The two previous letters in this series, Preparing to Reign with Christ have identified the characteristics required to reign with Christ and the spiritual nature of the context. This last letter in the series explains the necessity for Christians to take God and His Word seriously.

Kwanan nan, yayin da nake yin bimbini a kan ma’anar bangaskiya dabam-dabam, na fito da nawa: Bangaskiya ita ce ɗaukar Allah da muhimmanci. Wannan ya zama sakamakon haduwa da Krista da yawa da suke iƙirarin cewa suna da bangaskiya, amma ba su ɗauki Allah da muhimmanci ba.

Ɗaukar Allah da muhimmanci na nufin ɗaukar Maganar sa da muhimmanci. Idan mutum ya yi mana magana, amma muka yi watsi da ita - ko muka ƙi - yawancin abin da ya faɗa mana, ba ma ɗaukarsa da muhimmanci. A gaskiya ma, mu na da laifin rashin girmamawa.

Haka yake kuma a wurin Allah. Idan muka yi watsi ko muka ƙi yawancin abin da ya fada mana ta wurin maganarsa, ba ma ɗaukar Sa da muhimmanci. Haƙiƙa, muna, kin girmama shi. Duk da haka wannan shi ne yadda yawancin Krista suke dangantaka da Allah. Suna ɗaukar maganarsa kamar haɗe-haɗen abinci, suna zabar waɗanda suka yi musu ɗaɗi suna tsallake wasu.

Akwai hanyoyi huɗu masu aiki in da maganar Allah ke shafar rayuwar mu: alkawuran Sa, dokokin Sa, abubuwan da ya hana, da gargaɗin Sa. Za mu ɗauki misalan kowanne bi da bi mu duba yadda za su iya shafar mu.

Alkawuran Allah

Litattafan nan huɗu na Bishara na ɗauke da alkawura masu ban al’ajabi da yawa na Yesu, amma kafin mu karɓe su don kanmu yana da muhimmanci mu san ko su wanene aka ba kowane alkawarin. Marubutan Litattafan sun bada banbanci a sarari tsakanin kalmomin da Yesu ya faɗa wa almajiransa da waɗanda ya fada wa taron mutane ko kuma waɗanda ba almajirai ba. Akwai rubutattun ayoyi fiye da 900 na kalmomi da aka faɗa wa almajirai da kuma kusan 860 da aka fada wa waɗanda ba almajirai ba.

Babbar alamar almajirai na gaskiya ita ce sadaukarwa. Sun sadaukar da kansu gaba daya tare da yin biyayya da kuma bin Yesu ba tare da damuwa da abin da zai biyo baya ba. Yesu da kansa ya ba da wannan sharaɗi:

“Duk wanda bai ɗauki giciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. Haka ma, kowannenku in bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.” (Luka 14:27, 33)

Babu shakka mu da muke raye a yau ba mu nan sa’ad da Yesu ya ke maganar. Kafin mu yi amfani da ɗaya daga cikin alkawuransa a kanmu, muna bukatar yin tambaya: Ko ni irin mutumin da Yesu yake magana da shi ne? Ko alkawuran Sa sun shafe ni? Ko ina da ‘yancin karɓar su?

Misali, Yahaya 14 ta ƙunshi alkawura masu daraja, kamar:

“Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi. Kome kuka roka da sunana, zan yi shi. Saboda ina raye, ku ma za ku rayu. Na bar ku da salama, salama ta nake ba ku. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.” (aya 13, 14, 19, 27)

Amma waɗannan kyawawan alkawuran an yi su ne kawai ga ƙungiyar almajirai waɗanda suka sadaukar da kansu. Bitrus ya yi magana a madadin su duka sa’ad da ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka” (Luka 18:28). Karɓar waɗannan alkawuran ba tare da cika wannan sharadi ba ba bangaskiya ba ce, amma zato ne. Kowannen mu na buƙatar mu tambayi kan mu: Ni almajiri ne-ko kuwa memban majami’a ne kawai?

Dokokin Allah

“Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umurninsa. Kowa ya ce, ya san shi, ba ya kuwa bin umurninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi. (1 Yahaya 2:3-4)

Yadda mu ka ɗaukin dokokin Allah na bayyana gaskiyar yanayin ruhaniyar mu. Yin biyayya da su ne tabbacin cewa mun san Allah.

Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi dokoki da yawa da suka shafi fannoni dabam-dabam na rayuwarmu, amma Yesu ya taƙaita su duka cikin abu ɗaya sama da duka sauran:

“Sabon umurni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna; kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yahaya 13:34-35)

Ta wurin yin biyayya da wannan doka muna cika dukan shari’a: “Don duk shari’a an kunshe ta ne a kalma guda, wato, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” (Galatiyawa 5:14). Ƙauna ita ce babbar manufar da ta sa aka bayar da duk sauran dokoki:

“Alhali kuwa manufar gargadinmu ƙauna ce, wadda take ɓulɓulowa daga tsarkakakkiyar zuciya da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya, waɗansu sun kauce wa waɗannan al’amura sun shiga zancen banza...” (1 Timoti 1:5-6)

A kan wannan dalili ne ya zama dole mu auna biyayyarmu ga dokokin Allah. Muna buƙatar mu tambayi kanmu: Ko rayuwata na bayyana ƙaunar Allah?

Abubuwan da Allah ya Haramta

“Kada ku ƙaunaci duniya ko abin da yake a cikin ta. Kowa yake ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam.” (1 Yahaya 2:15)

A nan Allah ya haramta mu ƙaunaci duniya. Ya tilasta mana yin zabi. Za mu iya ƙaunar duniya, ko kuma mu ƙaunaci Allah Uba. Amma ba za mu iya yin duka biyun ba. Dole ne ya zama ɗaya ko ɗayan - ko dai ƙaunar Allah ko ƙaunar duniya.

A harshen Sabon Alkawari, duniya ta ƙunshi dukan mutane da dukan ayyukan da ba a miƙa su ga gwamnati mai adalci na shugaba wanda Allah ya sanya ba, wato, Yesu Kristi. Don haka, duniya - ko cikin sani ko a cikin rashin sani - tana tawaye ga Allah. Don haka son duniya shi ne haɗa kai cikin tawayen ta.

Irin jan da duniya take yi wa rayuwar mu yana da ƙarfi sosai. Tana ba mu abubuwan daukar hankali da ban sha'awa da yawa. Waɗansun su ga alama ba su da laifi, duk da haka a cikinsu akwai dafin tawaye a ɓoye.

Kafofin watsa labarai na ɗaya daga cikin hanyar da duniya ke jan hankali, tare da kowane irin nishaɗin da take bayarwa. Na yanke shawarar cewa nishaɗi ba al’amarin Krista ba ne idan zai sa mutane su zama ‘yan kallo. A cikin Littafi Mai-Tsarki Allah ya sanya wa mutanensa lokutan bukukuwa na farin ciki, amma mutanen da kansu na cikin aikin bukukuwan. Ba su kasance 'yan kallo kawai ba.

Bugu da ƙari, yawancin nishaɗin zamanin yanzu na cike da munanan ɗabi'u da kazamtar ruhaniya kuma suna ƙazamtarwa a boye. Wasu shekaru da suka gabata Ruth da ni mun kalli wani wasa mai kyau na ban dariya na wani fitaccen dan wasan kwaiwayo - amma yana ɗauke da jerin kananan munanan kalamai. Mun so mu sake kallonsa a karo na biyu, amma daga ƙarshe mun yanke shawarar cewa ba za mu bude wa Ruhu Mai Tsarki da ke cikinmu mugayen kalamai da ke cikin wasan ba.

A ƙarshe mun yanke shawarar cewa ba za mu ƙara kai kanmu ga wani abu da ke ɗaukaka zunubi da kuma wulakanta Yesu Kristi ba. Mun kuma mai da shi ƙa’ida cewa ba za mu ajiye wani littafi ko wani abu da yake ɓata Yesu a gidanmu ba. Ko hakan ya zama tsattsauran ra'ayi? Wataƙila yana iya zama. Amma addinin Krista addini ne na tsattsauran ra'ayi.

Gargadin Allah

A cikin Matiyu 24 Yesu ya yi annabcin yanayin kwanaki na ƙarshe. Ya fara da gargaɗi a kan yaudara: "Ku kula fa kada kowa ya ɓatar da ku." A cikin aya ta 11 ya maimaita gargadinsa: Sa'an nan annabawan karya da yawa za su firfito su ɓatar da mutane da yawa. Yaudara ita ce babban haɗari da ke fuskantar Krista a kwanaki na ƙarshe.

A cikin Matiyu 24 Yesu ya bada gargaɗinsa ga manzanni wadanda shi da kansa ya zaɓa kuma suna tare da shi a koyaushe har tsawon shekaru 3 na hidimarsa. Idan waɗannan manzannin suna bukatar irin wannan gargaɗin, ta yaya Krista a yau za su yi tsammanin cewa suna da wata kariya ga wannan haɗarin?

Duk da haka na ci karo da Krista da yawa waɗanda ke ganin gargaɗin da aka yi game da yaudara bai shafe su ba. Irin wannan tunani, haƙiƙa, alama ce cewa yaudara ta riga ta fara aiki a cikinsu.

A cikin 2 Tassalunikawa 2:9-10 Bulus ya ƙara ƙarfafa gargaɗi game da yaudara dangane da zuwan magabcin Kristi.

“Mai tawayen nan kuwa [magabcin Kristi] zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al’ajibi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri-iri. Yana kuma yaudarar waɗanda suke hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.”

Yawancin Krista masu morar iko suna da ra’ayin cewa duk wata koyarwa ko aikin hidima waɗanda ke tare da alamun allahntaka lallai daga wurin Allah su ke, amma wannan ba gaskiya ba ne. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan yana iya yin alamu iri-iri. Amincewa da duk wani abu na ikon allahntaka cewa daga Allah ne yana buɗe ƙofa ga yaudara.

Tabbatacciyar kariya ɗaya kaɗai daga yaudara: ita ce karɓar ƙaunar gaskiya. Wannan ya wuce sauraron wa’azi, ko kuma karanta Littafi Mai Tsarki kawai. Amma yana nuna himma da kwazo wurin mika kai ga ikon Maganar Allah da ya shafi kowane bangare na rayuwar mu. Yana haifar da wata kariya a cikin mu game da kowace koyarwa ko hidimar da ba bisa ga Maganar Allah ba.

Allah yana ba kowannen mu wannan kaunar gaskiyar. Ko muna shirye mu karba? Za mu ɗauki gargaɗinsa da muhimmanci ko kuwa za mu yi watsi da shi?

7
Raba