Tunanin Dan Adam: Mai Shirya Wa Magabcin Kristi Hanya

Derek Prince
*First Published: 1994
*Last Updated: December 2025
7 min read
“Ai famarmu ba da ‘yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu” (Afis. 6:12)
In the previous teaching letter, we considered the attributess of one who is fit to reign with Christ. This lesson is about the need to recognise the spiritual nature of the battle.
A matsayin mu na Masu Bin Yesu Kristi, mun sami kanmu a cikin jayayyar da ta haɗa da sama da kasa. Ikokin da ke yaƙi da mu “mutane ne marasa jiki”—miyagun ikoki na ruhaniya da ba sa ganuwa waɗanda suke gaba da kowane adalci na gaskiya da kuma suke ƙoƙarin kafa mulkin Shaiɗan a duk fadin duniya.
Haƙƙin mu a cikin wannan yaƙi na musamman ne, saboda Kristi ya ba mu fahimta ta ruhaniya da kuma makaman da za su iya bamu nasara. Gwamnatoci da sojojin wannan duniyar, su na aiki na jiki ne kawai, ba su fahimci yaƙin ba kuma ba su da ikon yin maganin rundunar Shaiɗan da ke cikin sama. Akasin haka ma, ba tare da sani ba, su kansu waɗannan rundunan Shaiɗan ne ke mallakar su kuma suna amfani da su.
Babban abin da ake buƙata don samun nasara shi ne a gane halin ikokin da ke aiki a kowane yanayi. A cikin ’yan watannin nan sa’ad da nake yin bimbini a kan abubuwan da ke faruwa a duniya—musamman a Amurka da Isra’ila—na gaskata cewa Allah ya nuna mani ainihin mugun iko na ruɗi da Shaiɗan yake shirin yin amfani da shi don cika manufofinsa na ƙarshen wannan zamani.Tunanin dan adam ne.
A da na ɗauki ‘tunanin ɗan adam’ a matsayin kuskure marar illa. Yayin da na duba ƙamus, na yi mamakin ma'anarsa:
“Ƙin amincewa da duk wani iko ko kyakkyawar ɗabi’a da ta fi ta ɗan Adam; watsi da addini don amincewa da ci gaban bil'adama ta hanyar ƙoƙarinsa."
Na gane cewa ‘Tunanin ɗan adam’ ba tsaka tsaki ba ne a al’amarin ruhaniya. Akasin haka, musu ne da ƙin ikon Allah da mulkinsa da gangan. Addini ne mai gaba da addini. Don haka, zai iya zama—kuma sau da yawa haka ne—ana koyar da shi a cikin tsarin ilimi, kamar na Amurka., wanda ya haramta koyar da addini yadda aka saba.
Na yanke shawarar bin diddigin tarihin ‘tunanin dan Adam’, inda na fara da mafarkin Nebukadnezzar na wata siffa mai kan zinariya, ƙirji da hannuwa na azurfa, ciki da cinyoyin tagulla, da ƙafafu na ƙarfe.Daniyel ya fassara wannan a matsayin alamar daulolin Al'ummai huɗu waɗanda za su taso bi da bi. Kai na wannan siffar ita ce Babila; kirjin da hannuwan Mediya-Farisa ne; ciki da cinyoyin Girka ne; kafafun su ne Roma (Dan. 2:31–40).
Wani muhimmin abu da na fahimta shine: al’aura sun kasance a yankin da aka haɗa da Girka . Saboda ilimin da na ke da shi a falsafar Girkanci, wannan ya zama a bayyane a gare ni. Na gane cewa Girka ce—fiye da kowace a cikin daulolin—wadda, ta wurin falsafarta, ta riƙa haifar kanta a cikin al’adu da suka biyo baya.
Biyu daga cikin masanan falsafa na Girka na farko waɗanda muke da su a rubuce su ne Heraclitus da Protagoras. Uku daga cikin daɗaɗɗun zantatukan su suka ce:
- “Dukan abubuwa suna gudana”
- “Ba za ka taɓa shiga kogi ɗaya sau biyu ba”
- “Mutum ne ma’aunin kowane abu”
Yana da ban mamaki yadda waɗannan zantattuka uku suka jimilta dalilin tunanin ɗan Adam. Sun yarda cewa komai mai canzawa ne; babu ɗabi'a ko shari'a da ke dawwama; kuma mutum shi ne babban mai mulki a duniya.
Ba shi cikin abubuwan da za mu duba na wannan nazari filla filla yadda wannan tunani ya canza, da farko, ra'ayoyin Turai, sa'an nan, ta wurin Turai kuma ra'ayoyin "wayewa" na zamani. Girkawa sun mai da tunanin ɗan adam wani gunki. Tunanin Aristotle game da Allah shi ne cikakken hankali mai nazarin kansa—saboda babu wani abu da ya kasa da haka da ya isa yayi nazarinsa. Daga nan ne dukan tunani na falsafa ya ci gaba.
Ƙari a kan falsafa, wani babban abu a cikin al'adar Girkanci shi ne muhimmancin da ta ba gasar wasanni. Gasar wasanninsu ya dauki fasalin abinda a gaskiya, bautar gumaka ne na masu ƙwazon wasanni, wanda ya sake farfadowa a wannan ƙarni. Shirye-shiryen da aka fi kallo a talebijin a yau su ne manyan gasar wasanni na kasa da kasa.
Har ila yau, Girkawa sun yi ƙoƙarin ƙasƙantar da dangantakar aure tsakanin namiji da mace, da kuma bada fifiko ga dangantakar luwaɗi tsakanin maza biyu a matsayin mafi "gamsar da hankali." A siffofin su, siffar namiji mafi kyau a yawanci lokaci ana gabatar da ita tsirara, yayin da mace kuma ake lulluɓe ta da wata doguwar riga.
Waɗannan da ake kira “alloli” na Girka sun nuna gazawar kyakkyawar ɗabi’a na ’yan Adam: sha’awa, fasikanci, kishi, ramuwar gayya da yaudara—a gaskiya, babu wata cikakkiyar tsayayyiyar ƙa’idar ɗabi’a. Wannan ya ba mutum 'yancin zama allahn kansa, ya kuma kafa nasa ƙa'idodin ɗabi'a. Da shike, babu wasu mutanen da za a sa zuciyar su yi rayuwar da ta wuce matsayin gumakan su.
Duk waɗannan abubuwan ‘’Tunanin ɗan adam’ na Girkawa ne da ya ke ƙara bayyana a cikin al'adun mu na Yamma a cikin wannan ƙarnin. Duk da haka, a cikin 1992, ruhun ‘tunanin ɗan adam’ ya kawo wani sabon hari mai zafi a kan Amurka da Isra'ila. Kusan a lokaci ɗaya, gajimaren ikokin duhu suka sauko bisa ƙasashen nan guda biyu.
A zaɓensu na ƙasa na waccan shekarar ya nuna a fili cewa wannan ikon da ya kawo mulkin Clinton a Amurka da kuma haɗakar Ƙungiyar Ƙwadago a Isra'ila, ‘tunanin ɗan adam’ ne tsantsa. Dukan gwamnatocin biyu sun nuna ƙin amincewa da dokokin Allah na adalci da kuma na alkawuran da ya yi da mutum, da farko ta wurin Musa sa’annan kuma ta wurin Yesu Kristi. Sun nuna cewa, manufar abin a ƙarshe, ‘tunanin dan Adam’ zai gaskata komai amma banda gaskiya kuma zai yarda da komai amma banda adalci.
Wannan ɗaukaka mutum shine ikon da zai tayar da maƙiyin Kristi a karshe, wanda sunansa lambar mutum ne (W. Yah. 13:18), mutum mai karya doka, mai yin hamayya da kuma ɗaukaka kansa sama da kowane abu da ake kira Allah ko kuma ake bauta wa, har ma ya ɗaukaka kansa a cikin haikalin Allah, yana shelar kansa shi ne Allah (2 Tas. 2:3–4).
Maganar Allah ta bayyana cewa zai mallaki dukan waɗanda suka ƙi ƙaunar gaskiya. Don haka, Allah zai aiko musu da ruɗani mai ƙarfi da za su gaskata da ƙarya— ƙarya ta asali, wato, wadda Shaiɗan ya ruɗi iyayenmu na farko da ita: “Za ku zama kamar Allah...” ko kuma “kamar alloli. ” Wannan ɗaukaka mutum a matsayin Allah zai kawo “babban tsanani”—lokacin kunci ne ga dukan duniya wanda har ma zai zarce kisan kiyashi da aka yi na 1939–1945 (Matta 24:21–22).
Kafin wannan lokaci na babban tsanani na ƙarshe, duk da haka, Allah yana da manyan dalilai da zai taimaki Isra'ila da Ikkilisiya. Aikin jinƙai zai rigayi aikin hukunci. An bayyana shirin da Allah ya ke yi domin wannan a cikin Zakariya 9:13: “Zan ta da ’ya’yanki, ke Sihiyona, gāba da ’ya’yanki, ke Girka...”
"'Ya’yan Girka" su ne waɗanda suka rungumi tunanin ɗan adam. “’Ya’yan Sihiyona” su ne waɗanda suka tsaya a kan Kalmar Allah marar kuskure, suna rike da alkawura da sharuɗɗan ta. Za a tsamo su daga Isra'ilawa na jiki da kuma Ikilisiya mai gaskatawa. Game da su za a ce, “Suka yi nasara da shi [Shaiɗan] ta wurin jinin Ɗan Ragon, da kuma kalmar shaidarsu, ba su kuma yi ƙaunar ransu ba har ga mutuwa.” Za su zama mutane masu wannan fifiko; wato, yin nufin Allah zai fi zama da muhimmanci a gare su fiye da kasancewa a raye.
Sa’ad da muka fuskanci wannan ƙalubalen, kowannen mu na buƙatar tambayar kan sa: Ko Ina shirye in ɗauki matsayina na zama ɗaya daga cikin ’ya’yan Sihiyona?
Idan za a ƙirga, ikoki na masu ‘tunanin ɗan adam’ sun fi mu yawa. Duk da haka, za mu iya samun ƙarfafawa daga misalin Asa, sarkin Yahuda. Da yake fuskantar yaƙi daga babbar rundunar da ta fi shi ƙarfi, addu'ar da ya yi ta karayar zuci ganin cewa za su ci shi da yaƙi, ta koma ta samun cikakkiyar nasara. A gare mu yau, addu’ar sa ta ba mu babban abin koyi na yin yaƙi da ikokin ɗaukaka kai na ‘tunanin ɗan Adam’.
“Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamar ka, wanda zai yi taimako sa’ad da mai ƙarfi zai kara da marar karfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, Gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum ya rinjaye ka.” (2 Tarihi 14:11)
Bari mu tsaya tare cikin yin addu’a!

*Free download
*This Teaching Letter is available to download, print and share for personal or church use.
Zazzage PDFLambar: TL-L003-100-HAU