina da baiwar Ruhu, amma ina cikin kangi.” Sai in amsa, “Wataƙila tsoron mutum ne! Kana jin tsoron abin da hukumar dattijai za ta ce; ko me shugugabanni za su yi tunani; abin da membobinku za su ce.” Bitrus ya ce, “Dole ne mu yi biyayya ga Allah fiye da mutane” (Ayyukan Manzanni 5:29). Inda akwai jayyaya tsakanin yin biyayya ga Allah da mutum, an riga an yanke mana shawara a cikin Kalmar Allah. Ba mu da wata matsala. A ganina, aƙalla kashi hamsin cikin ɗari na mutanen Allah a yau ba su da cikakken ’yanci domin har yanzu suna daure da kangin tsoron mutum.
Mun ga cewa tsoro na halitta, tsoron aljanu, tsoron addini, da tsoron mutum ire iren tsoro ne guda hudu wadanda ba tsoron Ubangiji ba ne. A wasiƙa ta gaba, za mu yi la’akari da mene ne tsoron Ubangiji.

*Free download
*This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.
Zazzage PDFLambar: TL-L030-100-HAU