“Ashe ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a?” (1 Korinthiyawa 6:2)

Allah yana da manufa biyu ta fansar mu. A bangare mara dadi, don ya cece mu daga jahannama - wanda ya kamata mu kasance masu godiya har abada. A bangare mai dadi, don ya shirya wa kansa mutane, waɗanda za su yi tarayya da Kristi a kursiyin.

This is the first in a series of three teaching letters that explore the purpose of preparing to reign with Christ.

Kafin ka ci gaba da karantawa, ka dakata na ɗan lokaci ka yi la'akari da ma’anar abin a gare ka, a matsayin ka na Kirista, ya kamata ka yi shiri don yin mulki tare da Kristi har abada. A namu bangaren, ni da Ruth mun gano cewa Ruhu Mai Tsarki yana ba da fifiko ga yin shiri don makomar mu ta har abada.

Alkawari yin Mulki

“Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa’ad da Ɗan Mutum zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu.” (Matiyu 19:28)
“Duk wanda ya ci nasara, yake kuma kiyaye aikina har ƙarshe, shi ne zan bai wa iko a kan al'ummai, ‘Zai kuwa mallake su da sanda ta ƙarfe, ya farfashe su kamar tukwanen yumbu.” (Wahayin Yahaya 2:26-27)

Shirin yin Mulki

Domin wannan babbar nawaya ta yin mulki tare da Kristi ana buƙatar mu yi shiri sosai. Ba yin iƙirarin an “maya haifuwa” ba kawai. Ga wasu manyan sharudda nan kasa.

1. 1. Jimiri

“Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwaje da na sha. Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku iko, ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra’ila.” (Luka 22:28-30)

Mutane da yawa suka fito zama almajiran Yesu, amma goma sha biyu ne kawai suka jure tare da shi har zuwa ƙarshe, kuma su kaɗai aka lisafta sun isa su yi mulki tare da shi bisa Isra'ila.

“In mun mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi. In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi.” (2 Timoti 2:11-12a)

Idan za mu yi tarayya da ɗaukakar Kristi, dole ne mu fara tarayya cikin mutuwarsa sa’anan mu ci gaba da dagewa cikin gwaje-gwaje har zuwa ƙarshe.

2. Tawali'u, Talauci na Ruhu

“ Albarka ta tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin mulkin sama nasu ne.” (Matiyu 5:3)
“ Albarka ta tabbata ga masu tawali’u, domin za su gāji duniya.” (Matiyu 5:5)

Allah ba ya bada mulkinsa ga masu girman kai ko masu son kai, amma ga waɗanda suka gane cewa in dai ta kansu ne ba su cancanci irin wannan darajar ba. Hannatu, uwar Sama’ila, ta fada a cikin waƙarta ta nasara:

“Ya kan ta da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman bakin ciki, Ya sa su zama abokan ‘ya’yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu muƙami.” (1 Sama’ila 2:8)

Bayan shekaru dubu, Budurwa Maryamu - a cikin waƙar nasara mafi girma - ta furta wannan gaskiyar:

“Ya firfitar da sarakuna a sarauta, Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.” (Luka 1:52)

3. Tsarki

“Almasihu… wanda ya bada kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama’a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.” (Titus 2:14)

Mutanen da Kristi ya yarda a matsayin nasa, su ne waɗanda ya fanshe su daga kowane aikin mugunta kuma ya tsarkake don kansa.

Amma akwai bangarori biyu na wannan aikin tsarkakewar: daya na Allah, dayan kuma na mutum. A cikin 1 Yahaya 3:3 manzo ya yi magana game da begenmu na samun sākewa zuwa kamannin Kristi sa’ad da zai dawo, amma sai ya ƙara da cewa: “Duk mai kwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa kenan, kamar yadda shi yake mai tsarki. Kristi zai tsarkake waɗanda suka yarda su tsarkake kansu kadai. Bugu da ƙari, Allah yana da ma’auni ɗaya kaɗai na tsarki: “Kamar yadda shi [Yesu] yake mai-tsarki.”

Bitrus ta fari 1:22 ta gaya mana yadda za mu tsarkake rayukanmu: “biyayya ga gaskiya ta wurin Ruhu”, yana haifar da “ƙaunar ’yan’uwa ta gaskiya”. Tsattsarkan rai shi ne yake cike da kauna.

4. Ƙaunar Gaskiya

Ta wurin yaudara ne Shaiɗan ya ja hankalin Adamu da Hauwa’u har suka yi wa Allah tawaye, kuma wannan shi ne babban makaminsa na gaba da ’yan Adam tun wancan lokacin. A cikin Wahayin Yahaya 12:9 an kira shi “macijin nan na tun dā… mayaudarin dukan duniya.”

A cikin 2 Tassalunikawa 2:9-11 Bulus ya yi gargaɗi cewa wannan dabarar ta Shaiɗan za ta bayyana sosai a karshe cikin magabcin Kristi, wanda zai yi yaudara da alamu na ƙarya da kuma al’ajibai ga dukan waɗanda “ba su karɓi ƙaunar gaskiya ba”.

To, wannan ce kaɗai kariyarmu: mu karɓi ƙaunar gaskiya. Dukan waɗanda suka ƙi wannan ba yaudarar Shaiɗan kaɗai ba. Allah da kansa zai aiko musu da babban ruɗu.

Ƙaunar gaskiya ba bin ƙa'idar addini kawai ba ce, ko da yake hakan ya zama "ra’ayin mafi yawa". Ba karanta Littafi Mai Tsarki da yin “addu’a a kadaice” kowace rana ba. Yana buƙatar sadaukarwa ta gabaɗaya don gaskantawa da yin biyayya ga Maganar Allah - wanda ke kawar da kowane nau'i na ja da baya.

A zamanin Yesu, Yahudawa da yawa sun gane cewa Yesu ne Mai Ceto, amma don tsoron shugabannin addini ba su amince da shi ba, “don sun fi ƙaunar girmamawar mutum da girmamawar Allah.” (Yahaya 12:43). Wannan shi ne dalilin ja da baya. Ya kamata mu tambayi kanmu: Wanne ne ya fi a gare ni – yardar Allah... ko kuwa ta mutum?

A cikin Karin Magana 23:23 Sulemanu ya ba da shawara, “ Ka sayi gaskiya, kuma kada ka saida...” Ba a samun gaskiya a sauƙaƙe. Akwai bukatar ɗaukar lokaci mai yawa don yin addu’a da nazarin Nassoshi, sa’annan a aikata shi a rayuwarmu ta yau da kullum. Dole ne a ba shi fifiko fiye da kowane irin nishaɗi da al'adunmu na zamani ke bayarwa a sauƙaƙe. Sadaukarwa ce ta dukkan rayuwa.

An gargade mu da kada mu sayar da gaskiya. Za a iya jarabtar mu mu sayi shahara a farashin gaskiya ta wurin guje wa “zantattukan” Yesu da kuma gabatar da bisharar da ba ta bukatar sadaukarwa, amma da alkawarin sassauƙar hanyar rayuwa. Wannan yana ƙaryata gargaɗin Yesu: “Domin kuwa kofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.” (Matiyu 7:14).

Idan da gaske ne kana da muradin shiga mulki tare da Kristi, bari in ba da shawarar cewa ka maimaita karantun nassoshin da na tsakuro a sama, kuma ka yi la’akari da yadda kowannensu ya shafi rayuwar ka. Idan Ruhu Mai Tsarki ya nuna maka wuraren da ka gaza, ka nemi taimakonsa don yin sauye-sauyen da ake buƙata. Ta haka za ka maida shekara mai zuwa ta zama shekarar girma da gamsuwa.

7
Raba