Wuraren Karatu:

  • Littafin Ƙidaya 22-25
  • Littafin Ƙidaya 31

Da farko yana iya zama kamar labarin Bal'amu, mai sihiri, wanda aka rubuta a Littafin Ƙidaya 22-25 ba shi da wani amfani ga Krista a yau. Amma duk da haka,marubutan Sabon Alkawari sun yi magana kan Bal'amu a cikin ayoyi dabam-dabam har guda uku tare da gargaɗi a kowane lokaci. A bayyane yake cewa labarinsa yana ɗauke da darussa masu muhimmanci ga Krista.

Bal'amu wani murɗaɗɗen mutum ne kuma shu’umi - wani haɗi mai ban mamaki na baye-bayen ruhaniya na allahntaka da mugun hali. Musamman, muna ganin ƙungiyoyi a cikin Ikilisiya yau da irin wannan haɗaka ta baye-bayen ruhaniya da mugun hali.

Labarin Bal'amu ya fara da yadda Isra'ilawa suka kafa sansani a kan iyakar Kan'ana. Zamansu ya ba Balak tsoro, sarkin Mowab, wanda yankinsa ya yi iyaka da sansanin Isra’ilawa. Ya dubi Isra’ilawa a matsayin barazana ga mulkinsa, ko da yake ba su yi wani abin da ya zama dalilin razanarsa ba.

Yana jin ba zai iya tarar Isra’ila da yaƙi ba, Balak ya yanke shawarar yin amfani da makaman ruhohi a kansu. Ya aiki waɗansu ‘ya’yan sarki, da kuɗi domin a yi duba, su kira Bal'amu ya zo ya la'anci Isra'ila. A matsayinsa na “Mai Sihiri” (mai duba) Bal’amu ya yi suna a kan ikon furta albarka ko la’ana mai kawo nagarta ko mugunta.

Bal'amu ya zo daga Fetor cikin Mesofotamiya. Shi ba Ba’isra’ile ba ne. Duk da haka ya san Allah ɗaya na gaskiya. Sa'ad da Balak ya umurce shi ya la’anta Isra'ila, ya ce, "Ba zan iya tsallake maganar Ubangiji Allah na ba." A Turance, “UBANGIJI” (a cikin manyan bakake), ita ce fassarar Ibraniyanci da aka amince da ita a matsayin sunan Allah Mai Tsarki, aka fassara shi zuwa “Jehovah” ko kuma “Yahweh.” Bal’amu ya san Allah da sunan Sa Mai Tsarki kuma ya kira shi “Allah na.” Sa’ad da manzannin Balak suka zo, Allah ya gaya wa Bal’amu kada ya tafi tare da su kuma kada ya la’anta Isra’ila (Littafin Ƙidaya 22:12).

Amsar Balak ita ce ya aika da babbar tawaga ta manyan sarakuna masu daraja - tare da alkawarin lada mai girma. A wannan karon Ubangiji ya ba Bal'amu izinin tafiya da sharadi ɗaya: idan mutanen nan sun zo su kira ka (Littafin Ƙidaya 22:20).

Duk da haka babu wani rahoto da ya nuna cewa mutanen sun sake dawowa kiran Bal'amu. Amma ya tafi, Ubangiji kuwa ya fusata saboda rashin biyayyarsa. A ƙarshe, Jehovah ya kyale shi ya tafi, amma ya bada sharaɗi: “Abin da na fada maka shi kaɗai za ka faɗa.” (Littafin Ƙidaya 22:35).

Balak ya marabci Bal'amu kuma ya yi shiri sosai domin ya sa shi ya la'anci Isra'ila. Amma a kowane lokacin sai sakamakon ya kasance akasin haka. Gabaɗaya, Bal'amu ya furta annabce-annabce huɗu waɗanda ke cikin wahayai masu kyau da girma a cikin Littafi Mai Tsarki na alkawarin Allah wanda ba ya warwarewa na sa wa Isra'ila albarka.

Bayan Allah ya rusa yunƙurinsa na la'anta Isra'ila, Bal'amu ya ba da wata shawara a kansu (Dubi Littafin Ƙidaya 31:16). Idan matan Mowabawa za su iya yaudarar Isra’ilawa zuwa bautar gumaka da lalata, ba sai an la’anta su ba. Allah da kansa zai hukunta su. Dabarar Bal’amu ta biyu ta yi nasara kuma Isra’ilawa 24,000 suka hallaka a cikin hukuncin Allah (Littafin Ƙidaya 25:1–9).

A cikin dukan wannan Bal'amu ya nuna ba shi da tsayayyen ra’ayi. An hana shi la'anta Isra'ila fiye da sau ɗaya. Sau huɗu wahayin Allah ya tabbatar da nufin Allah marar canzawa na albarkatar Isra’ila da kuma hukunta maƙiyansu. Amma ya nace goyon bayan Balak, maƙiyin Isra’ila, da kuma shirin hallaka Isra’ila. Wannan ya tabbatar da cewa ya kamata ya hallaka a cikin irin hukuncin sauran maƙiyan Isra’ila, waɗanda Isra’ilawa suka kashe tare da sarakunan Madayana (Littafin Kidaya 31:8).

Ana so mu tambayi kanmu: Wane dalili ne zai zama mai ƙarfi da kuma tursasawa har da zai sa Bal’amu ya yi tsayayya da wahayin da ya samu daga wurin Allah—zuwa hallakarsa gaba daya? Marubutan Sabon Alkawari guda biyu sun ba da cikakkiyar amsa ta musamman ga wannan tambaya.

Da yake magana game da malaman ƙarya a cikin Ikkilisiya, Bitrus ya ce:

“... sun yar da mikakkiyar hanya, sun ɓaude, sun bi hanyar Bal'amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta...” (2 Bitrus 2:15)

Yahuza kuma, da yake maganar malaman ƙarya, ya ce:

“Sun ɗunguma cikin bauɗewar Bal’amu don kwaɗayi...” (Yahuza 1:11)

Amsar a bayyane take. An jarabci Bal'amu zuwa ga hallakarsa saboda son kuɗi. Domin wannan ya kasance a shirye ya yi karuwanci da baye-bayensa na ruhaniya. Wataƙila ma ya ji daɗin kula da Sarki Balak da sarakunan sa suka yi masa. Son kuɗi na da alaƙa da son yin suna da kuma son iko. Duk wadannan mugayen sha'awace-sha'awace na fitowa daga tushe daya: girman kai.

Darussa daga Bal'amu

Akwai darussa uku masu muhimmanci da ya kamata mu koya daga labarin Bal’amu.

Na farko, Allah Maɗaukaki Sarki ya yi alkawarin da ba zai warware ba na kafa Yahudawa a matsayin mutanen sa har abada. Babu wani iko a duniya, na mutum ko na shaidan, da zai iya soke wannan alkawarin. Yahudawa sun sha yin rashin aminci ga Allah, sai ya yi musu hukunci mai tsanani, amma rashin amincinsu ba zai taba rushe amincin Allah ba.

Yana da mahimmanci a gane cewa wannan al’amari daga Allah ne, ba daga wurin mutane ba. Yahudawa ba su zaɓi Allah ba, amma Allah ya zaɓi Yahudawa. Ina da wani aboki, musulmi ne a da —bari mu kira shi Ali—wanda ya tuba ya karɓi Kristi. Bayan ya tuba, ya fara gabatar da dukan damuwoyin sa ga Allah a kan Yahudawa. Daga karshe Allah ya amsa da cewa, “Ali, matsalarka ba da Yahudawa ba ce. Da Ni ne. Ni ne na zabe su.” Wannan matashin a yanzu yana da kungiyar da ke jawo Musulmai zuwa ga Kristi da koya musu yin addu'a domin Yahudawa.

A cikin Littafin Ƙidaya 24:9 Annabcin Bal'amu ya bayyana wani muhimmin abu a kan makomar mutane da al'ummai. Da yake magana da Isra'ila, ya ce:

“Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, duk wanda ya sa muku la’ana zai sami la’ana.”

Sau da yawa mutane da Ƙasashe suna zaɓen makomarsu ba tare da sanin cewa ta wurin halin su ne game da Yahudawa ba. Masu sa albarka suna samun albarka, masu la’antawa kuma ana la’anta su.

Na biyu, daya daga cikin makaman Shaidan masu ƙarfi da nasara sosai a kan mu shi ne son kudi. Wannan ya zama gaskiya tun daga farkon Ikkilisiya har zuwa yanzu. Hidimar da ke tare da alamu masu karfi na allahntaka musamman mu'ujiza ta warkarwa tana zama hanyar samun kuɗi a kusan kowane lokaci.

A cikin 2 Korinthiyawa 2:17 Bulus ya kwatanta hidimarsa da ta Masu Bi da yawa na zamanin sa: Mu ba kamar sauran ba ne, ba ma yin wa’azin maganar Allah domin neman riba. Har a zamanin Bulus ma Masu Bi da yawa sun mori hidimar su don yin kuɗi!

Kudi kansu ba su da illa. Samun arziki ba zunubi bane. Asali, kuɗi tsaka tsaka ne. Ana iya amfani da su don alheri ko mugunta. Amma sa’ad da muka soma son kuɗi, mun fada cikin tarkon Shaiɗan. A cikin 1 Timoti 6:9–10 Bulus ya yi amfani da kalami mafi ƙarfi don ya gargaɗe mu a kan wannan:

“Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su faɗa a cikin tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Ai son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar son kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya sun jawo wa kansu baƙin ciki iri-iri masu sukar rai.”

A cikin hidima ta na sha yin koyarwa a kan shirin Allah na wadata Masu Bi waɗanda suka himmatu ga manufofin mulkinsa. Duk da haka idan na duba baya a yanzu, ina yin nadama kan lokutan da na yi wannan koyarwa ba tare da daidaita shi da gargaɗin Bulus cikin 1 Timoti 6 ba. A raina, ina kwatanta Masu Bi da suka faɗa cikin son kuɗi a matsayin mutanen da suka ɗauki wuƙa mai kaifi, mai dafi suka soka wa jikinsu. Hakika wannan shi ne abin da Bal'amu ya yi.

Na uku, muna buƙatar mu fahimci bambanci tsakanin baye-bayen ruhaniya da ɗiyan ruhu. Baye-Bayen suna nuna iyawa, amma ɗiyan na nuna hali. Ana samun Baiwa ne ta wurin ‘yar tabawa a lokaci ɗaya, amma ɗiyan na samuwa a hankali ta wurin yin girma.

Karɓar baiwa ta ruhaniya, a kanta, ba ta canza halin mutum. Idan mutum ya kasance mai fahariya ko marar amana ko mayaudari kafin ya sami wata baiwa ta ruhaniya, wannan mutumin zai ci gaba da zama mai fahariya ko marar aminci ko mayaudari ko bayan samunta.

Duk da shike, karbar wannan baiwar, na kara wa mutum nawaya, saboda ta na ƙara tasirin da zai iya samu a kan wasu. Har yanzu kuma ta na ɗauke da jaraba ta son ganin “nasara” a cikin rayuwar Krista ta fuskar yin aiki da baye-baye na ruhaniya maimakon ta haɓaka kyawawan halaye. Akasin haka sai ya zama kamar dai dai yawan baye-baye da mutum yake samu, haka kuma zai mai da hankali ga samar da ‘ya’yan. Lokacin da muka bar wannan rayuwa muka shiga ta har abada, za mu bar baye-bayen mu a nan, amma halinmu zai tafi tare da mu har abada.

An nuna cewa Bal'amu ya sami wahayi a bayyane na ƙarshe mai albarka da ke jiran adalai a cikin addu’ar sa:

“Bari karshena ya zama kamar ɗaya daga cikin mutanen Allah, Bari in mutu cikin salama kamar adalai!” (Littafin Kidaya 23:10)

Amma ba a amsa addu’ar Bal’amu ba. An kashe shi cikin hukuncin Allah a kan Mowabawa, waɗanda kuɗinsu ne suka jarabce shi ya hada kai da su ya yi gāba da Allah.

Karshen Bal’amu ya ba da kyakkyawan misali a kan koyarwar Yesu cikin Matiyu 7:21–23:

“Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, Ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin sama yake so. A ranar nan da yawa za su ce mini, 'Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe ba mu fitar da aljanu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al’ajibi masu yawa da sunanka ba? Sa’an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’”

A taƙaice, babu abin da zai maye gurbin biyayya ga Allah. Wannan kaɗai ya ba mu tabbacin wurin zama a sama.

13
Raba