“ Ƙira Mai Ban Tsoro Da Al’ajabi”

Derek Prince
*First Published: 2008
*Last Updated: May 2026
2 min read
This teaching is not currently available in Hausa.
A cikin Zabura 139:13–14, Dauda ya yi magana da Ubangiji, yana cewa:
"Gama kai ka sifanta kayan cikina; ka harhaɗa ni cikin uwata. Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin tsoro ce abin al’ajibi ce kwa. Ayyukanka suna da ban al’ajibi; wannan ma raina ya sani sarai."
A wata fuskar, yana gaya wa Allah, "Kana nan lokacin da nake cikin mahaifiyata; Kana harhaɗa ni."
Ban san ko mun fahimci cewa ƙirar mu abin tsoro da ban al’ajibi ce ba. Idan na yi tunani na abin da Allah ya yi na halittar jikina da kuma ba ni jiki, ina cika da razana. Gama ƙirata abin tsoro ce, abin al’ajibi, kuma dole ne in ba da lissafi ga Allah na duk abin da na yi da jikin da Ya ba ni.
Na’urori sun ɗauke mana hankali a yau— abubuwa ne masu kyau kwarai da gaske. Amma ina so in nuna cewa, naʻurori mafiya kyau duka su ne jikkunanmu. Krista da yawa suna kashe lokacinsu wajen lura da na’ororinsu fiye da yadda suke yi wa jikkunansu. A karshe duka, idan naʻura ta gaza ko ta lalace ko ta tsufa, za mu iya sayen wata da ‘yan kuɗi ƙalilan, za mu iya sayen wata. Amma idan jikin ɗan adam ya lalace, kamar yadda wannan naʻurar ta lalace, ƙarshen kenan. Babu wani abin da za a iya yi.
*Prayer Response
Na gode maka, ya Ubangiji, saboda jinin Yesu da kuma aikin Ruhunka Mai Tsarki. Ina furtawa da mamaki cewa ƙirata abin tsoro ce, abin alʻajabi ce kuma. Jikina haikali ne na Ruhu Mai Tsarki, an fanshe shi, an wanke shi, an tsarkake shi da jinin Yesu. Amin.
Lambar: WD-B097-058-HAU